BAKAR INUWA 21
Typing📲
Episode 21
………..Cikin girmamawa baba Adamu driver ya buɗema Raudha jibgegiyar motar yana faɗin, “Barka da safiya ranki ya daɗe”.
Sosai kunya ta kama Raudha, dan baba Adamu ba yaro bane ba, cikin ɗan murmushi tace, “Baba ina kwana”.
Amsawa yake cike da girmamawa da jin ƙaunarta, dan duk yanda kake kanaso a girmamaka a mutuntaka. Yaran gidan su Ramadhan kuwa ƴammatan nan yanda suke masa har ƙwalla yakeyi wataran. Sai dai idan Pa ya gani ko Bappi ko Anne su tsawata musu. Dan Ramadhan shima yana bashi girma sosai. Samun kansa yay da taya Ramadhan murnar samun mace tagari, tare da binsu da addu’ar fatan alkairi a zuciya.
Tunda motar ta fita a gidan Raudha na kallon titi ne kawai da shaƙar ƙamshin motar mai neman sakata barci. Ga wani sanyi dake ratsa jiki a hankali. Da farko a tsorace take, amma ganin babu kowa a motar sai zuciyarta ta samu nutsuwa.
Tafiyar da bata gaza mintuna sha biyu ba suka iso, abinka da lafiyayyar mota akan nagartaccen titi. Wani irin tsargawa cikin Raudha yayi ganinsu a airport, inda bata taɓa zuwa ba sai dai ta gani a tv. Zuciyarta ta shiga tsinkewa lokacin da take fitowa idanunta sukai arba da gayyar jama’ar Taura Family ƙwansu da kwarkwatarsu. Jitai ƙafafunta na hahharɗewa. Cikin sauri ta shiga ambaton addu’ar da duk tazo bakinta a zuciya. Anne da fuskarta ke faɗaɗe da murmushi ta riƙo hannunta tana faɗin, “Masha ALLAH wannan amarya kam da gaske zata iya ture gwamnatina”.
Raudha dake jin kamar zata nutse ta rissina tana gaida Anne. Sake riƙota Anne tayi ranta fal da jin ƙaunar yarinyar, harga ALLAH shigar mutunci da Raudha tayi na hijjab ya matuƙar burgeta. Bappi ne na biyu data gaida kasancewar shine kusa da Anne, shima kuma yanata zuba mata murmushi tare da sake tambayarta ƙarfin jiki tace Alhmdllhi.
Sauran ƙannen Ramadhan duk sun sake yarda Raudha ƙyaƙyƙyawa ce ƙwarai da gaske, wasun su ta shiga ransu, wasu ko sunajin ƙinta a rai badan ta musu komai ba. Bayan ta gaida Pa ta gaida su Gimbiya Su’adah badan tasan matsayin kowanne ga Ramadhan ɗin ba. Kawai dai yanda ta gansu manya matsayin iyaye yasa ta risina kamar yanda ta gaida Pa suma ta gaishesu. Su Hajiya Mufida sun amsa mata da fara’a musamman ma hajiya Shuwa da dama haka take da sakewa. Gimbiya Su’adah kam bana tunanin tama amsa mata. Sai wani kallon ciki da bai take mata fuska a yamutse.
Oho Raudha bama tasan tanai ba dan taƙi yarda ta kalli kowa. Sai ma juyawa datai ta gaida su Zainab ƙannen Ramadhan ɗin. A take Rumaisa da Fadila da Basma suka riƙota sun murmushi, zasu iya zama sa’anninta a shekaru, sai dai jin daɗi da hutu yasa sun fita girman jiki.
