Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 28

Episode 28

BAƘAR INUWA👉🏽 AREWABOOKS👇🏾

https://arewabooks.com/chapter?id=62aafdab52e2996a61a92f3d

………..Tun bayan idan da sallar isha’i take ƙara jin zuciyarta a matuƙar ƙuntace, kewa da kaɗaici na damunta. Tana so koda a waya ne taji muryar mahaifiyarta da ƴan uwanta. Kuka taci sosai kafin ta miƙe ta shiga bayi, daga ƙudirin wanke fuska sai ta zarce yin wanka. Sosai ko taji daɗin wankan, dan sai faman sauke ajiyar zuciya take. Fitowarta kenan ɗaure da guntun towel, sai ɗan ƙarami tana goge fuskarta zuwa kunne da ƙeya inda hular wankan bata rufe mata gashi ba harya jiƙe. Murɗa handle ɗin ƙofar yayi dai-dai da ɗora hannunta saman hular wankan data rufe gashinta da shi gudun jiƙewa ta zare, da sauri ta waigo dan tasan babu wanda ke shigo mata, ko mama tambaya tun ranar bata sake shigowaba, gyaran ma ita tace ta bari zata keyi da kanta. Akan gashinta daya tarwatse bisa dokin wuyanta zuwa baya saboda waigowar da tai a fisge ya fara sauke idanunsa.
Ƙirjin Raudha ya buga da ƙarfi tamkar yanda nasa ma ya harba. Sai dai ya dake kasancewar gwani akan jin kai. Gaba ɗaya jikin Raudha tsuma yake dan bata taɓa tsammanin cin karo da shi ba, tama rasa wace tambaya zataima kanta. “Miya kawosa nan? Mi yake so? Mi zaiyi? Mi akayi?…..” haka suka dinga turereniyar fitowa daga ƙwaƙwalwarta zuwa zuciya. A gefe kuma waige-waigen abinda zata iya rufe jikinta takeyi cikin tsananin kunya da tashin hankalin ganinta a haka tamkar tsirara. Sai dai a zahiri bazaka fahimci hakan ba sai ɓata fuska ma da tai.
Shugaban ƙasa Ramadhan yaso ya juya ya koma, sai dai zuciyarsa taƙi aminta da hakan saboda sanin fitinar Anne daba ƙarewa take ba. Idan har bai cika umarninta na haɗata da ita ba to lallai kam ya takaloma kansa wani sabon abune kuma.
Idanunsa ya ɗauke tare da cigaba da takowa cikin ɗakin a ransa yana juya yanda ta wani haɗe fuska, har a zuciya ƙamshin da ɗakin keyi da sabulun da tai wanka ya masa daɗi. Dan shi mutum ne mai girmama kamshi. Kan sofar dake a ɗakin guda ɗaya tal ya kai zaune, sai sake tamke fuska yake shima kamar wanda aka aiko Pa ya mutu. Ya fara sarrafa wayar da ke hanunsa alamar neman Anne.
Da wannan damar Raudha tai azamar nufar hijjabin sallarta ta ɗauka ta saka tana ƙunƙuni. Ta sauke ajiyar zuciya duk da bawai taji nutsuwar bane dari bisa ɗari ta harari inda yake. Tabbas bata son shi, amma tana tsananin ganin girmansa da kwarjini a idanunta. Yana matuƙar cika mata ido irin wanda wani ɗa namiji bai taɓa mata ba a rayuwa. Taga girma da kimar sayyadi Abubakar a baya. Amma akan shugaban ƙasa Ramadhan sai takejin hakan na musamman ne. Cikin ture tunaninta da ƙara aro nutsuwa kan harshenta tace, “Ina yini”.
Maimakon ya amsa mata duk da yajita sai ya miƙo mata wayar hannunsa. Baiyi magana ba, amma tasan hakan na nufin ta karɓa. Jitai jikinta ya sake komawa sanyi ƙalau tunda batai tsammani ko hasashen wanene ba. A hankali ta ƙarasa takowa gabansa, cikin risinawa ta amshi wayar har yatsun hanunsu na gogar juna.
