BAK’A CE Page 31 to 40

Tsai ta yi tana dubansa, a ranta fadi take…da gaske ne ko kuwa? Me ke damunsa yake magangannu irin haka yau ne?
Bata bashi amsa ba sai lumshe idannuwanta da ta yi ta bude motar tana fadin” Allah ya tsare ka,
Da ido ya bita bayan ta bude motar inda yana kallo Mu.azam ya karaso wajenta da sauri yana alamun tambayoyi inda ya hangi ta sakarwa Mu.azam din murmushi bata ce komai ba, daga nan ta juya ta tafi cikin saloon din.
Karasowa motar ya yi ya bude gidan gaba ya shiga ya tsare Wardugu da kallo,
Wardugu ya tayar da motar ya juya akalarta zuwa gidan Ayya
Tafiyar kurame ne suka yi har suka karasa gidan Ayya, suna tsayawa Wardugu ya daga karamar wayarsa ya danna number ya kara a kunne
Ana dauka ya ce” ka cira min tiket biyu zuwa agadez yau.
Yana gama fada ya katse kiran ya fita a motar shima ya bi bayan Mu.azam
Yana shiga dakin Ayya ya zarce direct, yana zuwa ya tarar da ita tana ninke abin shinfidar da ta cire
Kama mata ya yi suka ninke sannan ya gyara mata wanda ta shinfidar da kyau ya nemi waje ya zauna ya tsura mata ido,
Bakinta ta tabe ta karasa inda yake zaune ta ce” menene?
Murmushi ya yi mata yana dubanta ya ce” sai da wani abu d’a zai kali mahaifiyarsa kyakyawa Ayya?
Kanta ta girgiza , ta ce” da ace uwar bata san halayen dan nata ba, me ke tafe da kai malan?
Wardugu ya yi murmushi kafin yake yannayin magana mai mahinmanci, ya ce” na tambayeta idan tana son sa, amsarta ita ce” *Ina son sa, zan iya zaman aure da shi* , zan je na nema masa aurenta domin shima yana son ta,
A hankali ta zauna tana mai yi masa wani irin duba, ta ce” baku da hankali ne? A me kuka dauki kalmar aure? Sai kace wani abin wasa? To ko yar zan baku ai sai da alwalin da zan gindayawa dokoki kan yata bale ni bamu wani yi magana da ita ba, aikin banza gagawar me kuke haka ne? To naki din!
Kallonta kawai yake har ta dasa aya tana kawar da kai da yannayin haushi a fuskarta,
Murmushi ya yi , a hankali ya ce” Ayya, aure ai tayashi ake ko? Sunnar mazon Allahn salalahu alaihi wa salam din kike cewa baki bada ba? Haba Ayyana,
Yatsarta ta nuno masa ta ce” Wardugu ka kiyayeni, ni ban ce ba zan bada kwata kwata ba, aman yannayin yanda kuke maganar ne ya fara bani tsoro, meye na gagawa bayan kun san aikin shedan ce? Sannan yarinyar nan dai amana na dauko daga gidansu, idan wani abin ya sameta ba zan yafewa kaina ba!
A hankali ya dawo kusa da Ayya ya zauna, hannunta ya kamo ya rike yana dubanta ya ce” abinda ke sakawa ana jan aure bincike, da halin rayuwa na yau da kulun, Mu.azam namu ne, mun san waye shi, sannan Allah ya hore mana abinda zamu kawo mu nemi auren ko nawa ne, Ayya, bana son mu zurfafa bincike ne, ina so ki yi min lamuni ki duba , ba zan saka kaina a maganar idan na san shirme ne, ba zan tarki tarbenta a haka da garage ba idan na san cutarwa ne wa amanarki, ina iya yiwa aminina alwali, kuma tare da shi zamu tafi namiji alwalin kansa ne, ki taya mu raya sunna da yar ki, kina da damar bibiyar rayuwarta da shi …idan an yi maki abinda ba shi ba ki raba
Ayya kam du jikinta ya yi sanyi, tana dunansa gabanta na faduwa tana ayana lale da kwakearan dalilin da ya saka Wardugu shiga wannan maganar auren,
A hankali ta ce” menene? Me ke faruwa ne?
Wardugu ya kara sada kansa yana jin yanda zuciyarsa ke bugawa ya ce” alkhairi ne, ki taya mu.
