BAK’A CE Page 41 to 50

Haka na nace du kuwa da irin ma.aikatan gidanmu, na kara kai da kas cewar mu dauke shi, buzu ne sai ya koya min buzanci ,
Gannin hankalina ya ki kwonciya Abana ya dauke shi aiki a matsayin mai baiwa fulawowin gidan ruwa,
Mun shaku da wannan bawan Allah domin ya kasance mai barkwonci da bayar da dariya , ni kuwa du inda za.a bani dariya ina wajen, sannan ni ba kawaye ba, gashi a lokacin yayata tana zuwa aiki, ni kuwa makaranta dan wajen shekara goma ne tsakanina da ita,
Sunnan wannan Bawan Allah *Algabittt*, Algabiitt buzu , Saurayi kyakyawa, Algabiitt mai kyan dan maciji,
Ni dai abinda zan iya shaidawa wata rana na fito daga zance da wani dan ajinmu wanda ya nuna yana so na dan nima ina karantar fannin likita ne a lokacin, na dawo zan shige na ga Algabittt tsaye da wani abu a hannunsa jikinsa na rawa sannan da ya saka wani irin turare mai karfi da wani irin abu mai juyar da kwakwaluwa, daga nan na manta wacece ni, na kasance Jelar Algabiitttttt, !
Mahaifina, mahaifiata sunna raye? Ina suke? A ina ka san su?
Anna ta jefo masa tambayoyi tana mikewa tsaye, dan ta lashi takobin yau ko wace wace, sai fa ta danganta da danginta ko a kafa ne!
*Paris*,
Sunna shiga dakin ya ajiye mata akwatin nata kusan dirowa, tsayuwa ya yi yana dubanta ya ce” Agaishana, bara na samo mana abinda zamu ci , ki yi wanka ga bayi can, idan kin gama ki yi sallah.
Da kanta ta amsa masa inda ya fice ya barta nan tsaye,
A hankali ta taka gaban katon madubin dakin ta yi tsaye tana duban kanta,
A nitse ta yi adu.a ta cire kayanta ta bude akwatinta ta dauki hijab dogo mai ruwan milk color ta saka bayan ta daura tawul mai tsayi a kasa,
Bayin ta bude ta shiga , a gidan Ayya du ta san yanda ake anfani da su domin du irin na gidan Ayyar ne, dan haka cikin nutsuwa ta sala wankanta da ruwa masu dumi kafin take karawa da masu sanyi a kasan shower ta gama ta dauro alwallah ta mayar da kayanta ta fito,
Salaya ta dauka wace ta ganni ajiye nan ta shinfida,
Wata doguwar rigar ta canza ta kabarta sallah,
Bayan ta gama sallarta ta zauna ta yi adu.a mai tsayi ga iyayenta, iyayen rikonta, da mijinta da al.umar musulmi da kanta,
Agogon dakin ta daga kanta tana kallo, a kadan ya yi awa biyu da fita,
Ajiyar zuciya ta sauke, da ba dan can daman ta saba da zaman kadaici da kuma rayuwar daji ba da ta tsorata da zama a daki irin wannan ita daya,
Mikewa ta yi ta ninke salayar nata ta gyara hijab din jikinta bayan ta fesa turare mai sanyin kanshi wanda fitarsu da Wardugu da Alhinayeet wardugu ya kwaso mata su,
Ji ta yi ta kasa nutsuwa da jin shirunsa, dan haka ta mike a hankali ta bude kofar dakin nata da ba kara gare shi ba ta fito,
Abinda idonta ya ganni ne ya tayar mata da hankali,
Mu.azam ne zaune saman kujera, Khadija na gefensa da kaya irin sakakun nan na baci ta yane kanta da farin dan kwali tana bashi abinci cikin cokali tana fadin” sai fa ka kara haka kake son baci? Ka san ba zan yarda ba fa!
Tsaye ta yi ta harde hannayenta ta tsayar da dubanta kan su,
Khadija ce ta fara ganninta wanda ya saka ta mike da sauri cikin yannayi na jin kunya, ya salam shi ne ta furta a kasan zuciyarta, ita fa har ga Allah ta sha.afa da mai mata yake yanzu, irin yanda a da take tsare shi sai ya ci abinci yanzu hakan ma iya taba zuciyar matarsa,
Kanta ta dan sosa ta sakarwa Agaishat murmushi ta ajiye spoon din ta juya kanta na kallon kasa ta bar dakin dan wani irin shakar Agaishat din ta ji na lokaci guda da tsoron hada ido da ita………..
