BAK’A CE Page 1 to 10

A kauyen nan basu da ruwan pampo sai fan take, wuta bata kai can ba ,
Gari ne mai tarin ni.ima , albarkar noma garake , sannan mota bata shiga domin can cikin sahara ne sai dai a hau rakumi a samu a shiga cikin Timiya
Yan mata ne laye su hudu,
Cikin ukun nan kowace ta kala tamkar ka lasheta dan kyau da daukan hankali sun sha digo digonsu na buzaye da katanga , sai daya a gefensu wace kanta ke sade kasa jikinta na dan rawa rawa hanayenta kawai ake ganni bakin kirin da yafen mayafinta na turkudi (tufafin buzaye )
Shigowa wani datijo ya yi yana dan dukawa dan tsayi ne da shi, da hannunsa yake yiwa mutanen dake bayansa nuni da su shigo domin bashida hausar kirki a bakinsa
Yana dago kansa ya hangota a cikinsu, ya juyo da dan sauri ya ga mazan nan har sun zauna
Rai bace ya nufi dakinsu wajen uwar yaran wato matarsa yana zuwa ya daga hannunsa ya dungurewa yar datijuwar kai ransa bace cikin yaren buzanci ya ce” ban hane ki turo min da wannan bakar yar taki ba? Na aurar da yaya hudu saura uku na cire wannan bakar a yayana, na sha fada maki ni a danginmu ba baki aman kika tashi kika haifo min baka? Na yi na yi ki fada min gaskiyar waye ubanta kin ce ni? Kuma dan bakin ciki an samu elhazawa masu son auren yaren kin tunkudo (turo) mini da ita ko?
Bata ce komai ba sai sada kai da ta yi, har ya gama babatunsa ya juya
Yana komawa ya damki hannunta ya jata kiiiii suna shiga ya hankadata ta tafi tagataga ta duke nan kusa da gadon karagar mahaifiyarta kanta sade, ya aibatata sosai kafin ya juya ya koma wajen bakinsa
Kanta sade hawaye ya ziraro mata, ta dago a hankali ta kali mahaifiyarta da idannuwanta ke rufe ruf tana jin yanda zuciyarta ke suya
Murya a raunane ta ce” *ANNA* (wato mama)
Bata bude idannuwanta ba, bata amsata ba
Ta dan jima a haka kafin take mikewa ta dage rufar da ta yi tana kallon mahaifiyarta da wani irin yannayi, a gaskiya a jikin wannan matashiyar budurwa banda idannuwanta ba wani abu mai hasken fari domin kuwa tana da baki ga kuma tufafinta mai rinar da fata ne wato turkudi
Mamanta ta dago ta bude ido a karo na farko, murya shake cikin yaren buzanci ta ce” kal ki ce komi, ki yi hakuri kawai
A hankali ta juya dan ruwa gidan baba tsoho….
Ku biyo ni garina, *TIMIYA* domin a Niger nake…. ……taku har kulun YAR MUTAN NIGERSAJIDA
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2⃣
A hankali take tafiya tana dan rabewa, da ta hango gugun yara sai ta labe har sai sun fice idan kuwa wasa ne suke dole sai dai ta canza hanya domin irin wulakancin da mahaifinta da wasu a cikin yan uwanta ya sanya har jama.ar garin ke wulakantata suma suna dubanta daban cikinsu….