Cikin rashin sanin wanene takai wayar kunnenta. A nutse kuma tai sallama da muryarta mai sauƙin ƙarfi. Daga can Anne ta amsa mata da kulawa dan haka kai tsaye Raudha ta ganeta. A karon farko murmushi ya suɓuce a fuskar Raudha har tana nuna ɗokantuwa.
“Anne barka da dare”.
Amsar da Annen ta bata da ga can ya sata sake faɗaɗa murmushinta tana ɗan girgiza kai da faɗin, “A’a Anne ba haka bane. Kawai dai….”
Sai kuma tai shiru bata ƙarasa ba. Murmushi ta kuma saki mai sauti daya sa har shugaban ƙasa Ramadhan ɗan dubanta daga zaman ƙasaitar da yay bayansa jingine da kujerar, yanda take magana a sake da kakar tasa ya sashi ɗan taɓe baki.. wanda bai saniba zai ɗauka barci yake saboda idonsa a lumshe suke, sai dai ras yake kallo dasu dan ya kaisu ƙasane kawai kamar ya lumshe ɗin.
Ƙwayoyin idanun nasa ya janye a kanta, sai kuma ya ɗan yamutsa fuska saboda abinda zuciyarsa ta raya masa. Da ga haka bai sake yarda ya kalleta ba hartai sallama da Annen ta miƙi masa wayar tana faɗin, “Nagode”.
Bai tanka ba, bai kuma nuna alamar zai amsaba balle miƙewa. Ganin bai motsaba kuma idonsa a rufe sai tai mamaki da tunanin ko barcine ya ɗaukesa? Rashin amsa yasata miƙewa da wayar ta ajiye a table ɗin gaban sofa ɗin. Wadrobe ta nufa, ta buɗe box ɗin da aka zuba mata kayan ƴan kunenta masu muhimmanci ta ɗakko agogonsa da taketa faman ajiya tun a waccan ranar a Taura.
Inda yake ta sake dawowa ta zauna ɗofane a stool ɗin gefen kujerar, kafinma tayi magana sai taga ya miƙe, ɗan duƙowar da yay domin ɗaukar wayarsa a saman table ɗin ya sasu samun kusanci sosai. Babu shiri ta ɗauke numfashinta tsam tamkar zata shiɗe saboda kusancin nasu ya bama kamshin turarensa da fitar numfashinsa damar bugar juna da nata numfashin.
Komai baice akan agogon ba, bai kuma amsa ba ya ɗauka wayarsa zai juya.
“Ga agogonka”.
Ta faɗa da ƙyar batare da tunanin zai jita bama, dan haushi shariyar tasa ta bata. Dakatawar da yay daga yunƙurin fitar ya bata damar cigaba da faɗin, “Ranar da mukaje jefa ƙuri’a Taura ka mantashi a falo, sai Anne tace na dauka maka, kuma yazam ba tare muka taho ba dan haka na cigaba da ajiyesa a wajena”.
Karan farko yayima agogon kallon tsaf da ita kanta mai maganar, tana da yanayin sanyi a fuska, amma sam babu tsoro ko shakka a muryarta, kai tsaye take magana. Agogone mai tsadar gaske, sannan mai matuƙar muhimmanci a garesa. Dan Amnah ce ta bashi as gift ɗin anniversary ɗinsu na cika shekara ɗaya da aure. A bazata taji ya ɗaura yatsun hanunsa kan nata ya ɗauka agogon yana faɗin, “Thanks”.
Da kallo ta bisa harya fice yaja mata ƙofar, taɗan sauke numfashi da miƙewa zuciyarta na ayyana mata abubuwa masu yawa. Ta kula mutumin nan wutar kara ne sai da izo, komai da ƙarfin hali take yinsa kawai.