Sai yabata suke da faɗin yayansu yayi sa’ar ƙyaƙyƙyawar mace, ita dai ta kasa cewa komai sai ɗan murmushi, dan duk a takure take. Bata sake tsurewa ba sai da zasu shiga jirgi da batai tunanin nan ɗin zasu shiga ba, dan sanda suka fara taka steps ɗin sai da Bilkisu ta riƙota saboda tuntuɓe da taci zata faɗi. Tambayar zuciyarta ta dingayi ina zasuje ne haka? A ɗayan gefen kuma tsoro ne fal da fargaba.
Can aka kaita sashen vip ba inda sauran suka zauna ba. Duk da kuwa duk cikin jirgin Taura family’s ɗinne da ma’aikatan gidansu. A taƙaice ma jirgin nasune. Duk da ba gama tantance ƙamshin turarensa tai ba lokacin da suka iso hanunta cikin na Basma sai da gabanta ya faɗi saboda wani shegen ƙamshin turaren daya daki ƙofofin hancinta. Ta sake waresu da ƙyau tana zuƙa da yin tazbihi ga UBANGIJIN daya azurta ƙwaƙwalwa da gangar jiki akan son ƙamshi da banbance wari.
Sallamar da Basma tayi ne ya sakashi ɗago idanunsa da kallo guda zakaima cikinsu kasan yana matuƙar buƙatar son hutu, yay mata duba ɗaya ya janye ya maida ga magazine ɗin da yake karantawa.
“Yayanmu dama Anne ce ta ce na kawo aunty Raudha ta zauna anan acan zata takura”.
Cak ya tsaya da karatun, sai dai bai janye magazine ɗin daga fuskarsa ba. Tsahon mintuna biyu kafin yayma Basma nuni da kujerar dake kallon wadda yake kai batare da yace komai ba. Bai kuma kallesun ba har yanzu. Duk wannan abu Raudha na laɓe a bayan Basma ne. Sai da Basma ta juyo ta kamo hanunta tana murmushi.
“Bismillah auntynmu ki zauna anan, dan ALLAH ki saka yaya yay surutu, dan tunda aka fara hargitsin campaign ɗin nan ya sake zama shiru-shiru”.
Kasancewar a cikin kunne tai mata maganar yasa Raudha saurin duban gabansu, sai dai kafin ta iya furta wani abu Basma ta kamata ta zaunar a kujerar har gwiwarta na ɗan gogar ƙafarsa daya harɗe ɗaya saman ɗaya. Kamar walƙiya kuma Basma ta ɓace a wajen.
Zan iya ce muku a wannan lokacin zuciyar Raudah ce kawai zata iya sanar muku halin da take ciki, dan faɗa da bakima ɓata lokaci ne. Ta kasa dubansa balle ƙwaƙwaran motsi, abinda ta iya ƙarfin halin yi kawai shine faɗin, “Ina kwana”.
Bata damu da amsawarsa ko akasin haka ba, dan koya amsa bata tunanin ƙwaƙwalwar kanta zata iya banbance da wane yare ya amsa ɗin. Magana da na’ura ta farayi na a ɗaura belt ya sashi janye magazine ɗin daga fuskarsa a hankali. Akan Raudha idanunsa suka sauka. Harya janye idanunsa daga kallo guda dayay mata yana ƙoƙarin ɗaura belt ɗin sai kuma ya sake dubanta. Harga ALLAH yana matuƙar son blue color, shiyyasa duk inda yaga kalar da wahala bai nutsu a duba ba. Balle wannan daya haɗu da farar fata da cute face ɗin Raudhan. Motsin da zuciyarsa tayi a cikin ƙirji ya sashi janye idanun nasa gaba ɗaya daga gareta, harya sake ɗukar magazine ɗin zai buɗe sai kuma ya fasa ganin bata motsaba balle tai yunƙurin saka belt ɗin, ga jirgi ya fara ƙugi alamar zai tashi.
Cikin yatsine fuska da sake ɗaureta ya matso da jikinsa. ganin ya matso da hanunsa da gargasa suka ɗan bayyana a white skin nashi yasata saurin dubansa, sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska ya sata saurin rumtse idanun ta matse jikinta.
