BAK’A CE Page 41 to 50

Haka ta kamo hanyar gidan da ta bari tsawon kwana shida. (WALYN shagali)
Aiki mai tsanani ne ya rike shi yauma kamar jiya, an yankewa mutane hukucin zaman gidan yari wa.inda aka kama hannayensu dumu dumu cikin harkar shigo da miyagun kwaya da abubuwan maye wanda alkali mai girma mai shari.a *GUKUNNI* ya tsaya tsayin daka ba mai kudin ba talakan sai da ya binciko abinda ke kasan kasa kafin ya tafka gudumarsa mai nauyi ya zayano irin adadin lokacin da du mai laifi zai yi a gidan yari, ba damar daukaka kara domin babar kotu ta niger ce ta yanke hukunci,
Wannan lamari ya saka Wardugu kansa ya dau zafi domin sunna ta kai kawon canzawa masu laifin waje, ga tsare tsaren kara tsaro da aka baza a cikin gari, ga mutanen dake damunsa da magiyar ya fitar da y’ayansu su kuwa da sun san bashi da damar hakan, ga niyar zuwansa Paris a yau da dare dan a gobe karfe bakwai na safe za.a shiga aiki da amininsa dan uwansa, aikin dake tatare da hatsari, du wani masoyinsa yana cikin zulumin lamarin domin a daidai wannan lokacin Ayya ta san komai, ………
Bai gama saita abinda zai saita ba sai bayan magariba wanda a lokacin bai fi masa sauran awa hudu jirgi ya tashi da shi zuwa Paris ba.
Da gagawa ya fito ya shiga bayan motar da bodyguard ya bude masa, nan direba ya shiga ya ja shi( sabon tsarin da ya fitar , yakan yarda direba ya ja shi yanzu, wanda a da kuwa sam baya yarda), ya nufi gidan Ayya da shi,
Baiwar Allah tana zaune a tsakar gida , hasken fitulu sun garwaye gidan tana dan kada kafafuwanta da jarida a hannunta ta saka gilas na ganni a idannuwanta, shi kawai take jira
Wardugu na zuwa ta bayan kujerar ya rungume Ayya yana mai dora kansa saman kafadarta yana rintse idannuwansa,
A hankali ta dan tapng din hannunsa ta ce” Me ke damun ka?
Wardugu ya sauke ajiyar zuciya yana kokarin sakin Ayya ya dawo facing dinta ya ce” zan je na tafi Ayya,
Ayya ta girgiza kai gannin ya basar da tambayar da ta yi masa,
Hannunsa ta kamo ta rike ta ce” idan ka je ka zama jarumi , kar ka saki ambaton Allah ko me zai faru, ka kasance mai hakuri gaban abinda ya fi karfin ka, ka taimake ni ka kular min da yar amanata, ban so ka hana ni tafia ba, dan ban san ya zata tsinci kanta a ciki ba, yarinya ce, yarinya ce karama,
Wardugu ya lumshe idannuwansa kafin yake budewa a hankali yana duban Ayya, hannayenta duka ya hade ya dora a kirjinsa kafin yake sada kansa, a kadan ya kai minti biyar a wannan yannayin, wanda Ayya ta dora habarta saman yalwatacen sumar kansa utama ta lumshe idannuwan nata,
Shi ya fara motsawa a hankali yana duban mahaifiyar tasa, murmushi ya sakar mata mai tsari kafin yake cewa” adu.arki muke bara ya Anmi????????,
Allah ya kare ka, ya bashi lafia, ya kare min yarinta….Ayya ta fada tana shafa gefen fuskarsa
Murmushi ya saki yana amsawa saman lebensa kafin yake mikewa su jero da Ayya har wajen motar ya bude ya shiga,
Tukashi ake aman yana kara gannin girman soyayar dake tsakannin Ayya da yarinyar nan,
Murmushi ya yi ya muzkuta ya dauki wayarsa ya dannawa Khadija kira,
A lokacin Khadija na zaune saman salaya tana jan carbi, Agaishat na saman doguwar kujera mai zaman mutun guda ta lumshe idannuwanta da irin carbin nan wanda ake makalawa jikin yatsa tana danawa a hankali a hankali,
Mu.azam kuwa na baci wanda na allurar bacin da ake yawan yi masa ne dan ya samu cikaken hutu tunda aka kawo shi asibitin,
Ba wani magana tsakanin su aman suna mutunta juna….
