BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 31 to 40

Baba tsoho ta tarar yana yiwa Wardugu magana kansa a sade yana sauraronsa inda jikinsa ke fitar da hucin zafi gaba daya bashinda laka tamkar wanda ruwa ya daka zazabi ya rufe shi, zuciyarda kuwa ba dadi, dandannon bakinsa daci firit, sam baya jin dadin yannayin ranar nan.

Tana zuwa ta tsuguna infa suke, 

Muryarta na rawa cikin yaren buzanci ta ce” me ya same ta?

Idannuwansa ya dago ya sauke kan fuskar Anna, duda turkudi ya rine mata fata ba wani kula take samu ba, aman idan kana neman ainahin kyau, tsararan kyau ka ja ka tsaya wajen Anna, Agaishat kama take da ita sai dai hasken fata da ya bambanta, yaren tubanci ya juye da shi inda ya shaida mata komai cikin nutsuwa da sada kai da girmamawa,

Kunyarsa ce ta kamata, har ta hanata yi masa wata tambaya, 

Kanta ta sada bayan ta hangi Mu.azam dake tsaye ya rungume hannayensa yana kallonsu ta kawar da dubanta ta mayar wajen Wardugu,

Muryarta a nitse ta ce” *kar ka damu da bani hakuri d’ana, na saba da gannin auren yayana a wulakancema bale ita nata kun mutunta, ai dama halal malak na baiwa Ayya Agaishat, koda a can kuka daura mata aure bani da ja, fatana zaku ci gaba da riketa da amana, sannan ba sai ka kawota ba, ka barta a can kawai bara na kawo maka sako ka bata, ka fada mata Ayya uwa ce a wajenta, ta yi mata biyaya!*

Asalamu alaikum,

      Rayuwa ce da aka yi nake bi maku, duda na rufe abu dayawa, na kuma gyara wani dan labarina ya yi ma.ana, aman kar ku manta rayuwar nan an yita, kuma a gidan bak’a akoy Alhinayett dake yayata uba daya, team Mu.azam da Wardugu,,…..ku biyoni sanu zamu ji meye sirin, sanu zamu yi murmushi????????????????????????????????????

Hhhh yau kam na cika da yawa????????????????

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        4️⃣5️⃣

Yana kallonta ta shige bata jima sosai ba ta fito da yayun Agaishat, inda Mariama ta hade rai tamkar ta zunduma ihu dan bacin rai, 

Sai dai suna zuwa wajen Wardugu ta ji ba zata iya yi masa wulakanci ko kashedi ba, dan haka ta sada kanta ta ce ” Amana kanwata,

Kalonsu kawai yake har suka koma inda Anna ta bashi wani zani a kule wanda bai san ko menene ba,

Kamar bashi da laka haka ya mike jiki a sake inda su Mu.azam suka kama baba tsoho suka saka shi a motar suka dauki hanya,

Mu.azam na lure da yannayin Wardugu, inda gabansa ya yi ta faduwa kan lamarin, tambayoyi me cike da zuciyarsa *Me ke damun Wardugu? Me ke adabarsa haka? Bashi da lafia ne? Me ya fauke murmushinsa?*

Sai dai bashida mai bashi amsoshin tambayoyinsa domin rabinsa da jin muryar wardugu tunda suka baro kofar Baba tsofo inda baba ya baiwa Wardugu wani kuli a baiwa Agaishat shima harda carbi fari ya shaida masa cewa ya fada mata bata da gata sai na Allah.

Rike yake kamkam da sakon Baba da Anna, carbin kuwa sai ja yake yana duban hanya har suka karaso garin Agadez,

Fir Wardugu yace qi sai dai su tashi a jirgin sojoji , inda nan da nan aka taso daga garin niamey aka zo Agadez aka dauke su su biyu tal aka juya da su duka a cikin awowi hudu har jirgin ya sauke su inda dare ya fara tsalawa,

Tunda ya fito a jirgin ya daga kansa sama, garin niamey da yannayin zafi hakan ya sa ya fara jin har kamar ya cire rigar nan ya yar, 

Dubansa ya kai wajen Mu.azam ya kirkiro murmushi ya ce” zan karasa gida, zamu hadu gobe in sha Allah, 

Mu.azam ya amsa shi da kai yana kallonsa har ya bace masa da gani, 

Wardugunsa ne ya juye haka lokaci daya? Hannayensa ya dora saman kansa ya furta” innalilahi wa ina ilaihi raj.une, me na aikata haka? Na kutsa wajen da ba nawa bane ko me? 