Koda ya isa ɗaki wayar ya tilla saman lafiyayyen gadonsa, ya ɗago agogon yan ɗan murza fuskarsa tamkar mai son ganin lokaci, sai kuma ya ɗan saki guntun murmushi mai ciwo da ɗaci. A saman laɓɓansa ya furta “ALLAH ya gafarta muku”. Daga haka ya tura agogon cikin aljihunsa tamkar ba kwanciya zaiyi ba. A kuma wani gefe yarinyar dake matsayin matar tasa a yanzu ce ke masa kaikawo a rai.


   Tun daga wannan ranar Raudha bata sake saka shugaban ƙasa Ramadhan a idonta ba sai dai a television ko ƙaton hotonsa dake a gidan tako ina. Baƙi kam har yanzu tana yinsu jefi-jefi yayinda damuwarta da kaɗaici na nan a ranta daram. A ido ta ƙara ƙyau ga mai kallo, fatarta ta sake gogewa a cikin ac da rashin fita rana. Ga lafiyayyen abinci duk da baya mata wani ɗanɗano. Bata aikin komai da ga ci sai kwanciya. 
  A yanzu fatan gani ko Aunty Hannah ne take, danta roƙa alfarmar a kawo mata koda Yasmin da su Noor ne su dinga ɗebe mata kewa. Sai dai tsit kakeji babu alamar wani nata zai tuna da sun kawota nan. Hakama da ga ɓangaren Shugaban ƙasa babu wanda ya sake leƙosu har yanzun. Gashi suna a cikin sati na biyu da kawota gidan. Takanji motsin shigowarsa wani lokacin, kai harma fitarsa da safe. Sai dai bata taɓa gigin koda leƙawa ba balle su haɗu. Shi da ya ajiyeta ya nuna ya manta balle ita.
 Dan yau ma tanajin fitarsa yana waya kamar cikin faɗa-faɗa, dan muryar nan tasa mai faɗi da amo na fitane a kausashe har tana iya jinsa da ga ɗakinta. Ajiyar zuciya ta sauke da ɗaukar Al-qur'anin ta ta hau karatu. Dama a yanzu bata da abokin hira ko ɗebe kewa sai shi. Yanda take yawan karantashi yasa har tayi sauka ta ƙara ɗakkowa daga farko, dan Raudha ta sauke alkur'ani mai girma. Tana akan yin haddane ma da wasu littafan. Babban burinta a yanzu cigaba da karatun ta harma dana boko.

    A kallo ɗaya zaka fahimci tsannin ɓacin ransa da ma duk wanda ke a cikin ɗakin taron. Su biyar ne kacal, kuma dukansu manya-manyan jam'iyyarne dake da ƙarfin faɗa aji. Wanda suna ɗaya daga cikin waɗanda suka taka rawar gani akan ganin Ramadhan ya zama shugaban ƙasa. Da farko bashi yay niyar zuwa meeting ɗin ba wakili ya naɗa, sai dai shawarar Bappi ta sashi janye wakilin ya halarci meeting ɗin da kansa.
      Chairman party da yafi kowa shiga ɓacin rai ya sake duban Shugaban ƙasa Ramadhan B. Hameed Taura. Cikin son tausasa harshensa da haɗiye fushinsa yace, 
  “Amma ina ganin ranka ya daɗe kamar ya dace a dinga bin dokokin jam'iyya da tsare-tsaren dake shimfiɗe a cikinta tun usil. Dan duk shugaban daya hau mulki a ƙarƙashinta sai ya bisu”.
      Shugaban ƙasa Ramadhan da babu abinda zuciyarsa keyi sai tafasa ya haɗiye wani ƙududun abu mai ɗaci daya tokare numfashinsa, kamar bazaiyi magana ba sai kuma yay wani munafikin murmushin takaici.
   “Ƙwarai da gaske dokar Jam'iyya nada muhimmancin daya dace kowa yay biyayya a kanta, kuma shaidane kuma inayi, amma abinda nake nuna muku anan ya dace muyi biyayya ga jam'iyya ne bisa ga abinda ke huruminta. Bance karku kawo zaɓinku a cikin jerin sunayen cabinet ba, sai dai ina tabbatar muku bazai yuwu nayi 70-30 da jam'iyya ba. Dan ina buƙatar waɗanda zasu tallafamin na sauke nauyin al'umma dake a kaina. Taya kuke tunanin zan aminta da waɗanda zasu juyani bani zan juyasu ba....”
    “Ranka ya daɗe saboda a haka tsarin yazo”.
  “Ni kuma gashi bazanbi tsarin ba”.

