BAK’A CE Page 11 to 20

Dubansa ya kai wajen Mariama, a hankali ya ce” Mariama?
Dagowa ta yi tana dubansa bata amsa ba,
Baba tsoho ya ce” ina kwana,
Mariama ta kifta idannuwanta ba wani dar ta ce” Lafia, still tana kallonsa
Murmushi ya yi ya yi mata nuni da kofin ruwan dake hannunta sannan ya nuna mata hannayensa.
Tasowa ta yi ta karasa, dukawa ta yi ta kamo hannun nasa ta wanke masa da kanta sannan ta kuma ciko kofin ta ajiye masa ta koma ta ci gaba da gurza goron ba tare da ta furta masa kalma daya ba.
A hankali baba ya fara cin garin nan, yana ci yana dan kallon yannayin Mariama, Mariama ikon Allah, Mariama mai albarka,
A hankali ya ce” nima ina jin rashinta sosai,
Mariama ta dago kanta ta zuba masa ido, murya a cinkushe ta ce” dan me ka rabata da danginta?
Sai da baba Tsoho ya hadiye wanda yake dan tsotsa a hankali ya dan kurbi ruwa ya ce” dan ta rayu cikin nutsuwa, ta samu inci kafin ta yi kaura zuwa lahira
Mariama ta ce” a wajen danginta, a kusa da mahaifiyarta ta fi samun inci Sofo!
Idannuwansa ya dan lumshe kafin yake budewa ya ce” ta yaya? Ta hanyar ta kare rayuwarta a bakin titi? Ita ko arzikin mazan zamanin ta kasa samu idan sun shigo gari da gari dan jar fatar yayanmu ne da gashi da kyau! Ba ruwansu da tarbiya, usuli , da halaya! Burinsu shine au samu iri mai kyau ….bayan su kansu idan suka kalli kansu a madubi zasu gane cewa a da ba haka Allah ya halice su ba, kwonci tashi kuma fatarsu sai ta dawo irin tawa idan Allah ya nufa masu tsayin rai ne,
Su da ka hadata da su din kana da tabacin a inda zasu kaita ba.a kyamar bakar fata? Mariama ta maido masa da amsa du a hargitse da yannayin bacin rai tamkar a lokacin ne za.a tafi da Bak’a,
Baba tsofo ya ce” birni da kike ji ana fadi, wata duniya ce a cikib duniyarmu mai cike da abubuwan al.ajabi,
A birni mutane basu da lokacin dan kina da fata baka ko dan kina da muni ya kasance du idan kin zo waje za.ana kwagirar ki ko a hantare ki! Sannan birnu cike take da mutanen da kwakwaluwarki ba zata iya hasaso maki ba, idan wani ya tsana wani zai so…….Mariama, ku yi hakuri.
Kanta ta mayar ta ci gaba da aikinta, tana gamawa ta ware masa wanda zai ci a lokacin sannan ta zuba masa sauran ta kai kusa da dardumarsa ta ajiye masa ta ajiye tsintsiyar a gefe, ta fitar da sauran canjin kudin ta ajiye saman dardumar ta dauki robar Anna da tulunta ta juya,
Har ta fita ta dawo ta duka kusa da shi kanta a kasa da yaren buzancinta ta ce” ta kasance abokiyar fadana, wace idan na tashi itace kanwata ita nake cin zali, takan kwaso kayana ta wanke min, idan dare ya yi can tsakiyar dare in na je juyawa sai in jita nanake da jikina, sai in rungumeta sosai a jikina ita da marigayiya, sai gashi lokaci guda a cikin kwana goma na rasa su! su duka biyu, ita wace ta rasu ina binta da adu.a baba wace kuwa take raye inai mata adu.a sannan zan yi iya yina dan gannin na kyautatawa wa.inda take so take kyautatawa, haushinku nake ji ku duka har Annar!
Tana gama fada ta mike ta yi gaba abinta .
Baba sofo ya yi murmushi har cikin ransa ya ji dadin haka, ashe dai Mariama na tare da ikon allah, Mariama kennan Allah ya sa ranar da zaki hadu da yar uwarki ki bini da adu.a koda na mutu.
NIAMEY
Doguwar riga fara kar ce a jikinta mai siririn hannu aman tsayinta har kasa, irin mai laushin nan ce bata da kwaliya ko das ta tafi ne ta bi tsarin halitar jikinta,
Kamshi take bazawa du inda ta gota sai fai fuskarta ta cabe da hawaye tana biye da shi,
Murya a raunane ta ce” WARDUGU, nice ya dace na yi fushi irin yanda ka wulakantani, ka banzatar da ni a cikin duhu a garin da ba nawa ba , a garin da na je dominka, ka fice ka barni, sannan da safe da ka dawo ko ka kali motar da ka bar ni a ciki, ka yi tafiarka wajen mamanka ni kuwa ko oho! Shine dan na tafi zaka dauki zafi da ni haka?
