Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 28

Ad

_____

Episode 28

BAƘAR INUWA👉🏽 AREWABOOKS👇🏾

https://arewabooks.com/chapter?id=62aafdab52e2996a61a92f3d

………..Tun bayan idan da sallar isha’i take ƙara jin zuciyarta a matuƙar ƙuntace, kewa da kaɗaici na damunta. Tana so koda a waya ne taji muryar mahaifiyarta da ƴan uwanta. Kuka taci sosai kafin ta miƙe ta shiga bayi, daga ƙudirin wanke fuska sai ta zarce yin wanka. Sosai ko taji daɗin wankan, dan sai faman sauke ajiyar zuciya take. Fitowarta kenan ɗaure da guntun towel, sai ɗan ƙarami tana goge fuskarta zuwa kunne da ƙeya inda hular wankan bata rufe mata gashi ba harya jiƙe. Murɗa handle ɗin ƙofar yayi dai-dai da ɗora hannunta saman hular wankan data rufe gashinta da shi gudun jiƙewa ta zare, da sauri ta waigo dan tasan babu wanda ke shigo mata, ko mama tambaya tun ranar bata sake shigowaba, gyaran ma ita tace ta bari zata keyi da kanta. Akan gashinta daya tarwatse bisa dokin wuyanta zuwa baya saboda waigowar da tai a fisge ya fara sauke idanunsa.
Ƙirjin Raudha ya buga da ƙarfi tamkar yanda nasa ma ya harba. Sai dai ya dake kasancewar gwani akan jin kai. Gaba ɗaya jikin Raudha tsuma yake dan bata taɓa tsammanin cin karo da shi ba, tama rasa wace tambaya zataima kanta. “Miya kawosa nan? Mi yake so? Mi zaiyi? Mi akayi?…..” haka suka dinga turereniyar fitowa daga ƙwaƙwalwarta zuwa zuciya. A gefe kuma waige-waigen abinda zata iya rufe jikinta takeyi cikin tsananin kunya da tashin hankalin ganinta a haka tamkar tsirara. Sai dai a zahiri bazaka fahimci hakan ba sai ɓata fuska ma da tai.
Shugaban ƙasa Ramadhan yaso ya juya ya koma, sai dai zuciyarsa taƙi aminta da hakan saboda sanin fitinar Anne daba ƙarewa take ba. Idan har bai cika umarninta na haɗata da ita ba to lallai kam ya takaloma kansa wani sabon abune kuma.
Idanunsa ya ɗauke tare da cigaba da takowa cikin ɗakin a ransa yana juya yanda ta wani haɗe fuska, har a zuciya ƙamshin da ɗakin keyi da sabulun da tai wanka ya masa daɗi. Dan shi mutum ne mai girmama kamshi. Kan sofar dake a ɗakin guda ɗaya tal ya kai zaune, sai sake tamke fuska yake shima kamar wanda aka aiko Pa ya mutu. Ya fara sarrafa wayar da ke hanunsa alamar neman Anne.
Da wannan damar Raudha tai azamar nufar hijjabin sallarta ta ɗauka ta saka tana ƙunƙuni. Ta sauke ajiyar zuciya duk da bawai taji nutsuwar bane dari bisa ɗari ta harari inda yake. Tabbas bata son shi, amma tana tsananin ganin girmansa da kwarjini a idanunta. Yana matuƙar cika mata ido irin wanda wani ɗa namiji bai taɓa mata ba a rayuwa. Taga girma da kimar sayyadi Abubakar a baya. Amma akan shugaban ƙasa Ramadhan sai takejin hakan na musamman ne. Cikin ture tunaninta da ƙara aro nutsuwa kan harshenta tace, “Ina yini”.
Maimakon ya amsa mata duk da yajita sai ya miƙo mata wayar hannunsa. Baiyi magana ba, amma tasan hakan na nufin ta karɓa. Jitai jikinta ya sake komawa sanyi ƙalau tunda batai tsammani ko hasashen wanene ba. A hankali ta ƙarasa takowa gabansa, cikin risinawa ta amshi wayar har yatsun hanunsu na gogar juna.