Shugaban ƙasa Ramadhan ya faɗa a matuƙar hasale yana watsama Mr MM daya jima da lura baya ƙaunarsa wani mugun kallo da manyan idanunsa da babu abinda kake hange a cikinsu yanzu sai tsagwaron fushi da hasala.
Ƙasa Mr MM yay da kansa zuciyarsa na suya da sake jin tsanar Shugaban ƙasa Ramadhan. Mafi yawancinsu suna takaicin ɗan yaro da shi sa’an ƴaƴansu yana jayayya ga duk abinda suka kawo. Wanda a baya duk shugabannin da jam’iyyar ta kawo bisa kujera babu wanda ya taɓa ƙetarewa.
Alhaji Balarabe kwano ya ɗan risinar da kai yana fuskantar shugaban ƙasa Ramadhan, cike da ladabin munafunci yace, “Ranka ya daɗe ALLAH ya huci zuciyarka. Inaga ya kamata duk mu kwantar da hankulanmu a sasanta. Yau kusan sati guda kenan ana maimita zance ɗaya. Tun anayi a takarda har takai yau an zauna meeting face to face, amma babu wata masalaha”.
Nan ma shiru Ramadhan yayi tamkar bazai amsaba. A ransa yana jin wani irin tsanar mulkin da takicin kansa na amsa batare da binciken sanin yanda abubuwan suke ba. Ashe mafi yawan lokuta ana zagin shugabanin ƙasa ne kawai batare da hakkinsu ba. Dan tun a washe garin daya fara zuwa office ya fahimci ba shugaban ƙasa ke mulki ba, wanda ke zagaye dashi keyi. A mafi yawan lokuta baida maraba da hoto a katako kawai. Sai dai rashin sani yasa kowa ya yayo zaginsa sai ya sauke akan shugaban ƙasa saboda shi kaɗai akema kallon mai hakkin sauke hakkin al’umma alhalin ba haka bane sam.
Yaja numfashi da ƙyar yana gyara zamansa. “Zan iya yarda da 50-50 akan Cabinet amma bisa sharaɗi guda”.
Da sauri duk suka maida hankalinsu gareshi cikin takaici. Dan 50-50 ɗin badan ta musu bane. Amma wasu har fuskarsu ta washe da murmushi tunda koba komai za’a rage.
Ya sake jan numfashi dayin rubutu kaɗan a takardar gabansa ya tura tsakkiyar table ɗin yana bin fuskokinsu da kallo a ransa dariyar mugunta yake musu. “Zan yarda bisa sharaɗin nine zan zabi speaker na majalissa. Idan kun amince kuyi singing, nima zanyi”.
“What!!”.
Suka faɗa kusan su dukansu suna waro idanu dayin zallo.
Cikin ɗage kafaɗa na I don’t care ya miƙe abinsa, guard nasa yayi saurin ja masa kujera baya.
“Duk shawarar da kuka yanke ina saurarenku”.
Ya faɗa yana nufar ƙofar da zata sadashi da office ɗinsa kai tsaye batare da yabi hanyar fita ɗakin meeting ɗin ba ta waje..
Kallon-kallo kawai aka komayi kowa ya kasa magana, dan kuwa shugaban ƙasa Ramadhan ya dakesu ne a kan jijiyar wuya dake kawo numfashin kila wa kala.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button