BAK’A CE Page 11 to 20

Ayya ce ta bude dakin ta shigo da salama a bakinta
Firgigit Bak’a ta tashi ta zauna jikinta jikin garu tana bin Ayya da kallo
Ayya ta yi tsam itama tana karantarta, a kasa ta kwana du sanyin nan na kasa, sannan da alama bata yi sallah ba
Dukawa ta yi kusa da ita tana kallon yanda take jan mayafinta tana lulubawa a jikinta,
Murya a sake ta ce” kin yi sallah?
Da ido kawai Agaishat ke bin Ayya domin bata san me take fada da yaren tubanci ba
Ayya ta yi dabara ta kamo hannun Agaishat ta mikar da ita ta jata suka nufi bayi
Suna shiga Ayya ta dauki butar karfen dake wajen ta kunna ruwa mai dumi dumi ta cika mata ta nuna mata wajen da zata iya dukawa domin ta san ba wani gane lamarin wc zarai ba tukunnan dai, ta yi mata nuni da ta yi dagara ta yi alwallah ta yi sallah , ta yi mata nuni da har rana ta fito
Da kai Agaishat ta amsata tana kallo sai da ta fita ta duka ta yi fitsari nan inda aka nuna mata ta wanke jikinta ta mike ta yi alwallah tana jin dadin yanda ruwan keda dumidumi
Tana gamawa ta fito ta ga salaya aman ba kowa a wajen dan haka ta hau ta tayar da sallah ta yi abinta cikin nutsuwa kamar yanda Baba tsofo ya koya mata
Tana gamawa ta zauna ta hade kanta da gwuiwarta tana zubar da hawaye, tunani take ya Anna ta tashi? Ya yan uwanta? Ya baba sofo? Wa zai kai masa ruwa? Wa zai gurza masa goro? . …..
Buda kofar aka yi aka kuma shigowa ,
Wannan karon matar sarki ce da wata baiwa buzuwa da kuma Ayya
Ayya ta kali matar sarkin ta ce” so nake a fada mata ina so ta yi wanka ta shirya mu tafi garinmu domin Wardugu yace jirgin karfe daya zamu bi
Matar sarki ta yi murmushi har yanzu tana mamakin daukarwa kai irin na aminiyarta, ita da ko hausar juna basu iya ba
Ta kali baiwar nan cikin isa da dakewa ta fada mata abinda zata fadawa Agaishat wace tunda matar sarkin ta fara fadi take kallonta daga zaunen da take tana fahimtar yarenta
Kafin ma baiwar ta fadi Agaishat ta kallo Ayya, a hargitse ta ce” ina zamu tafi kuma? Kar ki kaini wani wajen kin ji? Ki barni a nan ma
Tana fada ne tana dan nufo su Ayya dake tsaye
Baiwar ta yi saurin tareta , da yaren buzanci ta ce” ki tsaya nan, kin san ina ne kike a nan? Kina garin agadez, a garin agadezma kina masautar agadez, a masarautar agadez ma gaki gaban matar sarki uwar gida sarautar mata,
Ki koma baya ki cika umarninta
Rakubewa Agaishat ta yi tana kallonsu, ta shiga ukunta, ya zata yi? Matar sarki kuma? Ko sarkin garinsu talaka bai isa ya yiwa matarsa ko yayansa wargi ba bale na garin Agadez
Kanta a sade ta ce” zan yi wankan
Ayya dake tsaye ta karaso kisanta tana kamo kafadunta ta kallo aminiyarta ta ce” me ta ce mata? Sai nake gannin kamar ta tsorata? Kar ta tsorata min yarinya fa kar ta rikitata
Anna dariya ma kawai yannayin Bak’a ke bata, ta fadawa Ayya abinda aka yi
Ayya ta dafe kanta ta zabgawa matar nan harara ta ce” ku tafi abinku tunda dai ba zaku tausasa ba, idan ita sarauniyarta ce ke ni ai aminiyata ce, bana son irin yanda kike nunawa kan yarinyar nan, kina manta mutun ce itama ?
Anna ta yatsina fuskarta ta ce” kin ga bara na je na ga in an kawo kayan da kika ce kina so, gaskiya ki yi hakuri ba zan iya wannan faman ba
Ayya na kallo Anna ta juya baiwarta ta bi bayanta suka tafi
Zaunar da Bak’a ta yi gefen gado wace ta takure waje guda, ta juya ta fauko wayarta ta zauna ta danna kira
Ana dagawa ta ce” kana ina?
