BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 41 to 50

Bayan zanen suna da kwana biyu,

Zaune suke suna kallon yanda Anna ke gyara miya , suna yi suna hirarsu a nitse ba wani hayaniya ko rawar kai, 

Gashi gidan ya bade da sanyayan kanshin turaran wuta

Dogari ne ya yi salama daga kofa,

Mariama ta leka nan yake shaida mata sakon sarki na yana son magana da Sirikarsa

Kimtsawa Anna ta yi, ta saka hijab sai baza kanshi take ta nufi gidan sarki

Tana zuwa ta karasa bangaren y’arta ba wani dari dari ko labe labe irin na da,

Sun jima suna hira tsakanin Anna da gaishata kafin sarki yake karasowa,

Kan maganar tafiarsu ne, Sarki ya shaida masu in sha Allah zasu je agadez a jibi, su gana da sarkin agadez sai ya sada su da *Gukunnin*

Amsawa Anna ta yi , sannan suka kara daidaita maganar inda dole dai da Gaishata za.a tafi dan ta kafe , yanzu kuwa Anna ta zama mai son y’ayanta, tausayinsu na mamaye zuciyarta, takan yi tir da wannan rayuwa, sai kuma ta godewa Allah da ya dawo da ita hanyacinta tun yanzu.

   

                 *After 2 weeks*

                            Paris

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________

             

*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          5️⃣6️⃣

              Barka da juma.a

A kwanakin nan 14 da aka yi ,duka kaf Wardugu na nan , ba.inda ya je, yana tsaye kan lamarin amininsa, du wani abinda za.a fitar da kudi komai nauyinsu yakan karba ya je ya dawo da abinda aka bukata, 

Ya kasance du idan lokacin cin abinci ya yi zai fita ya shigo masu kowa da nasa ci uku a yini,

Yakan yi jim idan ya ga sun yi jigum jigum ya ce da su” zai tashi, ku mu yi masa adu.a

Wannan abubuwan ya saka Khadija ta mugun zube kasa, wato ta ga ita ba komai bace a wajen son kyautatawa Mu.azam, wani irin girman wardugu da kwarjini, da kunyarsa suka karu a wajenta,

Ya kasance a yanzu ta yarda ba ita ta fi kowa son Mu.azam ba, sannan ta dan ja baya in dai Agaishat na wajen takan rage yawan leka wajen da Mu.azam din yake ma, sai dai idan bata nan kuma zata je ta tsurawa wajen ido,

Agaishat kanta da ya kasance kulun da sasafe zai zo ya dauketa su je asibiti, idan abinci zai je siya sai ta fadi wanda take iya ci, idan rana ta yi ya mayar da ita gida kuma sai bayan magariba ya daukota, duda ba wani hira ke hada su ba, sai kusancinsu ya karu, shakuwa ta shiga tsakaninsu, wanda hakan ba karamin illah ne ga dayansu ba, 

Idan ya kawo abinci bata ci ba kuwa zai kama dago kansa jefi jefi yana duban abincin ya dubeta ya kawar da kansa, idan har ya ga lokacin cin abincin zai shige bata ci ba zai mike daga inda yake ya zo ya bude ya ajiye mata ba tare da yace da ita kala ba ya koma mazauninsa, 

Kudi sun ji jiki, wai danma wasu abubuwan rabi yake biya albarkacin yana ma.aikacin asibitin, sannan likitocin nan tsaye suke kansa, baban likitan kansa ke kula da komai na Mu.azam har zuwa wannan rana inda suke tsaye a kofar su duka suna hangen likitoci uku dake tsaye kansa,

Tunda safe ya dace ya motsa, aman shiru ba alamu,

Wannan zuwansu na hudu ne wanda ya kama karfe shida daidai aman shiru Mu.azam bai motsa ba,

Zuciyoyi sun karaya, hankali ya tashi, a tsaye suke cir da kafafuwansa inda cikinsu ba wanda ya saka komai a bakinsa bale ya kai cikinsa, kai da azumi ma Wardugu ya tashi, su kuwa ba wace ta kula da wani cikinta ,

Agaishat hankalinta a karshen tashi yake, dan sala sala khadija ta kwatanta mata komai a jiya da yama, dan Gaskiyarta ta fadawa khadijar cewa ita ba karatun boko ta yi ba, bata san komai game da abinda ke faruwa ba,