Da sauri ya kawar da zacen nan ya nufi wajen da ya tabata ba za.a rasa motar wardugu ba dan yawan tafiye tafiyensa yakan zo da mota ya bari a aeroport,

Yelemun kuwa ya samu ya shiga ya tayar ya nufi gidan Ayya ransa cike da tunani, 

Wardugu bai zame ko.ina ba sai kofar gudan su Alhinayett

A lokacin karfe goma na dare ya kusa, anguwar ana dan kai kawo domin ba laifi suma anguwar yan gayu ce, manyan yan mata da samari sai kai kawo suke suna bada kala.

Wayarsa ya danna mata kira, tana dagawa ya ce” ina kofa,

Da sauri ta mike ta daga labulen tagarta, hango mutun ta yi duke a kofar gidansu, 

Da sauri ta fito da zumbulelen hijabinta infa kanwarta dake kusa da ita ta nace ita sai ta bita,

Dubanta ta yi da kyau ta ce” *Tghmass*, wajen yaya Wardugu ne fa?

Thgmass ta turo baki ta koma saman bed tana kunkunnin je ki, ba zan biki ba ya yi min muhunta wannan katoton da bai san yara ba!

Murmushi ta yi ta fice da sauri ta fito ta karasa da sauri tana fadin” Wardugu lafia? Me ke damunka? Me ya faru? Baka taba zuwa gidan nan a wannan lokacin ba, menene? Wani ne ba lafia?

Wardugu ya dago kansa daga duken ya kamo hannunta na dama murya a dake ya ce” Alhinayett, zuciyata ke min ciwo, ina jina tamkar zan mutu, ina jin dari sosai, na kasa tabuka komai, ina jin tamkar na rasa wani baban abu a rayuwana, ina jin iskar duniya ta yiwa kofofin hancina kadan, ji nake tamkar jikina na gasuwa da wani irin azabeben zafi da sanyi, ina jin jikina ya yi min nauyi, Alhinayett me ke damuna? Menene wannan?

Ban taba jin wannan abin ba, mutuwa zan yi!

Da sauri ta dafe kirjinta gabanta na bugawa,

 A hankali ta duka inda yake ta ce” innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Wardugu baka da lafia ne? Jikinka zafi, ka je asibiti ne? Daga ina kake yanzu? Ayya ke ce min ka je Garin su Agaishat nemawa Mu.azam aurenta, ko ka yi gamo ne? Bara na kira Abanmu,

Kokarin tashi take ya riko hannunta ta dawo gwarab kusa da shi tana share hawayen amininta yayanta a wani hali, a firgice ta kuma fadin” ka bari na tado abanmu ya baka magani ya yi maka turare ko ka yi gamo da wani mugun ne Wardugu

Wardugu ya ce” bana tunanin hayaki, tashin hankali, likita, kudina, ko mulkina zasu warkar da ni, tabas zuciyata sakara ce banza ce da take da gagawar yanke hukunci, ke kin fi kowani makusancina saurarata , na zo ne dan nima yau ki saurareni kamar yanda nake sauraronki, Alhinayett, a yau da inada mace nutsatsiya da na kwontar da kaina saman cinyarta ta taya ni saisaita bugun numfashina, Alhinayett halayen Walyn na tayar min da hankali, ina sane, ina hankalce, kawar da kai ne nake dan ta kula da kanta ta gyara, Alhinayett nima mutun ne, kuma inada rauni fa, ina da zuciya, ita a kulun hirarta da ni tuhume tuhume da zargi ne, a jiya jifana ta yi da maganar wai ina tare da watatsinaniyar? Ni ba mashayi ba, ni ba mazinaci ba, aman ta ki godewa Allah sai fata take yiwa kanta? Yau da zinar nake ta isa ta hana ko ta yi wani abin? *Wani lokacin nakan dauki niyar zuwa na yin na ga sai me?* (hatara mata, walahi yawancin lokuta mu ke jawowa kanmu masifa da bakinmu da banzan tunanin mu), sai dai har yanzu ban aikatan ba, 

Alhinayett sauraronsa take cike da yannayin tashin hankali, ko me ya firgita mata Wardugu ba karami bane, meye shi da yace ba zai iya masa ba? Ya fi karfinsa? Meye wannan? Gashi ya hanata kiran Aba, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button