BAKAR INUWA 51

dama sanda ya gansu da Bilkisu yaga kamar tafiyarta ba dai-dai ba, sai dai bai samu damar gama ƙare mata kallo ba suka shige. Falon ya koma dole wajen Bappi
suka cigaba da hirarsu har Pa. Dama zai kira Anne ɗinne kamar yanda Bappi ya sakashi, koda ya dawo sai ya ce masa bai gantaba amma yaji ƙarar ruwa a
bayi….
Babu abinda take sai sakin ajiyar zuciya a jajjere, Anne dake kallonta cike da tausayi ta nuna mata bakin gado tana miƙa mata shayi data saka aka
haɗo mata, sai gasashshen nama da akaima haɗi na musamman dan zuwa yanzu ta tabbatar da abinda ke faruwa. Kokwanton da ranta keta mata yasata kiran Dr Hauwa
tunda itace ta duba Raudha a wancan likacin da sukai zargin cikine da ita da kuma zubewar cikin. Dr Hauwa da take ɗaukar Anne matsayin uwa ta faɗa mata
gaskiyar lamari akan kowancan karon ciwon marane kawai irin na period, hakama lokacin da akace tayi ɓari maganin zubda ciki tasha batare data sani ba, amma
Ramadhan yace suyi shiru dan zaiyi bincike akan wanda ya aikata zuba maganin da Raudha tasha., kuma bayan shi Raudha ta karayi har sau biyu tama dubata akan
hakan, itace kuma ta sanarma Ramadhan mafitar da zai iya dakatar da Raudha daga azababben ciwon marar da take fama dashi a kowanne period.
Godiya Anne tai mata ta yanke wayar, shiyyasa kafin ma Raudha ta fito Anne tasa aka kawo mata wannan abincin da tasan zai taimaka mata. “Maza kici
kafin a samo miki magani”.
Yunwar takeji, amma sam bata son cin abincin. Sai ma wani irin barci dake fisgar idanunta. Haka ta daure taci abinda zata iya tace ta ƙoshi. A kusan
tare Ramadhan da Anne suka shigo ɗakin. Sanye yake cikin kananun kaya da tun ɗazun ya canja. Anne ce kawai ta amsa masa sallamar da yayi cikin tsuke fuska.
Raudha kam dake fama da kunyarsa dama bata yarda ta motsa ba, ba kuma ta ɗago ba.
Zama yay a ɗaya daga sofa’s ɗin. Idanunsa akan matarsa da yakeji kamar yaje ya rungumeta, sai dai ya daure ya fuske dan tunda yaga yanayin Anne
yasan fushi take da shi. Yanzun ma maimakon ta kirashi da wayarta Bappi tasa ya kirashi yana sashensa yana ƙullawa da kwancewa akan yanda zaizo ya tafi da
Raudha can.
A hankali ya janye idanun nasa a kanta yana jingina kansa jikin kujera ya lumshe su. Cikin ɗan furzar da numfashi yace, “Anne gani”.
Shiru kamar bazata kulashi ba, tanata ƙoƙarin sakama Raudha safa mai kauri a ƙafa bayan ta mulke ƙafar da wani mai da ita tasan amfaninsa. Sai da ta
gama tsaf ta kamo hannayen Raudha suma ta shafa mata man ta saka mata safar hannu sannan tai magana batare data dubesaba tana rufe man. “Magani nake buƙata
da zata sha”.
Idanunsa ya buɗe tare da ɗagowa. Sai ya saukesu akan Raudha da sam taƙi kallon ko inda yake har yanzu. Kafin cikin ƙanƙan da murya yace, “Waye baida
lafiya?”.
Wani shegen kallo Anne ta zubo masa cike da harara kai kace idonta ne zai faɗo. Daƙƙuwa ta watsa masa a zafafe tace, “Ramadhan ungo wannan.”
Tattausan murmushi ya saki mai sanyi yana lumshe idanu ya sake buɗewa a lokaci guda. Fuska ya ɓata sosai cike da marairaicewa kamar ba shugaban ƙasa
Ramadhan ba. “Waini Anne kamarma fa kinajin haushi na..”
