BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 41 to 50

Ta wani kada kai kafin ta shiga zayanno mata rashin lafiar mijinta, ta fada mata cutar cancer ce aman za.a shiga aiki da shi, ta karashe tana mai sakin gungurmen kukan da ya karasa dode kunnuwan Agaishat da ta rasa ina ta dosa, me hakan ke nufi, ta kai dubanta wajen Mu.azam da ya mike jiki a mace ya karasa wajen Khadija ya shiga rarashinta da nuna mata ba ta yi masa allawarin ba zata yi kuka ba? A wannan rana Agaishat ta yi masu kallon tsaf, a wannan rana ta ji idannuwanta na rufewa, hankalinta na tashi, a hankali ta kwonta saman bed din dakinta ta rintse ido, bata san fitar Khadija ba sai jin hannunsa ta yi saman fuskarta yana share mata hawayen da suka shiga zubo mata wa.inda batama san suna yi ba, a wannan lokacin ta buda idannuwanta da sukai mata nauyi ta sauke su saman fuskarsa, ta shiga rudani tsakannin abu hudu

Na farko, rashin lafiar mutumen da yake mijinta, wanda akai mata kira da cancer, ba.a fada mata aimahin menene cancern ba, ba.a yi mata bayani sala sala ba sai fada mata da aka yi cewar yana dauke da kansa wace za.a yi masa aiki nan da kwana uku, za.a shiga da shi asibiti a gobe gobe, wato mijinta na fama da babar cuta ne ko me?

Na biyu: irin yanda mijinta ne ke dauke da cutar, ita bata sani ba, sai da aminiyarsa ta sani, sannan aminiyarsa ce ta zo ta fada mata, du kuwa da irin kusancin dake tsakanin mata da miji?

Na uku” irin yanda aminiyar mijinta ke kauce mata, irin yanda ta hango halin shiga uku kan rashin lafiar amininta, irin yanda ya zabura ya nufeta ya dora kanta saman kirjinsa a gaban ita da take ainahin matarsa ta sunna wada ba zata nuna ranar da ya yi mata haka ba, ya rarashi aminiyarsa harma ya yi mata rakiya

Na hudu: sai a lokacin komai ya shiga dawi mata daki daki, ta kasance a dukan lamarin mu.azam tana zuwa ta biyu ne, wato Khadija ce fa fari! 

Da wannan kallon cikin idon da ta yi masa na tsayin lokaci inda ya dora hannunsa na dama yana gyara mata dogon gashinta da ya bazu kan bed dinta kafin a hankali ya ce” ki yafe mini, 

A haka ya ja mata bargo ya lulubeta ya kashe mata fitilar dakin ya fita da nufin ya barta ta yi baci ko me?

A haka ta hangi ficewarsa wajen ainahin aminiyarsa , Aminiyarsa, aminiyarsa!

Abinda ya faru da Agaishat da Mu.azam da khadija kennan kafin a kawo Mu.azam asibiti bisa kulawar likitoci sa Agaishat da Khadija aka shiga saka masa magungunna ta hanyar karin ruwa da nanauyan magugunnan baci dan ya samu isashen hutu…..

       Wannan kennan

Wardugu na karasawa gidansa ya fita ya nufi sashensa,

Yana budewa ya shiga da sabon cerrure din da ya canza ,

Yana shiga ya ga sabuwar mai aikin da ya dauka, wace a da babu namiji a yan aikin bangarensa bisa umarnin walyn, aman a yanzu ya dauka ta gyara falon ta saka turaren ruwa mai kanshi ta ajiye abinci, 

Ya san tana can bangaren da ya saka aka kaita wanda ke nesa da wajensa sosai dan haka ya zarce dakinsa

Sauri sauri ya yi wanka ya dauki jakarsa irin ta sojoji ya saka kananun kayansa na bukata da maclean da bros, da complet daya , 

Kananun kaya ya saka a jikinsa bakin dogon wando da bakar riga kafin yake dora costume (veste) saman rigar ya caje gashinsa ya gyara sosai ya fesa turare mai kanshi,

Jakar ya dauka da passport dinsa sai cart dinsa ta can wace a bankin can ya yita,

Fitowa ya yi yana duba dakin bai bar komai a jone ba? 

