BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 41 to 50

        Kadan ne

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________

             

*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          5️⃣1️⃣

Da kyar suka samu kunnayenta suka jiyo magangannunsu, domin du magangannun nan da take sun firgice basu san me take fada ba da yaren Tubanci take magana,

Shiru ta yi ta shiga bude idannuwanta a hankali numfashinta na sama da kasa da sauri sauri ta kankame hannayenta a jikin kirjinta tana mai bin mutanen wajen da kallo,

A hankali numfashinta ke daidaita rayuwar da ta yi a wannan kauye ke dawo mata daki daki,

Da sauri ta tsurawa y’ayan da suke malakinta ido, kafin ta kai dubanta wajen Gaishata dake rabe jikin garu tana duban mahaifiyar tata , domin da Jakadiya zata tafi kaiwa Sarki albishir bayan an yi kiran sallah ta umarceta da ta kamata su fito wajen yan uwanta, nan ta luluba mata katon bargon nan baki mai ciyayi ta fitar da ita dan kuwa har zuwa lokacin batai wanka ba, yo yaronma ba wani kulashi ta yi ba hankalinta na kan mahaifiyarta,

A hankali Anna ke girgiza kanta kafin ta furta” innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, 

Hannayenta ta dago tana bi da kallo wa.inda turkudi ya rike su da duhu aman ana ganni za.a gane fatarta ta fara nuna alamar gajiya irin ta zama datijuwa,

Tana tsakar haka sai ga ison Sarki na son shigowa,

Da sauri dogari ya tatare abin tatarewa ya karbi tabarma a hannun Mariama ya shinfida dan nesa da su kafin yake zuwa ya dage buhun dake a matsayin makarin shiga cikin gidan,

Shigowa Sarki ya yi bayan ya tsayar da yan rakiyarsa ya karasa cikin gidan yana mai salama ,

A hankali suke amsa masa, 

Dubansa ya kai wajen Gaishata dake rabe itama ta dago kanta ta dube shi ta sada kanta,

A hankali ya kai duban nasa wajen Minata dake rike da jariri ta lulube shi a cikin jikinta,

Ajiyar zuciya ya sauke ya duka yana gaisar da Anna,

Kanta kawai ta iya daga masa bata bashi amsa ba,

Zama ya yi ya ce” Anna ya jiki? Da yaren buzanci

Anna ta dago manyan idannuwanta ta sauke kansa, idannuwan kawai ta lumshe a zuwan amsawa,

Shiru ne ya biyo baya tana duban yaren, bakinta cike da magana, 

Can ta ce” ina Yake?

Mariama dake son ta mike daga irin zaman da ta yi ta matsa kusa da ita sosai ta ce” ANNA tun jiya ta fita bai dawo ba, Anna ki tashi ki wanke jikinki , ko sallah baki yi ba fa,

Anna jin maganat sallah ta samu ta ciciba inda Mariama ta kamata suka nufi dan zagayen dake bayi ,

Mariama ce ta kai mata ruwa a butar karfensu kafin take zuwa ta shiga kiciniyar dora ruwan zafi , inda Sarki ya karbi yaron ya dan matsa kusa da Gaishata yana rarashinta dan ta sake ,

Ta jima tana fama da ruwa , da omo blue din da ta bata wanda shi ne sabulun wankan, ta jima kafin ta sakawa fatarta shi, ta samu da kyar ta dan rage datin jikinta ta fito ta daura alwallah ta raba su ta shige daki ta tayar da sallah,

Ta jima tana salolinta dan kuwa baki daya sai da ta rama su, tana gama tahiyar karshe ta zauna zaman adu.a , nan ta fashe da kuka mai shiga zuciya tana jijiga gaba dayanta,

Hankali tashe suka shigo dakin gaba dayansu inda Mariama ta bude takar dakin dan haske ya kara shigowa,

Zuwa ta yi itama ba wani jira ta shige jikin Anna tana kuka ta ce” Haba Anna, haba Anna, menene ne? Me ya yi maki haka? A rayuwa mun ga tashin hankali kala daban daban , baki taba tankawa ba, aman jiya karar faduwarki kawai muka ji, shin me ya miki kika suma haka? Anna ki yi hakuri, ki dawo hayacinki domin ke ce nutsuwarmu????????,

Anna ta sasauta kukanta, tausayin y’ayan nata ya shiga zuciyarta,

Kanta a rufen nan ta vikin yaren tubanci ta ce” Amma ay yini zundu yigustiya, ayyinira unga ci? Dudonur? Tani ayyinira baranniri, abbanur dudonur ( fasara: wannan mutumen ya cuce ni, ina iyayena? Ina yar uwata? Ku taimaka ku kaini wajen mamata, da babana, da yayata.)

