BAK’A CE Page 31 to 40

Cike da tausayi take dubanta, su musulmai haka suke ko kuwa wasu da wasu ne? Tana jinjina girman son da Mariama ke yiwa docter mu.azam, in sha Allah zata sama mata takardar su biyu wace zata bata damar zuwa ta zo da shi su shiga aiki, koda bai tashi ba , ba zata tsangwami kanta ba,
A hankali ta dafa kanta ta ce” kar ki damu Docter, ki je zan neme ki, zan nema maki takardar
Da murnarta ta yi godiya ta fito ta shiga office dinta, hotonsu ta kaiwa duba kafin a fili ta ce” wai baka son farar mace ko? Dole ka so ni docter, ni ina son ka????????????
Wayo hanuna????????????????????????
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
4️⃣1️⃣
Ayya ki duba lamarina na roke ki,
Mu.azan ya fada kansa a kasa, kunya ta hana shi dago da kansa ya dubi Ayya domin ya fadi abu mafi nauyi a bakinsa
Da mamaki take kallonsa, so? Aure? Yana son Auren Agaishat? Aman yaushe suka yi wata soyaya da fahimta har za.a kai ga aure?
A nitse ta ce” Mu.azam, aman me ya sa kake sauri haka?
Mu.azam dake kallin kasa ya ce” Ayya , ina so ne a yi mu juya tare da ita.
Aman ai ka san sha.anin aure na bukatar nutsuwa ko? Sannan yarinyar nan amana na daukota daga garin su, eh lale mahaifiyarta ta bani damar ko aure ya tashi na yi mata aman da ransu da lafiarsu ba zan yanke hukunci irin na aure ba tare da yawun iyayen yarinyar ba ko? …. Ayya ta fada jikinta sanyaye tana dubansa
Mu.azam ya gyada kansa, hankalinsa ya dan fara tashi ya ce” Ayya, ki tura ni wajen dagin nata, na je na nemi a bani aurenta, bana son jan abin ne
Ayya ta kuma kale shi da mamaki, bai taba naci kan abu irin wannan ba, jikinta ta ji ya kara yin sanyi, aman Agaishat dinta dukanta ma nawa take da har za.a yi gagawa a lamarinta haka? Sai dai kuma bata tunanin Mu.azam zai wulakanta mata yarinya, duda haka tana son bin hanyar da kakarta ta bi da ita, zasu kai kulansu wajen Allah, a hankali ta ce” yarona, na ji, kuma zan fi kowa farin cikin sannin tana hannu mai kyau, kar ka damu zan san abin yi nan kusa in sha Allah, in dai Agaishat matarka ce zaka aureta kisa ba da jimawa ba.
Cike da murna ya yi mata godiya ya mike ya nufi dakinsa dan yin wanka,
Tsaye take a tsakiyar gidan tana kallon manyan tantabarun gidan dake kiwo nan balbalin gidan , tana yi tana duba kofa domin ranar juma.a da alhinayet ta zo tace zata dawo ranar lahadi su je gidan kitso Ayya sai fadan kitso take,
Kallonta yake daga inda yake tsaye, inda ya shiga takowa a hankali har ya karaso inda take tsaye, ma.ana suka jera,
A hankali ta dago da kanta daga kallon tantabarar ta kai dubanta wajensa , nan da nan ta matsa gaba sannan ta sada kanta kasa cikin yanayi na bawa wanda ke kusa girma.
Aghali ya ce” a garinku ke yar gidan waye?
Agaishat ta dube shi, ta kuma sada kanta, sarkinta ne, ita talakarsa ce, sarkinta ma talakansa ne, dan haka cikin yannayi na girmamawa ta ce” sunnan mahaifina *Ba*,
Ba , ai sunnan du uba ne a garin buzaye! Aghali ya fada yana kara tsareta da ido,
Agaishat ta ce” ka yi hakuri,
Aghali ya ce” baki min laifi ba,
Soyaya kike da shi? Kina tunanin zai mutunta ki zai so ki da zuciya daya?
Kallonta ta dago wannan karon ta sauke kan nasa,,
Bata kai ga bashi amsa ba Wardugu ya shigo da wata galeliyar mota fara kar, kusa da shi Alhinayet ce da ya dauko zai ajiye su wajen kitso wai????♀,
Birki ya ja irin na ka taka baka shiryan nan ba, da bakin gilas dinsa ya dan kale su kafin yake taka motar ya karasa wajen da ya dace a ajiye motar.