Nan ya ga hajia Walyn tsaye, ta sha kwaliya mai kyau da birgewa tana masa murmushi ,

Kallo daya ya yi mata kafin ya kawar da fuskarsa ya juya ,

Yannayin hade fuskar da ya yi ya saka bata iya tankasa ba, tsoro ya hanata tambayarsa inda zai je duda ta sani ne fita ne zai yi ya dawo dan haka sai ta nemi waje ta mike tana jiran dawowarsa ta lalabe shi ya manta fushin da yake su shirya (to ka ji)!

Bai dauki mota ba, bai kuma bi ta kan kowa ba ya fice a kafarsa yana mai duba agogo

Taxi ya tsayar ya shiga ya fada masa aeroport,

      

                 Timiya

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________

             

*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          5️⃣3️⃣

Timiya

A wannan ranar da kyar aka samu Anna ta koma ta zauna , shima sai da y’ayata suka rikice da koke koken dan girman Allah ta zauna a zana sunnan jaririn nan da aka samu sai su tafi, dan Gaishata ta kara kai da kasa yan uwanta da mahaifiyarta ba zasu tafi su duka su barta ba, kar a je su ki dawowa,

Gannin haka shima sarkin hankalinsa ya tashi dan haka harda shi a yan magiyar ta zauna a yi suna sai ya yi masu rakiya wajen wanda yake da alaka da gidan , wato sarkin agadez, shima rakia ya yi masa wani lokaci da suka je banban birnin, suna ganewa junna, 

Haka dai Anna ta yarda ba dan hankalinta ya kwonta ba, sai dan tinawa da ta yi y’ayanta, idan ta tafi wajen wa zasu rabu su ji sanyi? Dama gashi ya fara tado maganar mutanen da suka kawo kudin aurensu sun waiwayo zasu zo a daura aure,

Wani murmushi ta yi mai ma.anoni da dama kafin take fita ta juye zuwan zafin dake tafasa Mariama ta kama suka kai bayi ta fito fuska a dan hade ta zanawa sirikin nata du abin bukata na wankan jego kan a yi gagawa a kawo kafin ruwan ya huce, (abinda da bata iya ko tsayuwa gata ga shi, Annar yanzu ba ruwanta ba wani shaka ko tsoro), 

Da sauri ya amsa ya fita a gidan, inda Anna ta tube jaririn sai hada rai take na yannayin tsaftar gidan , du hankalinta da nutsuwarta ba a waje daya suke ba, sai ma da aka tashi neman turare abinka da batuba, kaf gidan Mariama ce kawai mai turare , itama irin na duran nan ne mai karfin tsiya, dan haka dole su Mariaman suka karbi makulin dakin Gaishata suka nufi gidan sarki dan ita tana da dan turaran wuta da na ruwa dan idan sarki ya je cikin birni yana bada kudi wajen mai dakin sarkin agadez q harhada masu tsumamun turaruka da sauran su,….

              Wannan kennan

                  *Paris*

Jirgi na sauke shi ya kunna abin localisat@ din wayarsa ya shiga carte cikin iphone dinsa ya danna localisation din wayar Mu.azam, domin a kunne take kuma ya tabata nasama ba a kashe ba,

Taxi na ajiye shi kofar asibitin ya je wajen shiga ya nuna takardar shaidar waye shi, ya bada cikenken kwatancen wajen wanda ya zo da ranar da aka kawo shi da komai kafin ake barinsa shiga dan an rigaya an hana shiga, suma da suke tare da shi dan Khadija na ma.aikaciyar wajen ita da Mu.azam din,

Yana shiga ya fitar da wayar ya shiga bin kwatancen da ta dora masa saman screen dinsa har ya iso dakin da yake kwonce,

Da yake akoy katon madubin da ana tsayawa a ga marar lafia ta nan, sai Wardugu ya tsaya ya harde hannayensa ya zuba masu ido,

Khadija na nanade saman salaya carbinta ya fadi da alama tana ja baci ya kwasheta,

Agaishat na zaunen dai saman kujera kuma lokaci zuwa lokaci takan dan motsa kafarta idannuwanta a rufe har yanzu kamar mai baci, da dogon hijabinta mai ruwan jini,

Sai Mu.azam dake sheme saman gadon mararsa lafia, an aske kansa kwalkwal har kyali yake , wanda shi ya saka aka aske masa da kansa tun kafin a shiga aikinma, yana ajiye numfashi a hankali,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button