Khadija ta yi mamaki ainun, daman wanda bai yi karatun boko yana iya zama wayis haka? Ita bata ga wani kauyanci a tare da Agaishat ba, ko aman da ta yi ta kelayawa a jirgi ta yi tunnanin ko irin mutanen nan ne da basa son tafiar jirgi ko mota yanzu sa kama amai, du kai kawon nan da ake a tunaninta ta gane komai idan likita ya fito ya yi bayani da french a tunaninta ta iya ta san me aka ce, 

Kwarai ta ji ba dadi, ta yi tunanin da itace fa? Hakan ya sa ta zauna ta yi iya yinta da kwatance da cicirarar hausarta ta fada mata komai a nitse wanda sai da ta yi data sannin fada mata dan sai a lokacin Agaishat ta birkice fiye da da ta ringa irgen lokaci tana fadin ya taimaka ya buda ido, ita a barya ta je ta tashe shi,

Wannan karon wardugu bai iya wani tsawata mata ba, shima zuciyarsa a hautsine take

Jikinta duka rawa yake, a hankali ta kai hannunta wajen Khadija dake tsaye tamkar ba jini a jikinta ta damie hannunta ko zata ji sasaucin tsoron da take ciki,

Khadijarma ta rike hannun nata gamgam suna gannin yanda likitocin ke ta aune aune suna magana suna rubutu a takarda,

A yannayin da suka fito, dole ne hankali ya tashi,

Wannan karon kam ba wani boye boye suka tsaya gaban Wardugu, Khadija, da Agaishat suka yi masu bayannin bai farka ba kuma basu san dalili ba, 

Sun auna basu ga abinda ya tare mashi farkawar ba, 

Suna fadi ne fuskarsu cike da alhini,

Khadija ta kwala kara ta ce” non, non impossible non (no, no imposible no!),

Wardugu dai na duban likitan dake bayani, ya ci gaba fa fadin” cikin wasiyarsa ya bar maganar, in dai bai farka ba, kar a ci gaba da rayashi da inji, a cire masa injin dake taimakawa lumfashinsa a bar shi ya tafi, lokacinshi je ya yi ba yanda za.a yi, dan haka ku saka ranar da za.a cire masa na.urar dake bashi lumfashi,

Wayo ba za.a cire ba, wayo na shiga uku, Mu.azam kar ka yi kin haka, Wardugu ba za.a cire masa ba, in dai kuka cire mashi kun kashe ni nima walahi ko kwana daya ba zan kara ba sai dai ku kaimu mu biyu, khadija ke fada tana girgiza Wardugu kan kar ya saka hannu a wannan decision din,

Agaishat ta matso da sauri ta kama dayan hannun Khadija itama tana kuka a rikice da yaren buzanci ta ce” ya mutu ne? Ya mutu? Khadija Mijina ya mutu? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une ,

Ta cika hannun khadija ta damki na Wardugu fake tsaye yana dubansu zuru tamkar bai san yaren kowace cikinsu ba, tamkar wanda ya rayu cikin jeji shi kadai, sun zame masa sababin halita a gabansa,

Agaishat ta rike shi da kyau ya dago hannunsa ta dora gefen fuskarta ta girgiza hannun da kyar ta ce” Wardugu, ya mutu? Mutuwa ya yi? Wardugu ya mutu ne? 

Wardugu ya janye hannayensa a jikin nasu ya juya da wani irin sauri ya fice a wajen baki daya,

Khadija ta zube kasa tana kuka inda likitocin abokannan aikinta ke rarashinta, Agaishat ta karasa jikin madubin ta jinginna kanta ta hadiye kukan a ranta ta shiga zabga masa adu.a tana tofawa tana duban ba.a rufe shi ba,

Wata likitar ta zo wajenta itama ta shiga rarashinta tana dafa kafadarta da yaren frency inda Agaishat dubanta kawai take aman bata san me take fada ba, ita dai zuciyarta ta cunkushe kukan ya tsaya cak, adu.a take ta yi kan Allah ya sa ba mutuwa ya yi ba!

Wardugu na fita ya je ya tsaya bakin titi ya tsurawa hanya ido,

Ba komai idannuwansa ke ganni ba sai zaman da suka yi da Mu.azam, abubuwa da dama wanda yawancinsu irin girman hakurinsa da zama da Wardugun ne, da wanda in ya juye wani sa.in sai an nemo Mu.azam din,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button