BAK’A CE Page 11 to 20

Idan ta juya can sai ta juyo nan, kallo take irin na kauyawa sosai jikinta kuwa har zuwa wannan lokacin bata saki ba, sai dai ta rakube jikin Ayya wace take kara rike hannunta dan ta saki jikinta
Direct gidan Sarki aka kai su Ayya, har ciki suka shiga da motar suka sauke su Ayya Walyn sai sauke ajiyar zuciya take ta rabu da alkakai
Har sun juya motar Wardugu ya ce” tsaya
Sojan ya ja ya tsaya ,
Wardugu ya juyo wajen Walyn ya ce” sauka ki kwana wajen Ayya
Walyn ta dago da sauri daga kakabe kakaben jikinta ta zaro ido ta ce” me me ka ce?
Wardugu ya tsareta da wani kallo na kar ki raina min wayo
Walyn ta ce” aman Wardugu , wani irin na sauka na kwana a wajen Ayya bayan ga mijina wajenka na sauka kayana a wajenka komaina na tare da kai? Yama zaka raba ni da kai ka hada ni shakar iska daya da wannan mumunar yarinyar mai siffar aljannu
Yatsina fuska ya yi, a ransa ya ce wai siffar aljannu, ko a ina ta san aljannun ita? A fili kuwa ya ce” Haka na yi ra.ayi
Walyn ta ce” Wardugu kar ka yi min haka, me na maka? Kar ka yi min irin horon nan!
Wardugu ya kalli sojan nan ya ce” sauka mu je
Sojan dai bai ce komai ba ya bude ta fita da bindigarsa yana kallon ikon Allah
Wardugu ma ya fito ya rufe ya tafi wajen sojan ya fara tafiya, sojan ya waiwaya ya ga a yanda suka ajiye motar a bakin hanya, bayan wannan matarsa a ciki, sannan tsakanin fadar da hotel din sojojin akoy tazara, kuma idan mutun ya tunkaro wajen haka kai tsaye daga bakin karfe goma na dare ordre da aka baiwa sojojin shine harbi ba ji ba gani in dai ba a mota ko wani abinda yake malakinsu ba wanda da ya tunkaro wajen akoy adadin odar da aka ce su yi dan shaida su ne wada kowace safiya ake canzawa
Shi dai biye yake da shi da sauri yana hadawa da fan gudugudu suna tafiya har suka fita daga gidan suka dauki hanya (???? sisi kika ce zaki iya da wardugu ko?????)
Walyn wani ihu ta saki a daidai lokacin da ta fahimci wardugu bara mata ya yi motar gaba daya ya tafi a kafa da ya je da ita, Wardugu ita yake wulakantawa? Toh ita kuwa ba zata shiga wajen wannan uwar tasa da wannan yarinyar mai karnin jini ba! Sai dai ta kwana a motar!
Haka ta takure a motar nan ta ki kunna hasken waya dan a gaskiya tsoro take ta kunna waya wani abin ya lura da mutun tun bama dare da ya tsala maguna suka fara kukan jarirai ba,
Kawata, tsakaninki da Allah ke haka rayuwarki wata irin mace ce bahaguma? Yanzu yarinyar nan da kika kwaso kin san asalinta ne?
Ayya ta yi murmushi tana kallon kawarta aminiyarta matar sarki, ta ce” mamanta ta iya tubanci
Anna matar sarki ta dafe kai ta ce” dan ta iya tubanci sai me? Dan ta iya yarenki shikennan sai ki wani kwaso yarta? Kin ce a gidansu kuka daukota
Ayya ta ce” ki gane kawata, lamarin mahaifiyar yarinyar da yarinyar ne akoy sarkakiya, wai kawai dan kalar fatarta shikenan take fuskantar tsangwama, ita kuwa uwar sai kawai ki ji tana yare kuma wai tace itama bata san sunnan yaren ba, kuma ni na yi haka ne dan cika alkawarin bawan Allahnan, baki ga yanda ya tsufa ba aman haka yake nisa lamarinta,
Anna matar sarki ta dafe kanta da hannunta dake cike da zobunnan zinari ta kalota ta ce” ai idan kin lura yanzu wannan matsakar ta zama ruwan dare, a kauye suna kin bakar fata tare da jahilci a birni suna kiyaye bakar mace dan dogon buri irin nasu sannan suna hakan ne da dabara, kina ganni daidaiya zaki ga a yanzu mutun ya tashi ya dauko bakar mace, sai ki ji suna fadin Allah ya basu farar mace koda maya ce, banza idan ta cinye su fa?