Harara ta sake dalla masa tana janyo burner ɗin turare kamar zata jeho masa. “Oh saima yanzu ka fahimci haushin naka nakeji ashe….” ta ƙare maganar
dayin kamar zata jeho masa har abin yaso bama Raudha dake kallonsu ta wutsiyar ido dariya. Amma saita gimtse yana sake kauda kanta dake mata tsananin ciwo
gefe…
Hannu ya ɗaga mata alamar surrender. “Kinga yi haƙuri ajiye burner ɗin. Ina arziƙi ranar Monday a ganni da fasashen kai azata matata ce ta fasamin”.
“Oh to bara na fasa ɗin ai gara sumayi zaton hakane koba komai ta rage zafin muguntarka”.
Tasowa yay daga kujerar murmushinsa na sake faɗaɗa. Ya zauna kusa da Raudha a gefen gadon yana mai ruƙo hanun Anne ya amshe burner ɗin. “Yi haƙuri
tagaba goshin Bappi yanzu mi akeso nayi?”. Yay maganar da juyawa yana ɗaura hanunsa a goshin Raudha da kunya ta dabaibaye kamar ta nutse saboda yanda ya
zauna gab da ita sosai duk da baya taɓa jikinta dai.
Mikewa Anne tai tana mita ta fice. Ka tambayeta abinda ke damunta kasa a nemo mata magani kafin na dawo kuma ku tattara ku barmin ɗaki barci zanzo
nayi”.
Gwalo ya ma bayan Anne, kafin ya maido dubansa ga Raudha. Jawota kawai yay jikinsa ya rungumeta baki ɗaya. Rawa jikinta ya farayi kaɗan-ƙaɗan har yana
iya jin gudun da zuciyarta keyi. Ga zafin da jikinta ya ɗauka sosai na ratsa shi.
“I’m sorry Ustazah”.
Ya faɗa a hankali cike da tausayinta. Ita dai babu bakin magana, sai ma lafewa da tai duk da tsoron dake tattare da ita nashi. Kusan mintuna uku suna a
haka kafin ya ɗagota daga jikinsa, hannu yasa ya share mata hawayen dake sakko mata a kumatu. “Yi haƙuri kukan ya isa haka Sweetheart, amma miyasa ɗazun
baki shiga ruwan dana haɗa miki ba”.
A hankali yake maganar cike da nutsuwa. Da ƙyar Raudha ta iya buɗe baki tace, “Akwai zafi ne”.
“Ai zafin shine zai taimaka miki Ameenatu, gashi ƙinyin haka ya saka miki zazzaɓi har kin tone mana asiri wajen Anne dama duk mai hankali da zai lura
da tafiyarki a gidan nan ɗazun”.
A ɗan tsoroce ta ɗago manyan idanunta a karon farko ta kallesa. “Ya Ramadhan kowa ya sani kenan?”. Tai maganar cikin rawar murya wasu hawayen na
rige-rigen sakkowa. Dariya da tausayi ta bashi lokaci guda. Maimakon ya bata amsa sai ya sake rungumeta. Kusan minti biyu ya sake ɗagota. “Kinga tashi muje
kisha magani dan tun ɗazu nasa aka kawo miki. Ga shi Anne dama ta koremu duk da nasan itama ba iya kwana zatai anan ba sai a bayan Bappi. Shiyyasa kema
takeso kije jikin mijinki ki kwanta ki more..”
Hannunsa ta turo dan yanda yay maganar da abinda hanunsa ke mata sai kunya ta sake lulluɓeta. “Ni ALLAH ka bari”.
“Uhhm iyayi, nasan dai kinana daɗi ya rufeki bazaki kwana batare da mijinki ba.”
“Innalillahi… ALLAH Ya Ramadhan ka iya sheri”.
“Su Yaya anji jiki, wane Yayane zaiyi bidirin da nai a daren jiy…..”
Hannu tasa ta toshe masa baki da sauri kafinma ya ƙarasa. Da ƙyar ya iya danne dariyarsa yana janye hanunta. “To shikeman nayi shiru”.
Yasan ya kora su Basma tun ɗazu, Anne kuma tana sashen Bappi, sai kawai ya duƙa wai Raudha ta hau ya goyata. Ƙin yarda tayi itakam. Ganin zata cigaba
da ɓata lokacinsa ya ɗauketa cak suka fice tanata mutsu-mutsu da roƙon ya sauketa bai saurareta ba. Dole tai saurin saƙalo hannayenta a wuyansa jin kamar
zata faɗi. Ta lumshe idanunta da hawaye ke zaryar fitowa kunya kamar zata halakata, fatanta suje lafiya inda zasu batare da wani ya gansu ba……….✍
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