Amsawa ya yi da” gani gefen aghali muna ratauna wata magana
To ka bari ka zo yanzu yanzu nan bangaren da aka saukeni ina ciki ina jiranka
Da toh ya amsa ya mike yana cewa Aghali ina zuwa
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
1⃣9️⃣
Shiga ya yi ya zarce dakin Ayya ya tarar bata nan sai ya fito ya shiga dayan dakin, daman falo ne mai daki biyu,
Yana shiga ya tarar da ita tsaye , Bak’a kuwa zaune inda ta ajiyeta
Karasawa ya yi yana tambayar lafia?
Ta amsa shi cikin kulawa ta tambayeshi kwannan iyalinshi
Ya yi murmushi dan ya san Walyn bata zo nan ba kennan wajen matar sarki ta je?
Ayya ta ce” Wardugu, zo ka yi mana fasara da y’ata ka ji? Ina son yi mata magana yanda zata fahimta aman ban lamunce maka ka rikita min ita ba ka ji?
Da mamaki yake kallonta, daman shine dalilin kiran nasa? Kai? Yanzu Ayya ya zata yi idan baya nan toh?
Kai kawai ya dan girgiza ya karasa inda Agaishat ta kara rakubewa jikinta ya fara rawa ta nuna alamar tsoronsa take ji
Ayya ta ce” Wardugu ka yi wani abin mana, ka ga tsoronka take ji, bana so dan Allah
Wardugu ya sauke ajiyar zuciya ya kali Ayya ya kara kallonta, uwa uwa hummm
Karasawa ya yi ya dan rage tsayinsa yana kallon yarinyar, kokari ya yi ya saisaita maganarsa ya ce” me ke damun ki?
Kallonsa take ita kuwa, irin kallon nan na kana jiran gannin me za.ai maka
Wardugu ya dan rontse idannuwansa ya bude ya ce” kin ga, mu fa ba mayu bame, ba mugaye bane kamar yanda kike tunani, mamanki tace mu zo da ke, idan kika kwontar da hankalinki kika nutsu sai ina kai ki kina gaishe da mamanki, kinga dai yanda kuka yi da ita ko so kike a mayar da ke ne??
Tsam ta yi tana kallonsa bata bashi amsa ba
Ayya ta matso ta ce” me kake ce mata?
Wardugu ya kali Ayya ya ce” ba komai
Ayya ta ce” to ka ce mata ta tashi ta shiga ta yi wanka , ko na yi mata da kaina ma
Ido Warsugu ya zaro, sai kuma ya basar, ya kaleta sosai ya ce” kin ce Sofo na koya maki karatu ko?
Kai Agaishat ta shiga daga mai
Ya ce” yawa, kuma sofo ya fada maki tsafta na cikin adini? Sai mai tsafta zai shiga aljannah fa
Agaishat ta kara gyada masa kai,
Ya fara jin haushin gyadegyadan kan nan, aman Ayya na wajen ta kasa ta tsare, ya tausasa murya ya ce” toh ki tashi ki shiga bayi, Ayya ta nuna maki kayan wanka ki yi wanka sosai kin ji?
Kai ta kuma gyada masa ta mike tana kallon Ayya, tunda ta ji yace za yana kaita wajen Annarta zata gwada yi masu biyaya ……
Ayya da jin dadi ta rakata bayin ta kuna mata ruwa masu dumi sosai ta bata sabulu da soso sababi, ta bude bruch da maclean ta mika mata ta yi mata nuni da yanda zata yi ,
Har ta juya ta dawo tana nunawa ta ce” ki cuta jikinki lungu lungu sannan ki wanke tafin kafafuwanki kin ji
Kai Agaishat ke gyadawa har Ayya ta gama ta fice
A hankali ta tube kayan jikinta, ta yi tsaye gaban ruwan tana kallon yanda yake zuba
Da tsoro tsoro ta tara hannunta ta janye, ta kuma tara ta janye hardai ta yarda da ruwa ne ke zubowa kuma ba zai konata ba
A hankaki ta shiga tana bismillah a ranta ta yi tsaye ruwan ya shiga kwararun mata a jikinta tun daga kanta dake da kitso kwaya daya tal har jikinta
Sai da ya gama dukanta ta dauki sabulun ta shiga gogawa a jikin soson tana jin yanda kamshinsa ke tashi tana jin dadin kamshin
A hankali ta shiga cuda fuskarta da soson nan ta cudeta da kyau ta darwaye kafin ta shiga wanke wuyanta sosai da bayan kunnayenta da cikin kunnen ta gangaro hamatarta kamar yanda Ayya ta nuna mata ta daga ta kama dirza ta yi kasa ta wanke jikinta sosai ta bi ruwan nan ya shiga darwaye mata kumfar da har ta zama baka dan tsabar datin dake jikinta, tana kallo ruwan na bin yar magudadar ruwa yana tafiya