Ayya ta dora kafarta daya saman daya tana ajiye tufar da ta gutsura ta ce” ba ko.ina ba, ban ki maganarki ba aman nima nace maki ba ko.ina ba,
Du macen da kika ga ana yi mata duban marar kyau ko anai mata wani gani gani ina mai tabatar maki ita ta saki kanta,
Mace du muninta idan ta iya wanka ta iya kula da jikinta ta iya kwaliya daidai da yannayinta sai ta kara da adu.a kawai
Sannan ita bakar mace da kike ganni baiwa ne da ita, bakar mace tana da kwarjini, bakar mace nada juriya a kowani fani, bakar mace na da kyau mai fuzga, idan bakar mace ta sakar maki tsararen murmushi zaki hangi haske ne a tatare da ita, ke kawata zaki sha mamakin yar amanata in sha Allah
Anna matar sarki ta yi murmushi tana jujuya kanta ta ce” oho dai, kina kare bakar fata dan kina da ita bayan taki mai kyau ce, na rantse maki ko ni na samu taki ina so domin bakinki mai kyau ne, ba gashi ba Wardugu ya samu dan bakinki da farin mahaifinsa sai ya samu kalar fatar nan ta yan ethiopia baki ga yanda fatarsu take ba? To aman wannan yarinyar kina ganni da akace wanka ta saka kuka aman kika biye mata wai kika rakata ta yi baci a haka? Anya kuwa zaki iya wani gyarata?
Ayya ta ce ” ki saka ido kawai…..
Sojan nan tafiya dai yake aman ba karamin gajiya ke tatare da shi ba, sai ya ga Wardugu daga kafa kawai yake yana jefawa yana kara kutsawa cikin duhun garin suna ta sauki su karasa hotel din
Ba su su karasa ba sai kusan sha biyu na dare,
Suna karasawa Wardugu ya saka kai kai tsaye ya nufi shiga wajen da idan ka shigo harbi ne zai salamo maka ………………..
Kadan ne ku yi maneji????????????????
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
1⃣8️⃣
*Godiya ta tabata ga Allah sarkin sarauta ubangijin talikai, godiya mai dumbin yawa gareku da adu.a Allah ya saka da alkhairi ya biya ….*
*Khadijat tawa ta grup BAK’A CE* wannan page din naki ne
Ja sojan ya yi ya tsaya bai san lokacin da ya ce ” Oga, zone interdite ce fa
Wardugu ya juyo yana kallonsa, ya yi murmushi ya ce ” tsoro kake ka mutu sergent?
Kansa ya dan shafa yana kallo Wardugu,
wardugu ya kara cewa” mutuwa fa ko kana kan gadonka sai ta daukeka sergent ba gwara mu tunkareta ba?
Kara kwalalo idannuwansa ya yi yana kallon wardugu
Wardugu ya matso ya dafa kafadarsa ya yi murmushi ya ce” mu je ……
Haka suka kutsa gaban Sergen din nan tamkar ya bale ya fado dan tsoro,
Sai dai ga mamakinsa sai ya ga sun kama wata yar raga a nan Wardugu ya bude ya shige
Shima shiga ya yi yana ta waige waige yana biye da wardugu nan ya hango ashe har sun shiga balbalin hotel din sun fice hatsarin
Wara wawar ajiyar zuciya ya sauke yana biye da wardugu
Wardugu ya rage sauri ya dan rage sautin muryarsa ya ce” nima bana so na yi mutuwar bindiga fa Sergen, ina so na mutu cikin nutsuwa kai da zabi gareni in mutu ina sallah kuma ranar juma.a,
Aman kawai yau ranar asabar gatsai gatsai sai mu tarbi mutuwa? Da juma.a ne ma,
Ya dan yi murmushi ya yi gaba ya barshi nan tsaye yana murmushin shima, kai ogansa idan ya yi wani abin tamkar ba shi ba, wai shifa a nan wasa ya yi masa da rai????
Tun fa wuri ta farka daga bacin da ya saceta, sai dai ta ki motsawa tun a jiya da aka sauketa saman gado ta yi baci ta kasa ta sauko kasa ta kwonta saman farin tls din ta rufa da mayafinta na turkudi tana kallon yanda pankar sama ke juyawa har baci ya dauke, a yanzuma ta farka tun da wuri tana son tashi sai dai tsoro take hakan ya sa ta yi kuri da abin mamaki a fuskarta tana kallon pankar nan, mamaki take menene? Ya aka yi bai daina gudu haka ba? A gaban idannuwanta aka kunna , tunda ya dauki gudu bata ga ya tsaya ba, ita tsoroma take ya yo kasa kasa ya kasheta