BAK’A CE Page 31 to 40

Ayya ta ce” Mu.azam ya zo min da maganar yana son auren Agaishat,
Wardugu dake rike da kafar Ayya yana matsawa sai tsayawa ya yi tsam da matsawar yana duban kasa,
Baka ji bane? Ayya ta fada,
A hankali ya dago dubansa ya sauke kanta, idannuwansa ya lumshe dan ji yake har kansa ya fara sara masa sanadiyar faduwar gaban da yake ji, me ke damuna? Ya tambayi kansa, me ya sa da an kirayi sunnan yarinyar nan ko na ganta sai na ji faduwar gaba?
Kansa kawai ya gyadawa Ayya,
Bakinta ta yatsina ta janye kafarta da haushi haushi ta ce” Wardugu bafa na son rainin hankali, ya zan fada maka magana ka wani gyada min kai sai kace inai maka wasiya?
Wardugu ya hadiye yawun bakinsa da kyar ya ce” Ayya, wai ya aka yi bakya yiwa sunana kara irin na d’An farin nan? Sai kawai in ji kin kama sunana kai tsaye wai Wardugu,
Ido ta zaro tana dubansa yanda ya yi maganar walahi sai ta ji wata kunyarsa ta kamata, ai kuwa ta juya ta dauki filo ta juyo dan buga masa sai gani ta yi ya fice da gudu a dakin,
Murmushi ta yi ta ce” ja.iri, ja.iri, ja.iri, !
Zan yi magana da yarinyata , in dai tana son sa, zan baiwa Aghali sako ya je da kansa wajen Mahaifanta idan sun amince ya kai kudin aurenta a daura kawai, Allah ya sa Alhairi ne……
To fa????????????????
????????????????????????????????????????
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
4️⃣2️⃣
Alhamdulilah Alla kulli halin…
A wannan rana bayan Wardugu ya ajiye su agaishat saloon dan yin kitso suka zarce park dinsa tare da samarin, inda Aghali ya zabi daleliyar mota irin ta ratsa rairai mai shegen tsada,
Bayan sun gama magana da yaron Wardugu, Mu.azam ya tsaya gurin wata mota mai ruwan ash , karama mai kyan gaske, kallonta yake yana murmushi,
Wardugu ya gama da Aghali yace” ku mu je ….
Mu.azam ya ce” wardugu, wannan motar nake so,
Aghali ya ce” me zaka yi da motar nan kai kuwa? Ta mata ne fa,
Mu.azan zai bashi amsa ya ji lumlumlum lema a hancinsa,
Da sauri ya juya yana mai ciri hankicin a aljihunsa ya goge jinnin da ya zubo masa ta hanci, a hankali ya karasa motar Wardugu ya bude baya ya shiga ya jinginar da kansa jikin kujera,
Ajiyar zuciya yake saukewa yana kara goge jinnin inda wata number ta fara shigowa saman screen dinsa, number saudiya ce,
A kasan zuciyarsa ya ji nutsuwa da number dan haka ya daga ya yi shiru ba tare da ya yi magana ba,
Ajiyar zuciya ta sauke kafin take share dan guntun hawayenta, so take ta yi magana tana tsoron kar ya ji muryarta ya kashe , ta godewa Allah da da ransa, ta godewa Allah da ya daga wayarta duda bai san ko wacece ba,
A hankali ta ce” ina son ka Mu.azam
Sai da ya ji wata kasala, a hankali ya dubi screen din, ya mayar kunnensa, ji ya yi wata nutsuwa na kara ratsa shi, a nitse ya ce” docterna, me kika je yi saudiya a tsakiyar shekara?
Idannuwanta ta lumshe ta ce” na zo rokar Allah ya baka lafia, ya nuna min jininka a duniya,
Murmushi ya yi ya girgiza kai, ya ce” kin ga jini ke zuba a hancina, bayan ina son na yi aure, har na saka a tambaya min auren yar, ina son yarinyar a raina ina son na aureta koda shi kadai zan yi a duniya,
Wani irin faduwar gaba ta ji, jikinta ya dauki rawa, a hankali hawaye ya shiga zarya a idannuwanta, a hankali ta ce” zaka aureta, kar ka damu, zaka rayu Mu.azam,
Shima idannuwansa nasa ya lumshe yana mai jinta gaba daya jikinsa, yana son yarinyar nan fa tamkar ransa, sai dai ba zai yarda haka ta faru da ita ba, ba zai yarda yana ji yana gani ya tsareta haka ba, ya sani ne idan ya nuna mata eh yana so zata sakawa ranta da zata jima da shi bayan yana ji a jikinsa an kusa zare sauran numfashin da ya ragewa gangar jikinsa,
A hankali ya datse kiran inda ya shiga shafa kansa yana mai jin jikinsa ya dauki zafi,, a hankali ya furta Agaishat ki aminta da ni na dan lokaci, ina son ki kema (????)
