BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 41 to 50

Idannuwansa ya rintse ya karasa wajen doguwar kujerar silbar da ya ganni a wajen ya zauna ya daga kansa sama yana jan carbin hannunsa ya tsurawa fitilar dakin ido

Yanda Wardugu ya ga rana haka ya ga dare, wajen karfe biyu ya ji motsi a dakin nasu wanda ya kyautata zaton alwalla aka dauro dan an jima ana dan motsi kafin ya ji shiru, a hankali ya leka nan ya ga Agaishat ce ta kai sujada kanta kasa tana adu.a, kawar da kansa ya yi da sauri ya koma ya zauna ya ci gaba da jan carbinsa, har karfe biyar ta yi

Ba kiran sallah zasu ji ba dan haka da agogo suke aiki , da lokaci ya yi zasu mike su yi sallah ne,

Zuwa ya yi ya samu ya dauro alwallah ya dawo,

Tapis ya dauka cikin jakarsa ya kebance kansa dan likitoci sun fara dan kai kawo ya tayar da sallarsa,

Ya jima yana rokom Allah ya sa a yi aikin nan lafia, yana gamawa ya mike dan shida ta gota ya dauki jakarsa ya dan kwonkwasa dakin

Agaishat dake kusa da kofar ta mike ta bude ,

Gabanta ne ta ji ya wani tsintsinke ya fadi a lokaci guda,

Kanta ta daga kafin take iya kallon fuskarsa, wanda shima ya dan duko da kansa ya sauke idannuwansa kan fuskarta,

Ba zaka iya karantar yannayin fa yake ciki ba, fuskarsa ba yabo ba falasa,

Shigowa ya yi ya mayar da kofar ya rufe,

Fuskarta da idannuwanta sun kumbura, hakan na nuni da ta yi kuka,

Kawar da dubansa ya yi daga kanta ya mayar kan Khadiha da ta mike itama tana dubansa,

Fuskarta itama ta bumbura ta yi jajajir,

Bai amsa gaisuwar da suke masa ba sai zarxewa da ya yi wajen Mu.azam,

Kujerar dake kusa da gadonsa ya ja a hankali ya zauna yana kallonsa, karfe bakwai saura yan mintuna Mu.azam ya farka,

Farkawarma ba can bace, ya fan buda idannuwansa da sukai masa wani irin nauyi ne,

A hankali ya ga Wardugu dake zaune ya rike hannunsa na dama,

Allah ya bashi ikon yin murmushi yana duban Wardugu, 

Magana yake a hankai wanda Wardugu ya kunnayensa aman bai ji komai ba dan haka ya nuna masa da ya yi shiru,

Da idannuwansa ya nuna ya yi shirun inda ya lumshe idannuwan sai ga hawaye sun fito daga cikin idannuwan nasa,

Docter Ce ta shigo da farar riga irin ta likitoci tare da nurse da uku da gadon tura marar lafia

Wani irin mikewa Khadija ta yi ta zuba masu ido inda docter ta girgiza mata kai, haka ne daman idan kana son gannin rikicewa sai idan ciwo ya taba likita, yakan fice a hayacinsa ya zama wani kala, yakan rude komai kankantar ciwo bale mai tsanani, 

Hakan ce ta faru da khadija, domin a lokaci daya ta rikice ana nuna mata kar ta yi gabansa aman ina bata san lokacin da ta dora hannayenta duka biyu saman kanta ta fashe da kuka , da sauri Wardugu ya juyo ya cire gilas din idannuwansa domin har ya mana dan baya so a san halin da yake ciki,, 

Da sauri Docter ta kama hannunta suka fice inda wasu likitocin maza biyu suka shiga kokarin daukansa suka dora saman dayan bed din

A hankali Wardugu ya saka hannunsa cikin sumar kansa ya shiga yamutsawa inda gaba daya jijiyoyin jikinsa suka mike tsabar yana cikin tashin hankali

Agaishat dake tsaye sai zarar ido take gannin yanda Khadija ta fashe da kuka aka fita da ita, da yanda aka dauki Mu.azam ranga ranga aka dora saman wani gado, du fuskokin likitocin a hade irin sun ci kalar serius din nan sai ta rikice, 

Tana ta zaro ido tana kallon yanda suka saka masa oxygen suka gyarashi da kyau saman gadon , 

Sai bayan sun gama gyara shi wani likita ya zo da takarda a hannunsa cikin file , da yaren faransanci ya ce” Chef, (sire), docter Khadija tace Nan zan samu Wardugu?

