BAKAR INUWA 48

Magunguna ta bata tare da wani bayanai a rubuce tace ta bama Ramadhan ba nata bane.
Kamar yanda akace shi ɗin zata bamawa kuwa bata buɗaba ta ajiye ta cigaba da sabgar gabanta. Tayi fes da ita, da alama kuma makaranta ta fara buɗe mata
idanu da wasu abubuwan. Gashi bata wasa sam da karatu sosai take nuna ƙwazo dake bama su Basma dama class mate ɗin nata mamaki. Gashi taƙi yarda kowa yasan
ita wacece, koda yaushe fuska a ƙunshe da niƙab. Bata shiga harkar kowa sai su Basma. Wasu na mata kallon girman kai wasu kuma tana ɗan birgesu duk da basu
san wacece ita ba. Suma su Basma kuma sun kame bakinsu saboda gargaɗin Ramadhan da Anne.
★Kasancewar yau juma’a da wuri ta dawo school. Ta zube a falo Bilkisu na mata dariya. “Aunty ahaka za’ai karatun kuwa?”.
Dariya itama Raudha tayi tana ajiye ruwan data sha sosai. “Wlhy bazaki ganeba Aunty. Abunfa babu sauƙi sam. Dan masifa yau text har biyu mukayi ga
submitting Assignment ɗin masifaffen malamin nan da nake gaya miki”.
Cikin dariya Bily tace, “Haka ake shan yaƙi ai Aunty har a cimma nasara. Fatanmu dai ki fito da first class duniya tasan firt lady ɗinmu bata wasa
bace”.
Dariya Raudha tai tana miƙewa. “Uhhm Aunty Rabani da wata first lady. bara na watsa ruwa nazo naci abinci ko breakfast banyiba yau”.
Bayan tayo wankan anan suka baje a falon bilkisu na sake nuna mata aikin yau da mata ƙarin bayani. Salla kawai ke tadasu har magrib. Sam Raudha batasan
yau shugaban ƙasa zai dawo ba dan tunda ta shigo gidan basu buɗe tv ba. Bayan sallar isha’i taɗan sake watsa ruwa. Fitowarta kenan a toilet ɗin ta samu
wayarta na ringing. Cike da zumuɗi ta ɗaga ganin Fatima. Tun jiya suka sanar mata yau zasuje Hutawa duba Abba (Dauda) da baida lafiya. Taso zuwa amma babu
dama har kuka tayi. Sai dai ta ƙudiri niyyar idan Ramadhan ya dawo zata roƙesa alfarmar zuwa itama. Bayan sun gaisa dasu Fatima har dasu Inna Fatisa ke
sanar mata ga ƙawarta Zubaida da tazo duba Abban su gaisa.
Cike da mamaki tace “Zubaida fa? Dama bata mance ina duniya ba?”.
“Ni na isa first lady ɗinmu. Ranki ya daɗe kin wuce a manta dake ai a ƙasar NAYA ”.
Zubaida data amsa wayar ta faɗa.
“Mara kirki bazaki canjaba dai?”.
Cewar Raudha cikin dariya.
Dariya itama Zubaida ɗin tayi, kafin su gaisa a mutunce. Zubaida ƙawartace ta islamiyya. Itama yarinyace mai ƙwazo da sanyin hali kamar Raudha. So da
yawama akance halinsu yazo ɗaya ne shiyyasa suke abota. Duk da abotar tasu bawai takai mai tsanani bace da har suka san sirrikan juna musamman ma Raudha da
ba’a jin cikinta. cikin tsokana Zubaida ke faɗin, “Halan kin kusa sauke mana babynmu ranki ya daɗe”.
Raudha tai dariya tana ɗakko kayan da zatasa a Wadrobe. “Aiko gashi ma har yana motsi a ciki, ina fatan kun shirya zuwa suna”.
Dariya sosai Zubaida keyi. Itama Raudha haka. “Uhm matsoraciya keda rakin nan naki ace cikin ya tsufa za’aji muryarki haka ragal”.
“Tabɗi mi kika ɗaukeni. Ki shirya zuwa Bingo kiga yanda nake daram kuma ga ƙaton cikin ƴan biyunku tare dani. K cikinfa ba wani wahala kwantar da
hankalinki ke huɗu zaki samo mana lokaci guda……”
“Idan ita bata samoba ke zaki samoshi yau ɗin nan”. A mugun firgice Raudha ta juyo har towel ɗinta na ƙoƙarin kwancewa jin muryar wanda batai zatoba
balle tsammani. Sanye yake cikin kananun kaya tausasa gaba ɗaya baƙaƙe. Ya ƙara wani fresh abinsa harda ɗan tumbi alamar hankalinsa kwance yake. Ga sumarsa
data sake samun kulawa na gyara. Sam batasan ya dawo gidan ba balle shigowa ɗakin dan ko shigowar motocinsa yau batajiba sam kokuwa hankalintane bai a
wajen, ta diririce da rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi ganin ita yake nufowa. Har yazo gab da ita bata samu mafitar kare kanta da ko saka hijjab ba. Ta
cikuykuyo wasu kaya zata yafa a jikinta ya riƙe yana mai zagayawa ta bayanta ya rungumota jikinsa.
Wayar ya zare da kallon screen ɗin, tuni dama ta yanke kiran, sai dai hakan bai hanashi ganin da Fatima tai wayar ba. “Ai bansan kina bukatar ƴan uku ba
Ustazah da tuni na ajiye ƙawancenmu gefe na baki ajiyarsu”.
Innalillahi ina ƙasa Raudha ta shige ta huta. Ya sake kanainaiyeta jikinsa da kai hannun kan ɗaurin towel ɗinta zai kamar zai kwance. Da wani irin zafin
nama ta wulƙito ta rungumesa jikinta na rawa sai ambaton “Innalillahi…” take har ƙarshe. Shiko mizaiyi inba dariya ba. Sai dai yay dauriyar gimtsewa
abinsa ya sake kama towel ɗin data ƙanƙanme cikin hannu ta gaba ɗaya. “Dan ALLAH ka rufamin asiri karka cire Ya Ramadhan. Inba hakaba zan iya rasa
numfashina”.
“Sai in baki nawa mu rayu tare ai”.
Ya faɗa cikin raɗa da wata irin murya mai wahalar fassara ga Raudha.
Raudha ta sake ƙanƙamesa saboda yanda zuciyarta ke masifar gudu cikin ƙirjinta. Tunda suke bai taɓa mata kalar abun nan ba. Iyakarsa taɓa hanunta
fuskarta ya dan sumbata ko laɓɓanta. Amma bai taɓa gwada ɗora hanunsa a wani sashe na jikinta ba sai yau. Dan kuwa a bazata taji saukar hanunsa kan
ƙirjinta.
“Na shiga uku”.
“Baki shiga uku ba. Ai maganar kunya kuma ta kare insha ALLAH yau zamu neman ƴan huɗu…………✍