BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 41 to 50

Yana tuki har ya karaso gidan Mu.azam

Agaishat ta sala wankanta ta saka wata doguwar rigar sai dai bata kai har kasa ba da dogon wando a kasan rigar ya rike kafarta tam dan rif ne da shi daga can kasa wajen idon kafa,

Tana zaune a falo suna vidio Call da Ayyanta, sosai Ayya ke yi mata hira dan sakata nishadi inda ta maida hankalinta har tana murmusawa sosai tana tambayar ayya abin tambaya tana bata amsa daidai labarinsu

A haka karaurawar dakin ta shaida da mutun wato ana son shigowa,

Mikewa ta yi tana warware dan kwalin dake daure a kanta ta yana shi a fuskarta ta je ta danna wajen budewa dakin ya bude,

Kallo daya ya yi mata ya ce ” mu je,

Da wani dan gudu gudu ta juya da wayar tana fadin” Ayya, ya Wardugu ne zamu tafi wajen Mu.azan din,

Da sauri ya juyar da kansa daga kanta, irin fizgar jikinta da ta yi bai kai idannuwansa da gangan ba sai akasi da aka samu yana tsaye a wajen,

Astagafari ya shiga ja yana zabgawa idannuwansa fada, fitama ya yi a gidan ya je wajen motar ya zauna yana jiranta har ta fito da lulubeben hijab dinta mai ruwan blue da takalmi plat blue sai carbinta, ko wayar bata dauko ba ta barta a gida,

Suna zuwa suka tarar da Khadija tsaye wajen da ake hangen Mu.azam din, ta jinginar da kanta jikin madubin , tana kallon wajen wanda basu san adadin lokacin da ta dauka a haka ba, basuma san ko ta je gida ta dawo ba, su dai sun tarar da ita,

Jin motsinsu ya fargar da ita zuwansu, juyowa ta yi gare su ta sakar masu murmushi kafin murya a sanyaye ta ce” sannun ku da zuwa,

Agaishat ta karasa inda take tsaye ta ce” ina yini, ya mai jiki? 

Khadija ta waiwaya eajen madubin ta waiwayo ta sauke ajiyar zuciya ta ce” Alhamdulilah,

Wardugu kam bai amsa ba ya zarce wajen madubin ta tsaya yana kallon yanda aka dadaura masa na.urori da mai taimakawa lumfashinsa, da mai aiki jikin bugun zuciyarsa, da wada in ya motsa zata yi kara, da karin ruwan dake jone , da ledar fitsari a ajiye gefe wace idan ta cika ake tsiyayewa, da fo kasan bed din, 

 A hankali Agaishat ta karaso inda yake tsaye itama itama ta tsaya ta kai dubanta inda yake kallo,

Idannuwanta ta zaro tana duban Mu.azan da tsoro karara a fuskarta, ai kuwa me zata yi in ba kuka ba? Ta aniya fashe masu da kuka tana nuna yanda Mu.azam yake kwonce,

Hankali tashe Wardugu ya dubeta, nan da nan ya turbune fuska tamkar bai san wata halita daria ba, rai bace ya ce” la ferme tu veut? (Chut up nah?!) , 

Ki rufe min bakin ki ! 

Ba wani da ihu ya yi maganar ba, sai dai a kausashe ya yita wanda dole ka yi shiru ko baka shirya ba,

Tsorata ta kara yi ta shiga ja da baya baya , 

Khadija bata taba jin Matar Mu.azam ta bata tausayi sai yau ba, dan haka ta rike hannunta ta baya ta jata suka fice a wajen,

Kuka Agaishat take tana shasheka inda du ta tsorata da komai, 

A hankali Khadija ta zaunar da ita a balbalin wajen kusa da fulawowi, 

Da tsinkakiyar hausarta take son rarashin Agaishat dan haka ta ce” ki yi hakuri, zai samu lafia, ki bar kuka kin ji?

Agaishat dake dubanta zuru bata iya amsara ba, dan haka Khadija ta jimke hannayenta , da kanta ta yi mata alamar ta kwontar da hankalinta sannan da dayan hannun ta yi mata nuni da sama cewar Allah na nan,

Ajiyar zuciya ta sauke ta sada kanta,

Wardugu ne ya karaso wajen ,

Ganninsa ya saka khadija ta mike ta yi masu salama ta koma ciki,

Wardugu ya zauna yana lura da yanda Agaishat ke dan ja baya, tsorata take son yi da shi baki daya dan haka ya zauna yana facing dinta,

A hankali ya ce” menene na kukan? Bakya so ki rasa mijin ki? Bakya so ya mutu?