Lip ɗinsa ya taune na ƙasa da balla mata harara yana girgiza kai, sai kuma ya taɓe baki lokacin daya zugo belt ɗin yabi ta cinyoyinta da shi batare daya taɓata ba ya sakashi a ɗayan gefen. Wani shegen numfashi dake fita da sassarfa ta saki ganin ya koma ya gyara zamansa kamar yanda yake a da. Sai taji kamar ta saki kuka kawai ta huta ita kam.
Bai sake bi takanta ba har jirgin ya ɗaga duk da yaga yanda ta dafe kai lokacin da jirgin ke shillawa cikin gajimare. Karatunsa ya cigaba dayi duk da ƙamshin khumra ɗinta ta mugun addabar hancinsa, amm ya fuske kasancewar sa gwanin jin kai.
Gaba ɗaya Raudha a birkice take bata samu nutsuwa ba har sai da jirgin ya sauka, dan kwata-kwata tafiyar mintuna ashin da uku ce ta kawosu jihar Bino. Ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya lokacin daya miƙe yana ajiye magazine ɗin, komi baice mataba ya kwashi phones nasa guda uku da wani ɗan leda. Sai da ya ɗaga labulen wajen zai fita sannan ta tsinkayi tattausar muryarsa mai faɗi da ɗan buɗewa cikin kunnenta.
“Zaki cigaba da zama ne anan?”.
Da farko bata fahimci da ita yake ba, sai da ta waiga taga dai ita kaɗaice a wajen sai ta miƙe tan ɗaukar bag ɗinta ta sakala a kafaɗa a sanyaye. Sai a yanzu ta samu damar iya kallonsa. Sanye yake cikin wani skay blue yadi mai shegen taushi, dan yanda ya ɗauka guga da ɗaukar idon mai kallo kawai ya isa kasan an sayesa da kuɗaɗe masu nauyi. Ga telan daya ɗinkasa ya fidda komai yanda ya kamta dai-dai da jikinsa kuma. Rigar iyakarta cinyarsa, hakama hanunta gajere ne iya gwiwar hannu, sai hula daya murza black da takalmansa suma black half covers. Sai agogonsa omega, fuskrsa tayi fayau saboda ɗan ramar da yayi da kuma gyaran fuska da Bappi ya takura masa yay jiya da yamma.
Da sauri taja da baya ganin ya juyo a bazata lokacin da suke gab da fitowa, ledar hanunsa na facemask guda biyu ya ɓare ɗaya ya miƙa mata. Ɗan ɗagowa tai, sai dai tai azamar janyewa kasancewar idanunta da suka faɗa cikin nasa a bazata. Karon farko da taji wani abu ya tsarga mata daga ƙwaƙwalwa zuwa yatsan ƙafa mai kama da tainkewar jini, taji tamkar ta saki fitsari lokacin da taji hanunsa a gefen fuskarta, tanaso ta ɗago ta kasa, sai rumtse idanu da tai da ƙarfi jin ya tura yatsunsa biyu ta cikin hijjab ɗin ya saƙala igiyar a kunnenta, kafin ta farfaɗo ya ja facemask ɗin zuwa ɗayan gefen haggunta ya saƙalo nan ma.
(Ya rabbi) ta iya ambata a ranta. Bata iya motsawaba duk da rawar da jikinta ke mata sai da taji alamar ya juya sannan ta iya binsa da kallo.
Yanada tsayi gwargwado, sannan ga jikinsa a murje kasancewar yana cin ƙarfe ga kuma jin daɗin rayuwa. Jin kansa da ƙasaita da mutane d yawa ke fassarawa da girman kai suna ƙara masa wani ƙyau da girma a idon mutanen. Musamman masu son kawo masa wargi duk da ƙananun shekarunsa kuwa. Duk da kasancewarsa ba miskiliba bashi da yawan fara’a. Bakuma dan baya yin dariyar bane, a’a kawai sai ya zaɓa wanda yaso yake iya ganin haƙoransa.