Cikin rashin sanin wanene takai wayar kunnenta. A nutse kuma tai sallama da muryarta mai sauƙin ƙarfi. Daga can Anne ta amsa mata da kulawa dan haka kai tsaye Raudha ta ganeta. A karon farko murmushi ya suɓuce a fuskar Raudha har tana nuna ɗokantuwa.
“Anne barka da dare”.
Amsar da Annen ta bata da ga can ya sata sake faɗaɗa murmushinta tana ɗan girgiza kai da faɗin, “A’a Anne ba haka bane. Kawai dai….”
Sai kuma tai shiru bata ƙarasa ba. Murmushi ta kuma saki mai sauti daya sa har shugaban ƙasa Ramadhan ɗan dubanta daga zaman ƙasaitar da yay bayansa jingine da kujerar, yanda take magana a sake da kakar tasa ya sashi ɗan taɓe baki.. wanda bai saniba zai ɗauka barci yake saboda idonsa a lumshe suke, sai dai ras yake kallo dasu dan ya kaisu ƙasane kawai kamar ya lumshe ɗin.
Ƙwayoyin idanun nasa ya janye a kanta, sai kuma ya ɗan yamutsa fuska saboda abinda zuciyarsa ta raya masa. Da ga haka bai sake yarda ya kalleta ba hartai sallama da Annen ta miƙi masa wayar tana faɗin, “Nagode”.
Bai tanka ba, bai kuma nuna alamar zai amsaba balle miƙewa. Ganin bai motsaba kuma idonsa a rufe sai tai mamaki da tunanin ko barcine ya ɗaukesa? Rashin amsa yasata miƙewa da wayar ta ajiye a table ɗin gaban sofa ɗin. Wadrobe ta nufa, ta buɗe box ɗin da aka zuba mata kayan ƴan kunenta masu muhimmanci ta ɗakko agogonsa da taketa faman ajiya tun a waccan ranar a Taura.
Inda yake ta sake dawowa ta zauna ɗofane a stool ɗin gefen kujerar, kafinma tayi magana sai taga ya miƙe, ɗan duƙowar da yay domin ɗaukar wayarsa a saman table ɗin ya sasu samun kusanci sosai. Babu shiri ta ɗauke numfashinta tsam tamkar zata shiɗe saboda kusancin nasu ya bama kamshin turarensa da fitar numfashinsa damar bugar juna da nata numfashin.
Komai baice akan agogon ba, bai kuma amsa ba ya ɗauka wayarsa zai juya.
“Ga agogonka”.
Ta faɗa da ƙyar batare da tunanin zai jita bama, dan haushi shariyar tasa ta bata. Dakatawar da yay daga yunƙurin fitar ya bata damar cigaba da faɗin, “Ranar da mukaje jefa ƙuri’a Taura ka mantashi a falo, sai Anne tace na dauka maka, kuma yazam ba tare muka taho ba dan haka na cigaba da ajiyesa a wajena”.
Karan farko yayima agogon kallon tsaf da ita kanta mai maganar, tana da yanayin sanyi a fuska, amma sam babu tsoro ko shakka a muryarta, kai tsaye take magana. Agogone mai tsadar gaske, sannan mai matuƙar muhimmanci a garesa. Dan Amnah ce ta bashi as gift ɗin anniversary ɗinsu na cika shekara ɗaya da aure. A bazata taji ya ɗaura yatsun hanunsa kan nata ya ɗauka agogon yana faɗin, “Thanks”.
Da kallo ta bisa harya fice yaja mata ƙofar, taɗan sauke numfashi da miƙewa zuciyarta na ayyana mata abubuwa masu yawa. Ta kula mutumin nan wutar kara ne sai da izo, komai da ƙarfin hali take yinsa kawai.

Ad

_____

1 2Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button