Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 58

damuwa”.
    Yafendo tace, “Faɗi kanka tsaye Bashari mike faruwa?”.
     Jin Anne da Bappi basuce komai ba ya sashi dubansu, sai dai yanda suka maida hankalinsu garesa suma ya sashi sauke ajiyar zuya. “Ba komai bane dama

akan Ramadhan ne da wannan auren nasa.”
       “Ba mun wuce wannan babin ba mi kuma ya faru?”.
Bappi ya faɗa yana kallonsa fuska a tsuke.
      “Kayi haƙuri Bappah, bawai na dawo da hanun agogo baya baneba. Kawai ina son muyi wani abune dan ALLAH saboda wani nazari dana zauna nayi.” batare da

ya jira cewarsa ba ya cigaba da faɗin. “Ni da ku duk munsan waye Ramadhan da kuma kammu, amma jama’ar gari da Ramadhan ke mulka har yanzu basu gama sanin

waye shi ba. Auren Ramadhan da yarinyar nan Ameenatu dududu watanni na bakwai muke a ciki yanzu, ko shekara bamuyiba. Aurene da yasha soke-soke da kace nace

a idanun mutane da bakunansu dalilin tazarar da su suke hange da mu babu ita a zukatanmu. Shin ya kuke tunani idan akace yanzu an fiddo maganar ƙara auren

Ramadhan wa duniya, kuma da ɗiya irinsa mai irin matsayinsa kuma ƴar uwarsa sannan mai dukkan kishiyar abinda akai cece kuce Ameenatu bata da shi a baya?.

Dama ance munyi haɗin auren Ameenatune da Ramadhan saboda mu gyara masa siyasarsa ace yana son talaka gashi harya auri ɗiyar cikinsu. To yanzu wannan auren

nasa da har yanzu bamu gama sanin kansaba ake masa shiri na tashin hankali bama tunanin cikkakkiyar amsace ga ƴan ƙasa da abokan hamayya?. Ba ina fargar

damu bane dan tunanin kar Ramadhan ya rasa kujera a zaɓe nagaba. Ina fargar damune domun kare mutuncin kammu dana Ameenatu yarinyar kirki da batajiba bata

ganiba, hakama ina kare kunyar da zamu daurama bayin ALLAH da suka goya da bayanmu suka kuma tabbatar da tsarkake abinda mukayin badan sakamakon mu a

hanunsu yake ba, sai dan bana son mu cire hope ɗin mutane akan mulkin Ramadhan. A yanzu Su’adah tazomin da wannan invitation card ɗin” ya ajiye iv ɗin gaban

Bappi. “Bappah ka dubafa ka gani, events kusan goma ne anan aka shirya wanda ake fatan duniya ta gani ta shaida za’ama Ramadhan auren gata bama ƙasar NAYA

kaɗai ba. Bayan kuma mu a wannan gidan duk bama hakan tun auren ƴaƴanmu na farko, sannan ko’a yanzun ma bawai shine kaɗai auren da za’a ɗaura ɗin ba”.
       Tsitt falon yay bayan Pa yayi shiru. Sai dai tsananin ɓacin rai ya bayyana ga fiskokinsu bayan duk sun ga katin da tarin bidi’oin dake a ciki. Anne

da idanunta suka fara cika da ƙwalla tace, “Anya kuwa Ramadhan ma yana cikin hayyacinsa? Bana son zargi sam a rayuwata ballema dana san dai Su’adah

mahaifiyarsa ce babu yanda za’ai ta cutar da shi….”
      Murmushi Pa yayi, cikin kunar rai yace, “Idan ita bata cutar da shi ba ai anyi amfani da ita da son zuciyarta an cutar da shi Anne. Bara yau na fito

na sanar muku gaskiyar lamari akwai sihiri tattare da Ramadhan, sam abinda yakeyi ba’a cikin hankalinsa yakeba..”
        Salllami falon ya ɗauka da sautin kukan su Yafendo. Yayinda Bappi ya tsurama ɗan nasa ido duk da shima ya jima yana wannan zargin. Pa yaja numfashi

mai cike da takaici. “Karku wani damu kanku ni hakan yamun daɗi ai, maybe a dalilinsa Su’adah zata dawo cikin hankalinta tasan abinda ke mata ciwo. Na jima

da fahimtar hakan amma bana son kowa ya nemawa Ramadhan magani dan ALLAH har sai anzo gaɓar daya dace…”
        Da sauri Inna ta katse Pa, “Baka da hankali Bashari. Taya za’abar yaro a baƙar inuwar sihiri? Kenanfa kusan duk abinda yakeyi baima san yanai ba!

Kai nifa ina mamakin canjawar yaron nan lokaci guda. Har takai yanzu zaizo gidan nan amma bamu sani ba. Barinsa cikin wannan tashin hankalin ai matsalane,

sai ya iya shafar mulkin da yake kai ko kai baka san hakaba”.
     Karon farko Bappi ya saki murmushi, cikin takaici yace, “Sadiya kenan wannan na nawa kuma. Badan ALLAH ya bashi chief of staffs na ƙwarai mai amana da

tsoron ALLAH ba ai da tuni halin da Ramadhan ke ciki ya bayyana a cikin mulkin nasa. ALLAH dai ya ƙyauta. Ni yanzu inaga kai Basheer faɗi dalilinka muji,

idan mai yuwuwane saimu riƙe. Idan bazai yuwuba a sake shawara”.
      Kai Pa ya jinjina masa. “Bappi abinda yasa na roƙeku kar’a nema masa magani saboda dalilai uku ne zuwa biyu. Na farko ina son Su’adah ta gane

kuskurenta akan Ameenatu, na biyu ina son ta gane wacece ƴar uwarta Asma’u. Na ƙarahen da bakinta nake son ta bayyana dana saninta a kansa. Dan haka ina

roƙonku yin wannan aure a sirrance. A ɗaurashi a sirrance iya wakilansa da wakilan yarinyar. Akuma hana kowanne biki da suka shirya da an ɗaura aure ya

dauka matarsa su wuce kawai, sauran dokokina a kansa sai bayan ɗaurin auren ne”.
     Shiru falon yayi kowa na nazari, bayan shuɗewar wasu mintuna Bappi ya fara jinjina kansa alamar gamsuwa. “Kamar hakan duk yayi gaskiya. Sai dai Jannatu

mi kuke gani ku?”.
       Anne dake ta danne kukan dake taso mata ta haɗiye da ƙyar. “Dattijo hukuncinka ai namune. ALLAH yasa haka shine mafi alkairi”.
    Da amin duk suka amsa. Daga haka suka cigaba da tattauna abinda ya dace…………✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button