Mariama ta juyo wajen sarki hankali tashe ta ce” ka ji yaren da take, tun da ta farka wannan yaren ne take yi, mu bamu san me take cewa ba, Anna ki taimake mu, shin kin manta yarenmu ne?

A hankali Sarkin ya karasa shigowa ya duka dan nesa da ita ua tausasa murya sannan ya sada kai irin girmama siriki da yaren tubancin ya ce” Halasss de wonnuy? Ammanuma ngalla cuku? Tussu ko ka yogodi taha tani tudaqanur cussu qunu. (FASARA: ki kwontar da hankalin ki, ni ban fahimci komai a magangannun nan ba, waye ya cuce ki? Sannan ki taimaka ki fada min da buzanci ko zan gane da kyau.)

Ajiyar zuciya ta sauke kafin take gyara zamanta tana dubansu ta ce” Sunana *ALLATCHI* yar gidan *GUKUNNI* kannin sarki Mahamat na *Ngimi*, 

Sunnan mahaifiyata *Hatimi*, sunnan yayata *Herde* 

Shiru ta yi tana duban yanda yayanta da sirikinta ke binta da wani kallon mamaki, ta yi murmushi ta ce” mahaifiyata fara ce kar kar tamkar ka taba jikinta jini ya fito, inda mahaifina ya kasance baki sidik , bakinsa har shuni yake domin bakin batube ne na usil, yayata ta yi bakin mahaifina duda ta kasance mace bakin nata bai kai can can ba inda ni kuwa na yi hasken mahaifiyata,

Da zaku tuna yannayin *Agaishana* fatar jikinta, kamanun fuskarta na mahaifiyata ne ba zan taba manta kamanun mamana ba, sai fatar ta yo ta abanna duda nata nada haske sosai kan na mahaifina, aman wannan yannayin shiru, tsayuwa kan kafafuwanta du kuwa da irin halin da take ciki du tana satar yannayin Abanna,

Sarki ya tafka tagumi cike da mamakin dake neman zauta shi yana duban Anna, da saurin maganar da ba maganarsa ba tsabar firgita ya ce” kina nufin ke din Jinnin Honorable *GUKUNNI CE?* 

Anna ta lumshe idannuwanta ta ce” ni yarsa ce ta biyu, wanda a sanina daga haihuwata aka juyar da mahaifar mamana dan rashin lafiar da take fama da ita daga bakin da ta samu ciki har haihuwa, ban san bayanna ko Abana ya kara aure ba . Mu biyu kawai iyayenmu suka malaka a sanina,

Sarki ya ce” na san honorable *GUKUNNI*, alkalin garin Niamey banban alkalin dake yanke hukunci masu laifi? Shi dai kike nufi?

Anna ta dago dubanta ta gyada ba tare da ta amsa ba, wani irin nauyin baki ta bude ido da shi may be haka take da.

Da mamaki sarki ya ce” aman aman ya aka yi kika tsinci kanki a nan?

Anna ta rintse idannuwanta ta ce” watarana mun fito daga saloon ni da yayata, muna cikin tuki muka bige wani saurayi mai rawani 

A rikice muka tsaya nan yayata da ta fara aiki ta nunawa police din da ya zaburo wajen dan duba abinda ke faruwa da kuma kama mai laifi takardarta ta shaidar ita din likita ce mai zaman kanta ga kuma sunnan mahaifin mu dan haka aka hanzarta aka kama shi muka nufi likita a rikice sai kuka nake dan a rayuwa na kasance mai shegen tausayi da shigewa mutanen da ban sani ba du kuwa da irin gargadin mahaifiyata kan na ringa kiyayewa dan ba kowa ya zama na kirki mai zuciya sanyaya ba,

Mun kula da wannan mutun har ya samu lafia, iyayen mu sun ziyarce shi har asibiti bisa uzura masu da kuka da na yi ,

Bayan an salame shi ne ya duka yana kukan dan Allah mu taimake shi mu bashi aiki ya shigo garinnan bashi da kowa, daman zuwa ya yi neman kudi dan ya ciyar da iyayensa 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button