A hankali ta karyo kwanar runfar baba tsoho
Sanda take dan karasawa domin bata son haduwa da almajiransa tun bama Ali ba wanda ya so hada shi da ita ya ci mata mutunci yayi mata kwakwaran kashedi na koda wasa kar ta yarda ta nuna tana son sa domin shi dama ya shigo garin Timiya ne dan ya samu buzuwa fara ya aura..to tun daga lokacin sauran almajiran ke tsokanarta suna fadin ta Aliyu *BAK’A*
zaune yake cikin bukarsa, rawani ne a fuskarsa kwaurin hannun sa da na kafarsa ake gani , hakan zai nuna maka tsohon mutun ne, domin fatarsa du ta yi yaba haka gashin dake kwaurinsa du sun yi fari sol sol da su
Waje daya kawai yake kallo, a zuciyarsa kuwa ya afka tunanin yau ina ta yi? Ya aka yi bata zo ta dauki karatu da safe ba? Bata da kawa, bata da wani mai rabata a jikinsa, mahaifiyarta kanta bata mugun sake mata dan tana tsananin tsoron mijinta a kan yarinyar
Shi kam yana cike da zulunmin abinda ya sa bata zo ba
A hankali ta daga kasarin dakin ta yi masa salama
Murmushi ne ya subuce masa yana kallonta kafin ya amsa salamarta
karasawa ta yi tana dan tatare tataren dakin ta kai dubanta wajensa, cike da kaunar tsohon sannan idan tana tare da shi takan ji ta wani iri, bata jin tsoronsa sai soyayarsa, tsohon shi ne kawai mai yi mata murmushi a duniya,
Dan murmushi ta sakar masa ta ce” SOFO (wato tsoho)
Shima murmushin ya yi, ya dan nunota da yatsarsa,
Ta karasa ta duka kasa ta ce” ta gode (gaisuwa kennan)
Turkudin kanta ya shafa a hankali kafin ya ce” Alharasssss
Mikewa ta yi ta gama tatare masa dakin ta dauko tsintsiyar kabar da ta yi da kanta dan share dakins ta shashare ko.ina ta dan dage kasarin ta dauki tulun ruwansa ta fice
Murmushi ya yi, ya bi ta da kallo….a kasan zuciyarsa ya ayanna” Allah ya nuna min farin cikin ki kafin na koma gareshi
Tafe take da tulunta cikin nutsuwa, tana zuwa ta duka wajen diban ruwan , wani dan kewaye ne aka yi shi ba rijiya ba, shi ba teku ba shi dai ruwan ana jayo masu shi ne, sannan kalar ruwan jajajir ne sai kanshin laka , akoy ruwa masu kyau sai dai idan ta yarda ta je wajen sai dai ta dawo ba ruwan ba tulun domin du yawancin yan matan garin can suke zuwa dibo ruwa su kuwa sun ki jinnin ganninta a wajen
Sai da ta cika tulun ta mike ta gyara bakin zaninta da kyau ta daga ta dora saman kanta
Yanda ta bar shi zaune haka ta dawo ta tarar da shi
Ta nemi wajen Tulun ta ajiye tana dubansa cikin yaren buzanci ta ce” baka gajiya da kallon waje guda?
Bai bata amsa ba sai mika mata allonta da yayi yana nuna mata wajen zama
A hankali ta zauna ya ci gaba da koya mata karatu wanda sosai ta nisa kuma shine malaminta tunda ta san shi
Suna gama karatun ya ce” menene tambayarki ta yau?
Ta yi tsai tana kallonsa, can ta nisa ta ce” sofo, shin mutun mai bakar fata laifi ya yi aka halice shi baki?
Da sauri ya kallota, ganni ya yi kanta a sade, tana faman murza hannayenta …..yarinyar akoy zurfin ciki sosai aman wani lokacin sai ta fadi dan abinda ke ranta domin tana gannin abubuwa masu firgitarwa a rayuwarta
Hannunsa ya daga, murya a sanyaye ya ce” ko daya mutun baki da fari du daya ne a wajen Allah
Dara daran fararan idannuwanta ta dago ta sauke kan nasa da sukai dan ja sannan du sun yi yaba irin na tsohon mutun, hawayen da ya taru a idannuwanta ta yi iya kokarinta ta mayar da su , daga haka bata kara komai ba, bata bari ta yu kuka ba ta mike tsam ta fice ba tare da ta kara kalma daya ba
Ajiyar zuciya ya sauke, yana tir da halayen Agali, Agali bashi da hankali da tunani, dan kawai Allah ya yi yarinya an haifeta bak’a cikin y’ayanka sai ta zama abin kyama abin kyankyami abin wulakantawa? Ita ta halici kanta ne?
Ta jima tana tafiya kafin ta karaso gidan iya mai siyar da nono
Har kasa ta duka tana gaisheta
Iya ta amsata kafin take cewa” kin ga nonon nan yana yi min wuya, ban san me yasa idan kin dauka cinikinki baya fice dala dari da ashirin …..sai dai ki maido mini shi haka du an motsa shi sannan in baki salama ni kam yau ki yi hakuri na sararma masu zuwa gida sara, kinga daman tausayin ki yake saka ni na baki dan ki samu dan kudin kashewa