BAKAR INUWA 21
Wata irin nannauyan ajiyar zuciya Raudha ta saki lokacin data shiga motar da aka rage domin su, dan sauran kowa ya shiga. Shigowarsa gefenta ya sakata ɗauke numfashi, bata sake ƙwaƙwaran motsi ba har suka iso cikin Taura.
Garin ya matuĆ™ar burgeta, dan an gyarashi titi ta ko ina, ga fitulun solar ma birjik. Cike garin yake ta ko’ina da mutane saboda masu jefa kuri’a. Wani wajen kuma sifiku ne aka warware kiÉ—a na tashi da waĆ™okin da aka rerama Ramadhan iri-iri na campaign, wani gefen kuma na abokan hamayya ne. Dan duk da nan É—in tushensane wasu basa ra’ayinsa magoya bayan Alhaji Audi Ć™aura ne da sauran Ć´an takara.
A jere motocinsu da tun shigowarsu garin ya ɗauki sabuwar hayaniya suka isa ƙofar ainahin family house ɗinsu dake tamkar masarauta a garin saboda ginine na ƙawa da aka narka kuɗi wajen yinsa. Sai da suka fito Ramadhan ya miƙama Raudha katin zaɓenta da batasan dashi ba. Amsa tayi kawai tare da faɗin “Nagode” a hankali batare da tunanin yajita ba.
Bappi da Anne ne suka fara jefa Ć™uri’arsu. Sai Pa da matansa uku, sannan Ramadhan B. Hameed Taura da Raudha Ramadhan B. Taura. Har cikin rai taji haushin jin cire mata sunan Abbanta da akai aka É—ora na wanda baima zama mijin nata ba tukunna. Daga haka Yafendo da Inna ma suka jefa, sai sauran al’ummar gidan suka biyo baya.
Cikin Ć™anĆ™anin lokaci hotunan jefa Ć™uri’ar É—an takarar shugaban Ć™asa a jam’iyya mai mulki da matar da zai aura ya fara yawo a yanar gizo da kafafen yaÉ—a labarai. Sai dai wasu har sun fara Ć™ananun magana akan facemask da Raudha ta saka. Har Ć´an yarfen siyasa da abokan hammayya na faÉ—in, _Matan wasu na wahala shi yana É“oye tasa da bai riga ya mallaka ba ma..
Duk wanda ya jefa tasa Ć™uri’ar yana shigewa cikin gida ne, dan haka ita da shi tare suka shiga katafaren gidan na Taura Family da za’a iya kira da masarauta. Kamar yanda tai tunani kuwa akwai mutane sosai a ciki, sai dai ta gagara É—aga ido ta kalli kowa da komai duk da tarba ta mutuntawa data samu ga mutane. Sai dai cikin nutsuwa take gaida kowa da girmamawa batare data kalleka ba.
Da alama anan zasuyi breakfast ma, dan an haÉ—a tarin abinci kala-kala a katafaren falon da suke zaune, wanda tunda suka zauna bata sake jin muryar Ramadhan ba. Batasan a yaya ma yake amsa gaisuwar mutane ba dan ita dai a Ć™asa ta zauna kamar sauran yaran kuma taĆ™i kallon kowa. Babu yanda ba’ai ta hau kujera ba amma taĆ™i, hakan datai sai ya birge Anne da wasu tsoffi na ahalin gidan, dan wannan dai alama ne na tarbiyya.
Bayan shigowar kowa aka É—unguma dogon dining table É—in dake can gefe gari guda domin karyawa. Sai dai gaba É—aya Raudha ta kasa kai ko lauma guda bakinta. Basma sai zungurinta take ita da Rumaisa dan sune suka sakata tsakkiya. Ramadhan kam nacan falo ma bai taso zaman cin abincin ba yana waya ne……….✍