Wardugu da kansa ya fitarwa da Aghali motar nan dan baya so a komawa su yi mota daya, yana gama fitar masa da komai ya bashi hannu ya ce” aboki, ka gama da Muhsin ni sauri nake,
Amanda aghali ya yi inda ya raka Wardugu da kallo yana ayyana a ransa ko lafia?
Wardugu na tafiya yana sake sake a zuciyarsa, yakan tsinci kansa wani sakarai idan ya ganshi gaban wanda yake so a ransa yana cikin wani halin da ba zai iya fitar da shi ba,
Motar ya bude ya shiga, a hankali ya juya fuskarsa gefensa ya ga ya lumshe ido tamkar mai barci,
Motar ya tayar ya juya a hankali ya nufi saloon din da ya ajiye su Alhinayett
Yana zuwa ya yi mata message cewar ta turo masa Agaishat, yana kofa,
Ba tare da ta tambayi komai ba ta dubi Agaishat da aka gama yi mata tsararan kitso a kanta mai dan girma girma aka saka wani dan roba a karshen kitson dan kar ya warware , ta mugun yin kyau tace da ita ta je mota wardugu na kiranta,
Duda gabanta ya fadi, aman sai ta dake ta mike tana tunannin lafia? Domin yace idan sun gama su yi tafiarsu, wani abu ya faru ne?
Bata da amsar da ta fi ta fice a nitse tana mai jin faduwar gaba,
Wardugu dake kallonta tunda ta fito, du takunta daya na kayar masa da gaban da bai san na meye ba, ya dai ajiye hakan a matsayin zai shige gaban abinda bai taba shiga ba, zai shiga rayuwarsu ba tare da izininsu ba, zai yi iya yinsa dan faranta ran amininsa,
Kare mata kallo yake, a kasan zuciyarsa ya ayanna”””””meye na naci a kan bakar mace? Menene sirin Mu.azam?,
Tana kara kusanto motar yana kara dubanta dan so yake sai ya karanto sirin a tare da ita, ,
Da yake ta gaban motar take nufo motar, kuma Wardugu ne ke tuka motar hakan ya saka idannuwanta sauka cikin nasa, manyan idannuwanta masu ruwan madara da bakin dake tsakiya mai girma wanda ke watso da hasken ruwa ruwa yana sheki , kallon nan mai shige da mai jin bacu shine kallon Agaishat wanda hakan ya samo asali da tun tana karama mahaifinta bata isa ta daga ido ta kale shi ba, sai ta saba da yin kalli a lumshe tamkar zata rufe idon aman kuma ta fi wanda ke kallo tar tar ganni domin wata kibiya ce ke jefo gannin nata har wajen inda ta yi niyar kallo,
A hankali ta lumshe idannuwanta wa.inda ta yi niyar cire nata idannuwan a idannuwan Wardugu, domin kuwa tsai kallo na cikin ido sukaiwa juna wanda basu san da haka ba sai fa ta cire nata ya farka ya yi gagawar mayar da dubansa wajen Mu.azam dake jingine da kofar motar,
Murya a dake ya ce” malan dan bani waje zan tatauna da yarinyar can,
Sai a lokacin Mu.azam ya ga Agaishat ce ke karasowa wajen motarsu , a wannan lokacin har ta karaso sosai jikin motar tana jira a bude mata kanta a kasa,
Mu.azam ya kali Wardugu , murya a raunane ya ce” war, kar ka yi min haka , me ta yi? Dan allah kar ka yi mata fada ko ka rikitata, na tuba ,
Wardugu ya tsare shi da ido yana mai jin wani tsoro a ransa da faduwar gaba, mutun ne shi tamkar kowa, dole abinda zai kayarwa kowa gaba ya kayar masa, sai dai ba zai taba nunawa ba, ba zai taba bari wani ya san halin jin tsoronsa ko faduwar gabansa ba,