Yana tsayawa ya kai dubansa wajensu, gani ya yi aghali na magana, yar gidan Ayya kuwa na kallon kasa, kansa ya girgiza kafin ya maida dubansa wajen Alhinayett ya ce” Alhi, Aba ya saka na yi bincike a kansa, yace bai yarda da adinninsa ba , hakan ne kuwa ba musulmi bane yace shi musulmi ne dan ya saje da jama.ar garin nan,
Alhinayett ta ce” General ya kuke so na yi ne? Ina zan shiga na samo wanda ya yi 100/100? Wannan na uku kennan yana zuwa da niyar aure abin na watsewa tun kafin a je ko.ina, Wardugu bana son auren Lieutenan na fada maka bana son auren soja.
Wardugu ya yi musrmushi yana dubanta ya ce” kuma ki ce ke aminiyata ce, a gabana kina fadin bakya son auren mai sana.ata, me zamu yi maki ne? Me muke yi?
Alhinayet ta girgiza kanta ta ce” Wardugu, bana iya zama da namiji mai mugun karfi, ba zan iya rigimar sojoji ba, ba zan iya firirita irin ta matan sojoji ba, ka san ko ni wacece ban iya fada ba, ban iya ihu ba Wardugu ina son namiji mai sanyin hali ne,
Wardugu ya ce” ba daga nan take ba, sai ki ga kin auri wanda ba sojan ba kuma ya kasance irin wanda bakya so din, kin gane Alhi ke dai ki yi adu.a , aman na san kina son lieutenant sosai, ke ra.ayinki na ba zaki auri soja ba dan bakya son mai fada, wannan ai shirme ne, ni na fi son ki auri wanda yake na san shi , du ranar da ya taka min ke na nuna masa bashi da wayo!
Murmushi ta yi ta kai hannunta suka cafke ta ce” Wardugu, aa fa, ba zaka dakar min miji ba wollah….
Ido ya zaro ya ce” kai, har kin fi son shi da ni?
Bakinta ta yatsina tana hararsa da wasa ta ce” oyah bude na gaishe da Ayya mu tafi kar yama ta yi sosai ,
Idannuwansa ya kai wajen su, nan ya ga Aghali baya wajen aman ita tana tsaye,
Cikin hijaban da Alhinayet ta kawo mata ne ta saka milk mai haske, hijabin har kasa yake mai hannaye sannan tamkar zubin riga aka yi masa ya dinku ya yi kyau sosai, ta saka takalminta mai dan tsini kadan da igiyoyinsa ta daure abinta das da ita,
Ajiyar zuciya ya sauke ya kai dubansa wajen Alhinayett da ya ga ta tsare shi da ido, sarai ta ga me yake kallo duda ya saka bakin gilas ya tamke kar a gane me yake ciki,
Kuma kallon wajen ta yi ta ga Agaishat ta juya wajen kofar falon ayya tana murmushi,
Wajen ta mayar da dubanta sai ta ga Mu.azam ne ya fito cikin shigarsa ta shada ya yi shar da shi , daga inda yake tsayen sai turo mata irin abin nan na soyaya yake sai yace Muah,
Ita kuwa sai ta rufe ido tana dariya,
Tsaki wardugu ya ja ya ce” ji wani shirme kuma?
Alhinayett da lumshe idannuwanta, ta ce” na me? Ba wani shirme walahi sai soyaya,
Dubanta ya yi kafin ya yi murmushi ya girgiza kansa, motar ya bude ya fita inda itama ta fito,
Tafiya ya fara da sauri sauri kamar yanda yake yi kulun, dakatawa ya yi ya dubota ya ce” kuma na saka ya tura magabatansa wajen Aba ,
Ido ta zaro ta ce” Wardugu, Wardugu,
Ina tuni ya yi tafiarsa,
Murmushi ta yi itama a fili ta ce” Wardugu zai min auren dole da soja………
Yana zuwa suka gaisa da Mu.azam ya tsare shi da ido ya ce” haka ka koma kan mace? Ka saka yarinya gaba kana abu irin na yara?
Mu.azam ya daga girarsa ya ce” kai raba ni amini, soyaya ce,
Kai ya dafe yana mai jin matsanancin faduwar gaba, juyawa ya yi ya shige ya barshi nan kar ya hadasa masa hawan jini,
Ayya bata falo dan haka ya haye sama dakinta dan ya san Aghali wanka ya shiga …..
Yana zuwa ya gaisheta kamar yanda ya saba sannan ya zauna daf da ita yana dan mamatsa mata kafarta,