Wardugu da ya gama saka mabalin rigarsa ya juyo ya kare mata kallo, a ransa ya ayyana ””’rainin hankali kennan, ta dawo daga tafiarta wace ta isa da kanta , shine aka sha karamar riga aka sha wankan turare aka zo ni ga maye ga mai jira aka kawo min na karbe ko?
Murmushi ya sakar mata kafin yake binta da wani mugun kallo irin na rainin nan, ya dauki yar karamar wayarsa ya bar ta chating din nan ya dauki ky din mota domin garin da hadari hadari baya son ruwa ya foke shi yau, ya fice ba tare da ya furta mata ci kanki ba;
Da kallo ta bi shi kafin take zama bakin bed din tana shafe idannuwanta, bakinta ta zumburo a fili ta furta” zaka sauko ne, haka kawai ka wani hada ni shakar numfashin wannan uwar taka harda wata karin malatin? Naki din wardugu! Na ki na shirya da mamanka duda baka tambaye ni ba na san hakan kake so sai dai ni a gaskiya ba zan iya jure mulkinta ba sai kaceatar wani sarki dan tana uwar General! ……..hum
Wardugu bai zame ko.ina ba sai aeroport, yana zuwa ya ajiye motarsa ya shige ta wajen sojojin dake tsaron kofar bayan sun sara masa ya shige ciki ya haye wajen tarban baki
Bai kai ga karasawa ba ya ji muryarsa ya ce” mek (men),
Juyowa ya yi, arba ya yi da amininsa, abokinsa, Mu.azam zaune saman kujera, gilas a idannuwansa ya saka costume kafarsa sanye da takalmi sau ciki baki sai sheki take…..sai dai abinda bai masa ba irin yanda ya rame
Yana kallonsa har ya karaso inda Mu.azam ya mike tsaye yana murmushi ya bude hannayensa irin ya zo ya rungume shi ,
Ido Wardugu ya zaro ya nuno shi da yatsa ya ce” kai ko?
Mu.azam ya saki dariya yana kara kure Wardugu da kallon yaushe rabo ya mika masa hannu ya ce” Asalamu alaika amini
Wardugu ya karbi musabaharsa yana mai furta” amen wa.alaika salam amini,
Murmushi suka yi kafin suke gaisuwar larabawa,
Wardugu ya yatsina fuska ya ce” kai dai ka cika naci, gaisuwar nan ta wani runguma ba wani sonta nake ba aman sai ka wani damki mutun kato da kai!
Mu.azam ya bushe da dariya yana biye da shi inda soja guda ya karbi jakar Mu.azam dake hannun wardugu ya shiga ja har wajen mota ya bude ya saka masu ya juya bakin aikinsa,
Wardugu ke jan motar yana dan kallon Mu.azam jifa jifa, a kasan zuciyarsa yana tare da damuwa na abubuwan da ya gani a tatare da Mu.azam wannan zuwan, ya rage magana, ya rage fara.a, ga dan cazbi a hannunsa yana dan dadanawa, ga rama da ya tafka ta mamaki sai dai fatarsa ta gyaru ta yi fresh aman ba alamun yana jin dadin rayuwa…..
Haka har suka karasa gidan Ayya wada rabonsa da gidan kwana hudu kennan tunda ya kawo su bai samu aiki ya barshi ya zo ba , aman ita Ayyar ta ue har wajen aikin ta amshi carte dinsa ta banki wai zasu je shopping ita da sabuwar yarta, ya yi murmushi da ya tuna irin kudin da suka kaso, Ayyarsa uwarsa Ayya manya…….
Zaune Ayya take saman kujera tana kallon yanda Agaishat ke dan turo baki tana kallon Ayyar da yannayin abin tausayi,
Daga ita dai gajeran wando da yar rigar da Ayya ta yi mata jan ido kafin ta yarda ta zauna da su dan ta shafa mata gomage a jikinta da fuskarta tamkar amarya, gefe hijab dinta ne baki dan kar kalar abin madarar ya bata hijab din Ayya ta dauko ko dan idan an yi baki, wani irin kulawa Ayya take baiwa Agaishat (Bak’a), kudi ta kashe na mamaki wajen siyen mayuka masu gyara fata ba canza kalar fata ba, sannan ta shiga kasuwa da kanta tare da Agaishat tana nununa mata abubuwa nasu na tubawa na gyaran jiki ta kwaso itacen magarya ta kwaso kayan gyaran jiki suka dawo gida, wata irin shakuwa ce ta shiga tsakannin Ayya da Agaishat, domin Ayya wayayiyar mace ce ta yo anfani da irin yanda ta waye ta ja Agaishat a jiki tun tana tsoro tana baya baya har ya zamana sun shaku tana dora kanta saman cinyar Ayya ta yi baci ba tare da wani dar ba.