Wardugu dake tsaye shima yana kallon yanda aka yiwa amininsa, nan zuciyarsa ta kara tsorata da girman ikon ubangiji, kaga mutun yanzu yanzu ka zama tamkar gawa ko gawar,

Da kai ya amsa masa cewa shi ne, dan haka likitan ya mika masa wata takarda kafin yake kara masa bayani kamar haka” Docter Mu.azam ya bar maganar cewa idan za.a shiga aikinsa a baka wannan takarda ka saka hannu, takardar na nufin idan Har Allah bai yi ya fito kalau ba kai za.a ba gawarsa ba likita zata birne shi ba,

Wani irin sarawa kan Wardugu ya yi, Wardugu dai soja ne, sojan ma baba, wanda ya shiga gwagwarmaya da manyan yan ta.ada, wanda ya kwana cikin rami, wanda ya shiga hatsari kala daban daban na rayuwar yau da kulun, yau gashi gaban ikon mai duka, yana ji yana gani ya karbi biro ya saka hannun idan amininsa ya mutu a dakin tiyata a bashi gawarsa,

Yana saka hannun suka karba suka juya da Mu.azam dake sheme tamkar gawa, 

A hankali wardugu ya kai wajen garu ya silale dan baki daya kafafuwansa rawa suke masa,

Agaishat da ta bi su da kallo sun fice mata da miji ta juyo da sauri wajen Wardugu ta karasa ta duka daidai inda yake yana kallon waje guda , murya a rikice ta ce” Ina zasu kai shi? Ina zasu kai min shi? Ina zasu kai min mijina? Ya mutu ne? Me ya sa suka tafi da shi? Wayyo Allahna, Wayo Allahna , 

Ta fada tana karasa zubewa kasan ta fashe da wani irin kukan da ya jima yana cin zuciyarta,

Wardugu dake kallonta ya lumshe idannuwansa kafin yake budewa,

Hannunsa dake rawa ya mika ya janyo hannunta kusa da shi sosai,

Murya can kasan makoshi ya ce” ba mutuwa ya yi ba Agaishat, aikin ne aka shiga da shi, ki daina kukan nan na tuba ki rufa min asiri ki yi shiru????????, 

Maimakun ta yi shirun sai kara kukanta da ta yi tana ta rike hannunsa tana kiran ya kaita wajensa, ya kaita ta ganshi, kar ya mutu ya barta, tana son sa! 

Ido kawai ya lumshe ya yi shiru ya damke hannun nata, bai kuma yi mata magana ba sai sauraron sambatunta da yake tamkar ta zauce ,

Wasa wasa awa daya, awa biyu awa uku, awa hudu, awa biyar, awa shida ba.a fitar da Mu.azam ba, daga dakin sun canza waje ya fi a kirga inda karshe suka dangana dan nesa da dakin tiyatar kusa da Khadija dake zaune tana wani irin numfashi tamkar mai athsma, da kyar aka barsu suka tsaya nan din sai da aka kusan kwasar rashin mutunci da Wardugu kafin masu tsaron asibitin su bar shi,

Agaishat zaune take jikinta hade da garu itama tana rawar sanyi, zazabi ne jikinta inda Wardugu ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai kawo yake hankalinsa ba a kololuwar tashe.

Suna haka baban likitan asibitin ya fara fitowa, nasara ne mai sunna,Roger , shi ya jagoranci aikin inda likitoci kamarsa biyar suka taya shi,

Khadija ce ta fara mikewa ta nufe shi jikinta na rawa baki daya,

Daidai nan wasu uku suka fito suma suka tsaya kusan docter Roger,

Tambaya ya yi cewar” ina Wardugu?

Wardugu da ya tsaya yana hangensu ya ji gabansa ya fadi, a hankali ya shiga takowa inda wata zazafar zufa ke karyo masa, du takunsa guda daidai da mutuwar tunaninsa yake har ya karaso kusa da likitocin,

Likitan ya dago kansa cikin wani yannayi ya ce”””…….

                           ????

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________

             

*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          5️⃣4️⃣

Likitan ya dago kansa cikin wani yannayi ya dubi Wardugu kafin ya dubi Khadija, ya ce” mun fito aiki, za.a fitar da shi a saka shi dakin observation na sati biyu, komai nasa zai dawo hannunmu na tsayin wannan lokacin, cinsa , tsaftarsa, komansa, tsakaninku da shi sai dai ku ringa hango shi ta jikin madubin dake makale da dakin, ni kadai zan iya shiga in daidaita komai in fito, za.a baku takardar magani da kuma irin abincin da za.a ringa saka masa ta mesa ta hancinsa, fatan ka fahimta idan baka gane wani abin ba sai ka tambaye ni ko ka tambayi matar tasa *Docter Khadija* ai ta san komai itama zata kara maku haske,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button