BAK’A CE Page 61 to 70

Amarya da ango na zama suka fara juyawa dan kai yan matan wajen zamansu,
Dan tsai ta yi a lokacin da ta fahimci yanda wajen zaman yake, haka ta juya jiki sabule zata je wajen zaman yan matan ta zauna ita daya,
Bai fi taku biyu da ta yi ba ta ji hannunta cikin nasa, ba zata iya rasa sannin hannunsa bane domin ta gama karantar yanda hannunta ke zama daram cikin nasa,, ta yannayin da jikinta ke nuna mata du idan ya yi irin wannan lamari ya saka ko dubansa bata yi ba ta karantawa zuciyarya shi din ne, a hankali ya kara kusanta kusancinsa da ita ya shiga bin takunta ba tare da ya kaleta ko ya ce da ita ufan ba har suka sauka suka nufi wajen zama,
Suna karasawa ya tsaya wajen kujerar da kanwar Alhinayett ke zaune, wace take facing dinsa ,
Kallonta kawai ya yi da idannuwansa ta mike a wajen ta koma wata inda ya kali yannayin kujerar kafin da hannunsa na hagu ya yi mata nuni da ta zauna,
Cikin nutsuwa ta dago idannuwanta da sukai mata nauyi , nan ta ga ikon Allah ashe du yawancin hankalin mutanen wajen na kansu, tun daga kan sojojin har yan matan wajen, uwa uba Farid da ta gani zaune shima ya yi zuru yana kallonsu,
Da sauri ta zauna tana dan zaro idannuwanta inda ya dan yi tsai , kafin ya rage tsayinsa wajen kunnenta ya ce” Na haramta maki motsawa a nan har sai an tashi!
Du mai kallon su, zai yi tunanin maganar soyaya ake a wajen nan, zai yi tunanin an gama mutuwa a son juna ne, bai damu da kallon da ake binsa da shi ba, hasalima sai da ya dan kara tsayawa ya mike da kyau ya bi kowa da kallo hakan ya sa mutane suke kawar da dubansu daga kansa kafin yake nufar kujerarsa,
Walyn, Walyn, walyn, wani kakausan kallo take binsa da shi har ya gama du abinda yake ya dawo ya zauna a wajensa wato kusa da ita,
Bata dubi tarin mutanen wajen ba, bata yi la.akari da wajen ba bale ta ari kissa irin tamu ta mata ba, yana zama ta shiga magana kamar haka” Wardugu, wannan wani irin mulakanci ne? Meye hadinka da kaskantaciyar yarinyar da muka dauko daga kasurgumin jeji dan cireta daga kangin talauci? Meye daraja a bakar mace har da zaka dauki hannunka mai daraja ka rike nata? Wardugu menene tsakaninka da tsohuwar bazawarar da amininka ya aura ya saki dan ba zai iya zama da ita ba? Wardugu wacece ita a wajenka? Wardugu!
Ta karashe tana mai dan daga murya da wawatsa hannayenta wanda duka na kusa da su na jin abubuwan da take fada da irin dibar albarkar da take tafkawa inda na nesa da su ke hangen Walyn na yuwa Wardugu fada , domin kuwa geste dinta kamar uwa na yiwa yaronta fada ce, irin zazafan fadan nan ma kuwa,
Dubansa ya dago ya dora saman kanta, hauka? Shirme? Aa Raini! Kai tsaye, ido cikin ido, ba wani gargadar murya, ba wani kawar da fuska, ko tausasa harshe Wardugu ya ce” kina son ki san ko wacece ita? Ita din *ORRONUR* dina ce…….
Dankari,
Kaka kara kaka
Ku samo ma.anar ORRonur sai na baku wani page????
Walyn? Walyn! Wardugu!
Agaishat
More comment bilahi????????????????????
Share this
[ad_2]