Agaishat ta dube shi da sauri, bata san lokacin da ta ce” Wardugu,,

Sai kuma ta sada kanta kasa, a hankali ta ce” bana so ya mutu, *ina son sa*,

Shiru ne ya biyo baya, 

Jin shirun ya yi yawa ya saka ta dago a hankali, dan ta ji kunyar fadin gatsai gatsai tana son mijinta, sai dai itafa iya gaskiyarta kennan, duda da alama shi hankalinsa rabe yake gida biyu, zata zauna da shi, to meye ma fan ya so watanta? Ai ba ita kadai ce mace ba, dan haka ita ba wani zata ja ba, yo irin rayuwar da ta gani a gidansu da Ba ke sheka abinda ya ga dama Anna ta bi shi ita mema akai mata? Ba zata zama mai raki da rashin godiyar Allah ba,

Wardugu dake zaune tamkar mutun mutuni gannij zata dube shi ya saka shi mikewa da sauri ya yi gaba,

Da sauri saurin itama ta bi shi dan ta fara karantar halayensa , yakan yi magana da ido, ko da jikinsa.

                       *Timiya*

Gari mai gawo, Timiya garin sarki ne, 

Yau aka zana sunnan Gimbiyar garin Timiya, sarauniyar birnin zuciyar sarki wato Gaishata,

Taron sunnan da ya tara mutanensa na arziki, garin ya dauki jama.a ya cika makil inda aka soke amale biyar aka yanka aka shiga gashi da wasu wasu aka kai wajen madafa inda mata ke tone alkabut da gurasa na kasan kasa suka aza miya,

Cuwa cuwa ake wanda sai ka leka bangaren Amaryar jego zata ci karo da mamaki,

Wato amarya ce hakimce cikin shiga ta alfarma sabon turkudi mai fari da maroon, ta sha sarkar zinari da amarwaraye, hakama yan uwanta sai kai kawo suke sunna tarbar baki inda dakinta ya sha sababin kayan daki da gado sabo dal irin na yan birni ga inji ya bada wuta panka na sheko masu sanyi, jariri a lulube a wajen tsohuwa mai kulawa da mai jego,

Kadan kadan zaka ga Mariama ko Fatimata sun duko wajen bakinta ta fada masu abin tambaya ko na shawara, cike da aji su fice su nufi gidan da sarki ya maido su kafin a gama zanen sunna su daga wajen Anna dake zaune cikin runfar kara mai sanyi saman tabarmar leda ta sha jan kunshi a kafafuwanta da hannayenta, ta nada lifaya ja, idannuwanta dauke da kwali shar, sai zobuna da awarwaraye na zinari da ta saka itama uwar mai jego ta kuwa hakimce abinta , su zo su fadi maganar yarta ta fari ta kuwa mike idan na mikewa ne ta yi iya yinta dan gannin ta daidaita komai, idan sako ne ta tura daga inda rake cike da aji da sannin abinda take yi a je a yo a zo har yama ta yi aka shigo da kyautar kayan jariri da na uwarsa daga mai girma sarkin garin timiya….

Mai karatu zai yi tambayar ina ta samu kudade haka na sayen zinari?

*Ba* na ajiyar kudadansa idan ya samu a cikin gidansa, kuma Anna itace kadai ta san ma.adannin kudin aman koda yinwa zata kashe su ba zata iya tabawa ba dan tsabar tsoron ransa ya bace, 

Bayan warwaren kulin da ya kula mata, ya kasance su har yanzu basu da labarin inda yake dan haka ta je da kanta ta kwaso baki daya kudaden da suka rage wanda bai masu mugun kashewa ba ta zo ta samu sarki a lokacin da suna ya matso ta bashi ta zana masa bukatarta baki daya yayanta harda Agaishat wace kudin aurenta ne danma sun tafi da sadakinta, ta saka a yo masu sarkar zinari da awarwaraye, ta saka a kawo masu turaren wuta na arziki da na feshe na ruwa masu kanshi, ta saka a kawowa yan matan kayan kwaliya da lale na hausa da sauransu, ta saka a yo masu siyayar kayan jiki ba wasu masu yawa ba aman masu kyau da tsada da ma.ana, nan ta kawo maganar kayan dakin Gaishata inda sarki ya nuna a bari yana da niyar canza masu su duka matan nasa, duda haka ta nemi alfarma ta kara wasu abubuwan irin zannin shinfida na gado, kayan jere na zamani, karshe dai kudin da suka rage a hannunta basu fi million daya ba inda Mariama ta kawo mata ta wajen Ba da ya basu ta hada ta rike a wajenta da niyar zasu rike saboda hanya. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button