A nitse ta daga wayar Wardugu, wanda a kwana biyun nan yakan kirata sau hudu du kuwa da irin yanda aiki ya sha kansa,
Tana dagawa kamar yanda ya saba , salama ya yi mata sai kuma ya ja bakinsa ya yi gum,
Murmushi ta yi , kai halayan abokin Mu.azam na bata mamaki, wannan da mace aka yi gaskiya za.a sha yanga,
Khadija ta mike a hankali ta fita dan kar ta yi wani dan motsinma da zai iya tayar da shi ta ce” Alhamdulilah general, jikinsa na karbar magungunnan yanda ya kamata kuma yana supporter, yanzu haka ya samu baci
Ajiyar zuciya Wardugu ya sauke kafin ya ce” Agaishat?
Khadija ta shafa gaban goshinta ta ce” gatannan zaune,
Ta ci abinci? Ya fada
Wayar ta ciro a kunnenta ta kuma duban sunnan, idannuwanta ta bude da kyau, tana mai jefawa kanta tambayar” wannan damuwa haka? Dan tana yar uwarsa ko dan tana matar abokinsa? Kamar wata baby kulun ya yi kira zai tambaya ta ci abinci? Idan bata ci ba zai kashe ne da an jima ya kuma kira har sai ta shaida masa da ta ci, kuma ita ba cewa yake ta bata wayar ba, koma ba wannan ba ai Ayya na kiran Agaishat din a waya, tana da waya, baya kiranta ya tambayeta sai dai wani?
Amsa ta bashi kan ta ci, kafin yake cewa” Merci (thanx) ya katse kiran
Wayar ta bi da kallo, daga inda take tsaye ta hango Agaishat na dan motsa kafa kennan dai idannuwanta biyu,
Ajiyar zuciya ta sauke ta samu waje nan ta zauna
*Kwana uku da suka shige kafin a kai Mu.azam asibiti*
A wannan kwanakin tsakannin Agaishat da Mu.azam an samu shakuwa, shakuwa irin ta zama waje guda, shakuwa irin ta sosai din nan domin Khadija ta daina shigowa gidan sai dai shi yakan fita a kai a kai ya leka wajenta dan makotan juna ne sai dai Agaishat ta hango shi ta windows
Ya nunawa Agaishat kulawa, sukan zauna su yi hira, harma su buga gem din da ya koya nata,
Ya koya mata cacakar waya ta iya shiga ta yi abinda take so,
Ya shaku da ita sosai , sai dai da magariba ta yi zai yi mata salama ne ya rakata dakinta ya fito, shima ya je dakinsa,
Bai taba hada shinfida da ita ba, kai ko kissing din hannunta bai taba ba bale ya zarce gona da iri, yana dai bata kulawar da ya saka Agaishat ta shaku da shi, har in bata ga wulginsa ba takan shiga yannayin damuwa har sai ta ganshi sun yi hira hankalinta ke kwonciya,
Ba zaka ga yanda halitar Agaishat ta kara kawatuwa ba sai ta saka wando dogo ko gajere , damame ko sakake irin shigar bacin nan da take, nan zaka ga mace a tsaye komai ya ji sai hamdala, Agaishat irin matan nan ne da sun san su waye su sai a slow, dan kuwa zasu iya anfani da halitar da Allah ya kawata su da shi dan firgita dubu su take dubu,
Zama waje daya, cin dadi, kwonciya baci tsala wanda sai sallah kawai da suka kasance ayyukanta na yanzu ya saka ta dauki yannayi na babar yarinya, daidai da murmushinta takan dan murmusa ne ta basar, koyon danna waya ya saka ta iya zama a karkace saman kujera, takan dan karkace kadan ta shiga danna wayarta tana gem na princess tana sakin dan murmushinta mai kawata fuskarta,
Mayukanta da Ayya ta siya mata dan kara gyara fatarta bata sanya da su, tana murzawa ne a duk lokacin da ta yi wanka ko alwallah, jikin Agaishat ya zama fresh ta kara haskawa sai santsi da fatarta ta kara,
Wannan fannin kam alhamdulilah ko ita tana gannin sauyi bale mai kallonta, hakan ya sa Khadija ke kara sarewa, bata iya zama na lokaci mai tsayi a tare da Agaishat, kamshin da take bazawama na turaran tubawa ya isa ya rikita maka tunani,
Tunda ta zo abu daya ya saka ta kuka, a ranar da ana gobe za.a shiga asibiti da mijinta, Mu.azam ya kasa zuwa ya fada mata ainahin abinda ke faruwa da shi, sai da macen da yake kira da aminiya ta yi masa jagora har cikin dakin barcinta, ta samu waje ta zauna ainahin wajen da Agaishat ke zama dan lumde jikinta da humura,