Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 53

datai mata ƙyau matuƙa, ga ɗinkin ya fidda jikinta tsaf kamar ka saceta ka gudu. Ɗauri tai mai sauƙi amma ya mata ƙyar ta saka ƴan kunne kawai harda yafa

mayafi sannan ta fito da nufin zuwa gaida mutanen gidan duk da kunya da nauyin ƙin zuwa akan lokaci na cinta. A tunaninta Ramadhan ma nacan, sai dai tana

fitowa falo taci karo da gogan nata zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallon labarai a television da alama sallar azhar yaje yayo kawai ya dawo.
     Tsamm tayi a ƙofar ɗaki kamar bazata karaso ba. Sai kuma cikin dauriya ta cigaba da takowa har inda yake. Kanta a ƙasa tana wasa da zobon hanunta tace,

“Ya Ramadhan zanje naje na gaida su Anne”.
    Maimakon ya amsa mata duk da idonsa ba’a kanta yakeba sai taji ya riƙota ya zaunar saman cinyarsa. Mutsu-mutsu zata fara ya dakatar da ita ta hanyar

yaye veil ɗinta gaba ɗaya. “Banda ƙauyanci miye na zuwa gaban miji da veil?”.
        Duk da maganar ta bata haushi sai ta dake. A sanyaye tace, “Wajensu Anne fa zanje”.
      Wasa yake da jelan kitsonta idonsa a tv, “Sunce sun yafe yau ko ƙofar corridor ɗin can bazakije ba nayi gaisuwan da taki ai tun ɗazun”.
      “Kai Ya Ramadhan wlhy bai kamataba ace banje na gaishesu ba. Gashi dama lokaci ya gama shigewa ai da kunya”.
        Maimakon amsa mata maganar ko barinta tafiya sai ya ɗagata daga jikinsa shima ya tashi, dining ya nufa da ita dan shi ta yunwar cikinsa ma yakeyi.

Dolo ta haɗiye komai dan yaci serious kamar bashi ba. Tsorone yaɗan fara kamata na gudun karfa mutumin nan ya juya mata baya bayan ya rabata da mutuncinta.

Dan taga tun jiya ya koma sha mata ƙamshi irin yanda yakeyi mata a baya. Da wannan tunanin tai saving nashi komai, zata zuba nata ya hanata yay mata nuni

data zauna kawai. Dole tabi umarninsa zuciyarta fal tsoron abinda ba haka bane. Shi Ramadhan yana ɗan ɗaurewa ne kawai dan gujema abinda zuciyarsa ke

kwaɗaita masa game da ita. Dan tausayinta yakeji matuka. Amnah mai shekaru da suke gab da nashi duk da tanada lalura bata iya jure ɗaukarsa akoda yaushe

balle ita. Dan sauda dama idan yaje gareta sai tayi kuka balle Raudha da yakema kallon jaririya. Shi kansa yasan yayi juriyaa shekarun da babu Amnah, amma

ya tabbatar ɓacin rai da tashin hankaline suka girmama juriyar tasa, yanzu ko daya ɗan ɗana bayajin zai ɗaga ƙafa duk da ƙoƙarin hakan da yakeyi.
      Tare sukaci abincin Raudha nata sinne-sinne. Shi dai bai kulataba. Daga ƙarshema ya amshe cokalin ya koma bata da kansa. Ina ƙasa ta shige amma babu

damar gardama dan ya haɗe girar sama data ƙasa……..✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button