Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 58

Episode 58_*

……….A hankali ta saki numfashi tare da nannauyar ajiyar zuciya ganin Bilkisu ce ba wanda take fargabar haɗuwar da shi ba ko’a hanya bare a cikin ɗaki

da ga ita sai shi. Zama Bilkisu tai kusa da ita tana kai hannu a goshinta. “Aunty Lafiya kuwa kika dawo da w….”
     Maganar tata ta maƙale jin jikin Raudha da zafi. “Ya salam baki da lafiya yauma ko? Dan ALLAH ki yarda muje ko cikin clinic ɗin gidan nanne inma bazamu

je wajan Mommyn Jabeer ɗin ba. Aunty wai zaki cigaba da cutar da kankine akan Yaya Ramadhan ne? Kin hana na faɗama kosu Anne halin da kuke ciki, ni kaina

ɓoyemin abubuwa da yawa kikeyi wlhy. Harga ALLAH nidai na gaji da shurun nan da kika dabaibayeni da haɗani da ALLAH akan nayi”.
       Murmushi Raudha tayi tana haɗiye hawayen dake son zubo mata. Ta tashi zaune cike da ƙarfin hali ta kamo hanun Bilkisu cikin nata. “Aunty B kiyi

haƙuri dan ALLAH, ban hanaki gayama su Anne bane sai dan yanda kike kallon matsalar ba haka take ba. Aiki ne kawai yay masa yawa, sannan ni babu wani abu na

rashin daɗi dake tsakanina da shi, kawai dan ba zaman gidan yake kamar da ba saboda ayyuka yasa kike ganin akwai matsalane. Kinga babu dalilin kai ƙara akan

laifin da babu shi aunty. Nasan kina ganin kamar auren nan nasane cutarwa a gareni shiyyasa. Dan ALLAH kibar damuwa ALLAH ni banajin komai akan hakan duk da

nasan dole ne naji kishi matsayina na matarsa. Amma karki manta Aunty ALLAH ya bashi damar yayi huɗu, a addinance ma da biyu aka fara, sannan uku, sannan

huɗu. Sannan a yanayin da Ya Ramadhan ke ciki dama ya kamata ace yanada mace mai ilimi da zata jagoranci wasu abubuwa na mulkinsa bawai irina da iyakata

secondary ba kuma mai ƙarancin shekaru. Karki manta aunty yanzufa nake shekara ta shatara kawai a duniya, koba komai kuwa Aynah nada kusan ashirin da tara

ko talatin da ɗaya ko fin hakan ma, sannan tayi ilimi mai zurfi daga ƙasar NAYA har wajenta. Tako ina ta cancanci zama matarsa koda nauyin al’umma dake a

kansa”.
      “Humm Raudha sam ban gamsu da wannan bayanin naki ba. Babu ruwan hankali da ƙarancin shekaru, hakama babu ruwan sanin yakamata da ilimi. Mutane nawane

a zamanin da basuyi ilimin boko ba amma sunada basirar tsara abinda ko professor na yanzu bai iya tsarawa ba. Kai har a wannan zamanin akwai wanda basuyi

ilimin boko ba amma wlhy idan sukai miki wani abun sai kinsha mamaki. Hakama shekaru, shekaru baga kowa suke taka rawar hankali ba ga mai su. Zakiga mutum

da shekarun manya amma idan yana tafka miki baranɓarama ke kyace ɗan goma sha ne. Kuma kiga karamin yaro na gyara masa. So ni a tawa mahangar banga ta inda

Aynah zata taimaki Brother ba wlhy. Ƴar uwatace ita kuma jinina, amma bazan ɓoye miki cewar inaji a raina akwai manufa acinkin wannan al’amarin ba Raudha.

kuma insha ALLAH bazan gajiyaba wajen ganin na daƙile hakan sai dai in ƙaddararsa ce zama da ita”.
   Tana gama faɗa ta mike ta fita hawaye na sakko mata a fuska. Da kallo kawai Raudha ta bita sai itama ta fashe da kuka. Sai da tayi mai isarta sannan ta

mike ta shiga toilet ta wanko fuskarta….

(ALLAH ka bamu ikon cinye jarabawa a duk yanda tazo mana????????????).

___

          A ɓangaren su Gimbiya Su’adah kuwa shirin biki suke na ƴaƴan gata, dan a wannan gaɓar ko auren Lubnah da Bilkisu bata bama muhimmanci ba kamar na

Ramadhan da Ayna’u. Babu abinda zuciyarta ke raya mata sai cewar zata haɗa cikar birinta da maido ɗanta ƙarƙashin umarninta ta kuma rabashi da wadda ta zame

mata ƙayar kifi a maƙoshi badan ta taɓa mata wani laifi ba ko kuskure.
      Hatta da Ramadhan yanzu wani gata take masa na fitar hankali ita da su fulani da uwar gayya Addah Asmah. Baya iya jera sati baizo gidan ba a sace.