Can daman Ayya ba mai musa maganar wardugu bace, hakan ya sa ya yi gagawar shawo kanta kan zasu je garin su Agaishat neman aurenta wa iyayenta……,
Bai bar dakin Ayya ba sai da ya tabatar da ya samu kanta ta bada amanarta da dukan yawunta, ta yi fatan alkhairi
Haka ya fito ya tisa keyar Mu.azan dake cike da mamakin lamarin sukaiwa Ayya salama suka nufi aeroport dan tafia garin agadasawa su nufi timiya gari mai gawo ????
……..sowi kadan ne…..
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
4️⃣4️⃣
Basu dauki tsahon lokaci a jirgi ba Allah ya sauke su lafia,
Direct hotel suka nufa infa Wardugu ya yi kira kan q shirya masa mota da yan tsiraku sojoji zasu je kauyen Timiya,
Sai bayan ya yi wanka ya mike saman bed ya danna wayarsa ya danawa hajia Walyn kira yana mai lumshe ido,
Daga bangarenta ta daga tana duban agogon dake dakinta, hakimce take ta hada uban maltina tana son kwankwada tana tsoro, ance mata yana zubar da jaririn ciki wai, dan haka ta gyara zama da niyar sha sai ga kiran Wardugu,
Dagawa ta yi gabanta na faduwa kar a je ya zo yana nemanta ne,
Walyn……..ya fada yana mai jan sunnan,
Idannuwanta ta lumshe ta kwontar da kanta saman hannun kujerar tana sauraron yanda ya wani ja sunnan har tsakiyar kanta,
Bakya neman mijinki wuni guda? Ki ji na ci abinci? Me ke damuna? Da wa na hadu? Karshema inda nake? Ko kin yarda da kanki har haka ne?
Walyn ta yi murmushi ta ce” na yarda da kaina ne,
Murmushin ya yi shima ya ce” baki da matsala,
Kana ina? Ta jefo tambayar
Wardugu ya daga kai yana karewa dakin kallo ya ce” ina hotel , a Garin Agadez.
Me? Hotel? Agadez? Yaushe ka je? Me ka je yi? Kuma a hotel? Kai da wata yar iskar?,
Idannuwanda ya lumshe, a hankali ya dora hannunsa na hagu saman kansa, shafawa yake yana lalabar kansa, shiru ya yi mata wanda hakan ya saka take ta kiran sunnansa da karfi tana fadin ka fada min da wata tsinaniyar kake hotel? Har ka bar gari da gari ka je garin agadez? Me ka je nema? Farin, kyan, ko gashin? Wanene bani da? Ka ban amsa Wardugu,
A hankali ya katse kiran da wayar baki daya ya furzar da wata zazafar iska ta kai dubansa wajen Mu.azam da ya yi tsai cike da takaicin matar abokin nasa yana dubansa, mamakin irin rashin hankalin Walyn yake, du yanda wardugu ya kai ga zafin rai yana raga mata, yana matukar kawar da kai a shirmenta, tunda ya zo niger bai ga inda Walyn ta taka kafarta gidan mahaifiyar mijinta dan ta gaisheta, bayan kulun sai ta fice yawo kwararo kwararo,, ga abubuwa na rashin da.a da take shukawa suna zuwa kunnuwansa , sai ta tafkawa talaka rashin mutunci ta yi ikirarin me ka isa ka yi bayan ikon a hanuna yake a matsayina na matar General Wardugu,
Karfi da yaji ta saka wasu talakawan na shayin tunkarar iko koda da gaskiyarsu , suna tsoron gawo ya juye da mujiya! Sam halayar Walyn suna bukatar gyara,
Bai iya cewa Wardugu komai ba, domin du tsakaninsu basa irin maganar nan, sam Wardugu baya bada fuskar a yi maganar iyalinsa da kowa, idan abu ya ishe shi yakan ja dogon numfashi ya ce” Mata kennan, kwakwaluwarsu irin ta yara ce,
Wardugun ma dubansa yake har ya karasa wajen bed yana dana waya ya ce” Wardugu, yanzu kayan buzaye ne zamu nada , kawai kai tamkar diarhee kake idan ka tashi abu yi kake? Bamu wani shirya ba, bamu zo da datijo ba zamu je a bamu aure? Ni dai kar ka ja iyayen yarinyar su hana min Agaishat ba zan jure hakan ba , zan haukace maka ne!
Tsuru ya yi masa daga kwoncen yana jin wani iri da maganarsa, wani irin tashi ya yi zaune yana dubansa ya ce” kai zo zauna mu yi magana!