Shima kansa ya sada kasa ya kasa dago da kan,
A nitse ta karaso wajen da yake zaune ta duka ta dauki plat guda ta saka spoon din da ba.a yi anfani da shi ba ta debi abincin da ta san zai isheta ta ce” yunwa ya fito da ni, bara ka ga na yi na ci????,
Shatata ya yi yana kallonta har ta shige dakinta,
Agaishat na shiga ta ajiye abincin dan nesa da wajen da ta yi sallah ta cire hijabinta ta zauna ta tankwashe kafafuwanta ta dauko wayar da Wardugu ya saka mata a hannunta da kuma wayar da Ayya ta saya mata ta ajiye gefenta ta yi bismillah zata fara cin abincin
Tsai ta yi ta tsurawa abincin ido, a fili ta ce” *Me ya sa ban ji wani abu wai shi kishi kamar yanda alhinayett ta fada min wai idan kana son mutun kana masa makahin kishi?* , shi din kishin kansa waye shi? Ya ake jinsa? Ta ce min idan na ga mijina da wata zan ji hankalina ya tashi, wasu na kuka wasu kuwa na nuna bacin ransu karara,
Ko dai bani da zuciya ne a jiki na?
Arrrakham
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________
*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????
Na
*SAJIDA*
5️⃣2️⃣
Kafadunta ta daga tana mai baiwa kanta amsa” ai kawance ne, ba ga Alhinayett da Wardugu ba? Shi ya sa ban damu ba, kuma a hankali ai zan so shi, idan na so shin mai yiwuwa na kamun da kishin nasa?
Murmushi ta yi kafin take kuma wata bismillar ta shiga cin abincinta a nitse domin a gaskiya yunwa take ji , ita kuwa ko a daji ta saba du tashin hankalin da take ciki in dai ta samu sanwa bata raga mata , tana ci ta yi nak sai ta dora daga inda ta tsaya.
Tunda ta dauki abincin nan ya bi bayanta da kallo har ta kurewa ganninsa,
Hannayensa duka biyu ya dora a habarsa yana shafawa yana kai kawo, mamaki shi ne ya baibaye shi, ya mace zata tarar da mijinta zaune da wata a irin wannan lokacin a irin shigar Khadija duda ba wani shiga ne na kadaici ba, a irin kusancin zamansu, sannan tana ciyar da shi abinci ta juya ba tare da tace da shi ci kanka ba? Me hakan ke nufi? Ina , ina, wannan ba maganar dan ta fito a kauyen nan bata san so bane, su yan kauyen basa so ne? Su basu da zuciya ne? Su basa kishi ne? Bata nuna komai ba, shi bai ga wani yannayi na bacin rai a irin halin da ta tarar da shi da watanta ba, wani irin sanyi jikinsa ya yi harma ya katse masa hanzarinsa a kanta inda ya yi ta kai kawo ya kasa shiga dakinta dan kunyarta yake ji ya kuma kasa shiga ainahin dakinsa, har dare ya raba masa.
Su Walyn basu zo gida ba sai da ta yi kwana shida a gidansu, domin da likita ya salameta ta daure fuskar a fice gidansu da ita,
Mahaifiyarta ta bi umarninta suka je gidan su inda take samun kyakyawar kulawa daga iyayen nata tamkar su hadiye ta, dan du motsi za.a je ne a dauko kudi a banki sai dai Wardugu ya ji alert a wayarsa wace layin bankin ke ciki, yakan yi murmushi ya ci gaba da shagulgulan gabansa,
Wanka ta yi yau ta dandasa kwaliya da lifayar da ta sa mamanta ta sayo mata,
Sosai ta sha kwaliya ga kitso kananu ta yarfa a kanta ta hade karshe tana fitar da dadadan kanshi,
Yar jakar hannu ta dauka ta karbi kys din mamanta inda ta rakota bakin motar sunna bankwaba yau ta yi niyar komawa gidanta,
Zama ta yi wajen direba ta mikowa mamanta hannunta ba tare da ta yi magana ba,
Maman nata ta yatsina fuska ta mika mata carte din Wardugu ta banki ba dan ranta ya so ba ta juya ta tafi bayan ta kara jadada mata ta kiyaye hayewa Wardugu sannan in ta je ta san irin zaman da zata yi da shi!