Takai yanzu ko sashen su Anne baya shiga sai dai suji labarin yazo a bakin Basma. Hatta yin waya ya rage dasu, komansa gimbiya Su’adah. Ko abu ya shige masa

akan harkar mulki maimakon kiran Bappi da yakeyi ko Anne a da sai ya kira Gimbiya Su’adah yanzun. A mafi yawan lokuta shawarar tata bata haifar da ɗa mai

ido a garesa. Dan kuwa dai gadarace kawai da son nuna isa take ɗorasa akai, ALLAH ne kawai ke taimakonsa da in yay maganar da Cos sai yay saurin faɗama

Bappi shi kuma ya gyara, wani lokacin idan Bappi ya kirasa yace kar ai kaza ɗin nan kaza ya kamata ayi har haushi yakeji, ya dinga ƙunkuni kenan yana cika

yana batsewar fushi. Idan kaga haƙoransa a waje yanzu to tare yake da su gimbiya Su’adah. Aynah kam kamar yanda bokan Adda Asmah ya faɗa mata a ɓoyeta kar

Ramadhan ya ganta har sai an kaita gidan gwamnati haka akai, sai suka fake da cewar gyaran jiki ake mata, amma a zahiri umarnin boka suke bi, dan ya

tabbatar musu inhar Ramadhan yay ido huɗu da Aynah kafin aure duk wani sihirin jikinsa sai ya warware.
    Game da Raudha kuwa a yanzu basu da lokacinta, dan su tunaninsu sun gama da shafinta lokacin komawarta gidansu kawai suke jira. Shiyyasa ko bibiyar

lamarinta basa waniyi gaba ɗayansu.

        Mutane har yanzu basu farga da halin da Ramadhan ɗin ke ciki ba, sai dai yanayinsa na kullum fuska a cunkushe yanzu kansa wasu yin kananun magana.

Ƴan adawa kuma suka samu na suka a garesa da sake dawo da furicin nan na mai girman kai garesa.

      Pa da duk abinda ake a gidan ya saka ido badan baya cikin damuwa da halin da ɗansa yake a ciki ba. Ya barine kawai azo gaɓar da gimbiya Su’adah zata

gane kurenta. Sai dai a yanzu bita da ƙullin daya shirya musu akan shirin da suke gagarumi na auren ne. Dan ko events an haɗa yakai kala goma, sanin Taura

family ba’a wannan almabazaranci sai suka fake da cewar duk a gidansu amarya aka ɗauki komai. Lokacin da gimbiya Su’adah tazoma Pa da zancen dariya sosai

abin ya bashi. Amma sai ya gimtse kayarsa yace ALLAH ya bada sa’a.
     Daɗine ya kama gimbiya Su’adah, dan gani take yanzu fa kamar ta fara samun kan Pa ɗin a dalilin turaren da Adda Asmah ta kawo mata tace tai amfani da

shi a duk sanda zataje gareta. Dukan wata bukatarta sai ya amsa babu musu sai ma shakkarta da zai dingayi. Murmushi tai tana ficewa cike da tafiyar takama.

A ranta kuwa sakama Addah Asmah albarka take da yaba mata. Dan ta tabbatar wannan turare shike taimaka mata wajen hawa kan Pa ɗin yanzu a yanda takeso. Amma

da tasan bata isaba indai wannan uban kafiyar ne da taurin kai.
    Bayan ficewarta nannauyan numfashi ya sauke da girgiza kansa, sai kuma ya saki murmushi tausayin ɗansa na ƙara ratsa masa zuciya. Mikewa yay ya fice

sashen mahaifansa. Acan ya samu har su Yafendo suna hirarsu cike da farin ciki kamar yanda suka saba.
     Bappi dake shan fura ya ɗan tsura masa idanu cike da nazarin ɗan nasa. Sai kuma ya ɗauke kansa. Ita kanta Anne idanun nata a kansa suke, dan tun

shigowarsa ta fahimci akwai damuwa tattare da shi. Bayan ya gaishesu Inna ke faɗin, “Bashari lafiya kuwa na ganka kamar mai damuwa?”.
     Ɗan murmushi yay mata yana furzar da huci. Sai kuma ya gyara zamansa sosai yana fuskantarsu. “Lafiya lau Inna, kawai nazo nayi magana da ku ne in ba

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button