Tunda suka fara sakkowa. steps ɗin jirgin hasken camaras keta walainiya a kansu, dan su Bappi duk sun sauka har suna ƙoƙarin shiga motocin dake jere da aka kawo dansu. Sake ruɗewa Raudha tayi duk da ya zartata da step ɗaya, dan yana gaba ne tana biye da shi.
Ƴan jarida nason ji daga garesa amma securitys sun musu zobe. ganin yanda wani keta son kutso kai yasa Ramadhan ɗan dakatawa ya ɗagama securitys ɗin hannu. Dole suka ɗan janye hannayensu suka bama ƴan jaridar dama suna antaya musu harara.
“Ranka ya daɗe gaka a jiharka ta Bino domin zuwa tushenka ka jefaa ƙuri’a. Ko zamu iya sanin ya kakeji a wannan ranar kuwa?”.
Wani ɗan murmushi ya saki dakai hannu ya shafi gashin daya zagaye bakinsa, “Inajina tamkar kai, kamar kuma kowa, domin banda banbanci da kowa”.
“Amma ranka ya daɗe duk wani mai irin matsayin da kake kai na ɗan takara a yanzun musan hankalinsa nakan zaiyi nasa ko bazaiyiba. Miyasa kai kakejin kanka kamar kowa irina?”.
“Saboda nayi imanin ALLAH shine ke bada mulki ga wanda yaso, a kuma lokacin da yaso. Idan ni ba alkairi bane ga ƙasar NAYA ALLAH ya hanani damar samun wannan kujerar, ALLAH ya bamu wanda ya fini alkiri”.
A take wajen ya ɗauki tafi, fuskokin mutane cike da fara’a. Yayinda wasu suka shiga masa kirari da suna DOGARO GA ALLAH JARI.
Harya ɗaga ƙafa zai wuce wani ɗan jarida yace, “To amma ranka ya daɗe baka ganin mutane zasuga kamar basu da galihu musamman dasu suka kasance a rana tun daga fara campaign amma ko sau ɗaya ba’a taɓa ganin budurwarka ba a wajen, gashi kuma yau ranar zaɓe ma babu alamar zata fito jefa maka ƙuri’a?”.
Ɗan tsura masa ido Ramadhan yayi na sakanni uku, sai kuma ya janye yana sakin murmushi. Shi lauya ne, yanada sauƙin karanta da fassara kalman mutane, dan haka ya ɗan dubi Raudha da kanta ke ƙasa, a ranta tana jera godiy ga ALLAH ga kuma Ramadhan daya bata facemask ɗin nan, dan da batasan yanda zatayiba.
Sarai ya fahimci ɗan jaridan yayi wannan magana ne saboda son tabbatar da Raudha matsayin wadda ake ta raɗe-raɗin zai aura. Sai kuma ya janye ya maida ga ɗan jaridar tare da kai hannu ya ɗora kan kafaɗarsa ya ɗan bubbuga. “Duk da hakan ba huruminka bane zan baka amsa, Ganin wadda zan aura a wajen campaign ba shine ya kamata kai da ire-irenka su maida hankali ba. addu’a da neman zaɓin ALLAH na samun shugaba na gari ya kamata mu maida hankali. Ƙuri’a kuma insha ALLAH zanje na jefa tare da my wife to be insha ALLAHU yanzun”.
Ya ƙare maganar da juyowa ga Raudha yana ɗan ranƙwafawa da maida hanunsa ɗaya baya ɗayan kuma ya nuna mata hanya. Wannan respect daya nuna ga Raudha ya matuƙar ɗaukar hankalin mutane da ƴan jaridar dake a wajen, dan take aka shiga zuba musu ruwan camaras tare da darewa aka basu hanya suka fito daga zoben da akai musu.