Bakar InuwaNOVELS
BAKAR INUWA 28

Shigarsa office ɗin baifi da minti biyu ba kiran Gimbiya Su'adah ya shigo masa. dole ya danne ɗaci da fushin dake a zuciyarsa har maƙoshi ya karɓa mata da girmamawa. Har yanzu haushinsa takeji, dan haka cikin kaushin murya ta sanar masa su Lubnah zasu zo musu hutu. Ba zuwansun bane ya bashi mamaki koya damesa. Jin har su biyar zasu zo da sunan hutu, bayan a cikinsu akwai wanda ke aiki da karatu.
“Okay Maa, amma kuma su su Lubnah aikinsu fa? Sannan Basma duka yaushe ta fara zuwa school da zata fara sakaci da shi?”.
A zafafe gimbiya Su'adah tace, “To sai akace maka bazasu iya zuwa daga nan ba ne? Zanje ganin likita na ne london, idan kuma baka buƙatar suzo ɗin sai su wuce Bina”.
“Am sorry Maa ba haka nake nufi ba. Insha ALLAH nima zan shigo gidan cikin weekend ɗin nan”.
Bata amsashi ba, sai ma yanke kiran da tayi. Ya rumtse idanu da ƙarfi, tare da tura lip ɗinsa na ƙasa cikin baki ya hau tauna da ɗan ƙarfi. Waɗan nan takaicin ya hanashi yin komai yau a office, duk da dai dama aikin bawani mai tsauri bane duk tsare-tsarensane akan ayyukan da yaga ya dace ya fara shimfiɗawa kodan tukuyci ga talakawan da suka tsaya a rana domin zaɓensa.
__________________
Tun bayan tashin shugaban ƙasa a meeting ɗin wasu a cikin yaransu suka sanar musu da sharaɗin daya kawo na yarda da 50-50 akan cabinet saɓanin 70-30 da suka tsara. Ransu ya ɓaci suma matuƙa, basuyi ƙasa a gwiwa ba wajen miƙa zancen ga nasu god fathers ɗin. Suma da ga can hankalin nasu a tashe yake, kuma ransu a ɓace yake. Duk da kasancewarsu a mabanbanta gari a wannan ranar suka nufo Bingo gaba ɗayansu suka haɗu domin tattaunawa. Sai dai zaman nasu bai samu akan lokaci ba sai wajen sha ɗaya na dare. Tsabagen ƙwarewa a siyasa kuma kusan ƙarfe huɗu na yamma sai da suka kaima shugaban ƙasa Ramadhan gaisuwa har office.
Yayi farin ciki da zuwansu, ya kuma girmamasu matsayinsu na manyan ƙasa kuma kakanni a garesa, dan dukansu zama su iya girmar Bappi, wasu kuma sa'anni da shi. Su ɗin kowa yasan manyan mutanene a ƙasar kuma dattijan arziƙi da sukai hidima ma ƙasa shekaru masu yawa da suka shuɗe. Sannan mutanene masu dattako da bazaka taɓa jin bakunansu akan mulkin ƙasar ba har sai idan ta ɓaci. Sai dai abinda ƴan ƙasa dama shuwagabannin basu sani ba, waɗannan dattijan lulluɓin biri ne kawai a jikin kuraye, sune ke juya ƙasar NAYA bisa table tamkar mulmulallen ƙarfe bisa ƙarfe. Duk wani shugaba da zai hau a gwamna ko shugaban ƙasa sai da yardarsu, sannan duk wani mai taimaka masa da zai naɗa sune da kaso mafi yawa a ciki, shiyyasa a kowanne mulki, a kuma kowacce jaha yaransu ne akan madafun iko.
Kamar gaske shawarwari masu daraja suka bama shugaban ƙasa Ramadhan. Wanda yaji daɗinsu kuma yay farin ciki dasu, barin office ɗinsa kuma bai wuce da awa guda ba har zuwansu gareshi da shawarwarin da suka bashi sun watsu kafafen yaɗa labarai dama yanar gizo. inda kowa ya samu damar tofa albarkacin bakinsa. A mafi yawan Comments ɗin kuma ya ta'allaƙa ne ga yabonsu da jinjina mutuncinsu a idanun al'ummar ƙasar NAYA.
11:00pm
Su dukansu biyar zaune suke a cikon falon gidan ɗaya daga cikinsu mai ƙarancin haske kasancewar an kashe mafiya yawan fitulun. Sai yaransu huɗu irin su shugaban jam'iyya, da Alhaji Yaro glass sai shugaban ƙasa mai sauka Usama S. Hamada da Mr Mike Bando vice president ɗinsa.
Bayan sun gama sauraren ƙarin bayanai daga bakunan yaran nasu oga kwata-kwata mai shugabantar tawagar dattijan ya ajiye kofin shayin hanunsa yana wani shegen murmushi da faɗin, “Da alama yaron nan bazaiyi tsahon ran cika 2years ba, kamar yanda mukai masa fata”.
Sauran dattijan huɗu sukai ƴar dariya, yayinda su su Alhaji Yaro glass basuga abin dariyarba anan. Dan har cikin rai sun fara jin fargaba akan taurin kan shugaban ƙasa Ramadhan.
“Amma ranku ya daɗe kenan zamu yarda da sharaɗinsa?”. Forma Vice president Mike Bando ya faɗa cikin jin ɗaci.
Wanda ke kusan tsakkiyar dattijan zaune ya ɗan taɓe baki da faɗin, “Well! Zamu iya yarje masa zakuma mu iya jayayya da shi. Sai dai ku sani dukansu biyu sunada haɗari. Yarje masan, da kuma yin jayayyar”
Cikin takaici Alhaji Yaro glass yace, “Kenan ranka ya daɗe wannan ƙaramin alhakinne zai zamar mana ƙadangaren bakin tulu, ya ringa juyamu yanda yake so? Wai mizai hana ya mutu ne a wata shida?”.
A tare dattijan suka kwashe da dariya. Sai kuma suka gimtse fuska. “Haka tunaninsa ke ayyana masa, shiyyasa har ya sharɗanta abinda ke a zuciyarsa. Shi yaro ne, baisan siyasa ba, bai san komai nata ba, bai san wahalar rayuwa ba dan cikin dukiya ya tashi. Dan haka wannan ba tunaninsa bane...”
Da mamaki suka dubi oga kwata-kwata da yay maganar. Murmushi ya sakeyi batare da damuwa da kallon da suke masan ba. Yakai yatsunsa biyu ya ɗan ɗalli bowl ɗin gabansa mai ɗauke da fruits. “Tabbas ba tunaninsa bane, wannan tunanin Alhaji Hameed Taura ne. Dan haka shine zai fara mutuwa kafin yaron”.
Ya ƙare maganar cikin kaushin murya da ɗaure fuska. A take su alhaji yaro glass suka shiga kallon-kallo. Dan su kam bama su hasaso hakan ba a ransu, tunda sun san shima Ramadhan ɗin gwanine na taurin kai da rashin mutunci. Har cikin rai wannan abu yay musu daɗi, kuma sunyi na'am da shi. Dan kuwa mutuwar Alhaji Hameed Taura suma shine burin ransu..........✍