BAKAR INUWA 61-62
Episode. 61-62
………..Wani irin tsargawa kanta yay ganin Ramadhan shimfiɗe a ƙasa Bappi ya toshe masa baki, ga Pa a kansa yana karatun suratul baqara. Tuni jikinta ya
fara rawa. Ta matsa da sasaarfa takai duke gabansa cikin rufewar idon manta waɗanda suke a falon. “Ya ALLAHU na shiga uku ni Raudha Ya Ramadhan mike faruwa
da kai haka?”.
“Kinga Ameenatu yi hakuri baya cikin hayyacinsa yi masa karatun kawai”.
Ai Bappi baima kai karshe ba ta fara karatun itama cikin suratul baqaran. Wata muguwar zabura ya kara yunkurowa zaiyi saboda masu karatun sun zama biyu,
ga zazzaƙar murya da ALLAH ya azurta Raudha da ita inhar tana karatu komai taurin zuciyarka saika nutsu a saurare. Tun sunayi yana fisge-fisge har ya fara
lafawa a hankali. “Idan ma mu an koremu ai akwai wanda suke tare da shi tun yana yaro”.
Bakin Ramadhan ɗin ya faɗa a kausashe, amma a tabbaci bashi bane sai kuma ya fara sakin tari mai ƙarfi. Raudha da Pa basu dakataba suka cigaba da
karatunsu sudai. Yayinda Anne ke duke gabansa tana rike da kansa ita da Bappi. Tsahon mintuna talatin suka sake kwashewa suna karatun kafin jikinsa yayi
laƙwas. Duk da hakan Raudha bata dakata ba har sai da takai karshen suratul baqara lokacin agogo ke nuna karfe ɗaya da wasu mintuna na dare.
Ta matuƙar birgesu, sun sake jin kaunarta mai tsanani da taya gudanjininsu murnar samunta matsayin mata uwar ƴaƴansa. Bayan ta rufe da addu’a suka
shiga sanya mata albarka. Ita dai kanta a ƙasa tana sharar hawaye. babban burinta tasan miya kawo mijinta gidan a wannan halin? Yama akai yazo? Miya faru da
shi?. Waɗan nan sune jerarrun tambayoyin dake mata yawo bisa kai. Sai dai ta kasa furtasu ga kowa.
Anne da tasan lokacin barcin Raudhan ya gota cikin sanyin murya tace, “Ameenatu kije ki kwanta kinga kema fama kike da jikinki. Tunda Alhmdllhi da
alama komai ya dai-daita barci ne ya ɗaukesa. Kamar Raudha zatace a’a sai kuma tay yunkurin mikewa domin bin umarnin Anne. Caraf taji an ruƙo mata hannu,
bama ita kaɗai ba kowa a ɗakin sai da ya kalli hanun Ramadhan ɗin, kafin ya firta. “Ameenatu ruwa! Bani ruwa na sha inajin ƙishi”.
A hankali yake maganar amma hakan bai hanasu jinsa ba. Raudha duk kunya ta isheta. Amma saita daure ta dauka goran ruwan dake kusa da Anne, a sanyaye
tace, “Ga ruwan to buɗe idonka”.
Bakinsa kawai ya buɗe mata yana ɗan girgiza kansa, kamar zata sake magana sai kuma Bappi ya dakatar da ita ta hanyar ɗago kan Ramadhan ɗin yanda zata
iya zuba masa ruwan batare da ya cutar da shi ba. Duk da kunyar da takeji haka ta daure ta ɗora masa gorar a baki. Sai ko gashi yana zuƙarsa da yawa harya
shanye. A hankali ta janye goran shi kuma ya ɗan buɗe idanunsa yana kallonta. “ALLAH yayi miki albarka”. Ya faɗa a hankali tare da maida idanunsa ya lumshe.
Kusan atare duk suka amsa da amin tare da sauke ajiyar zuciya. banda Raudha datai kasa da kanta ta amsa a kan laɓɓa. Bappi ne ya basu umarnin zuwa su
kwanta, shi kuma zai kwana da Ramadhan ɗin sugani ko zuwa asuba zai dawo hayyacinsa su samu ya koma can government house kafin a farga. Dan sun tabbatar
fitar ɓadda kamar daya sabayice yayo yau ɗin ma.
Badan Raudha taso ba ta mike. Koda suka isa ɗaki Anne wanka ta sakatayi, ta bata tea tasha kamar yanda ta saba turketa a duk dare kafin ta sakata
kwanciyar dole. Sai dai ta lumshe idanune kawai badan barcin ba. Amma ita kanta tasan idan tace zatai barci a irin wannan halin yaudarar kanta zatai
kawai…
A ɓangaren su gimbiya Su’adah kam kowa tunda baiga Ramadhan ba sai hankalinsa ya karkata akan Addah Asma’a da suka samu a kasa wanwar. Ruwa aka bata
tasha, aka kuma dagata zuwa kujera sannan suka shiga mata sannu. Bayan numfashinta yaɗan daidaita Gambiya Su’adah ta sallemsu su duka falon ya rage daga ita
sai Adda Asmah da Aynah.
“Adda inaga kuje gida zanzo da safe na sameku, dan zamanku yanzu anan akwai matsala zai iya fargar da jama’ar gidan wani abu. Su kuma ku barni dasu
game da Ramadhan zanma tufƙar hanci”.
Addah Asmah da ba fahimtar komai takeba a yanzu gudun kar gimbiya Su’adah ta ɗagota ta jinjina mata kai ko maganin da suka kawo ɗin bata samu bata ba
suka fice cikin taraddadin da ƙaulani. Numfashi gimbiya Su’adah saukewa, kafin ta nufi sashen su Anne. Sai dai tana tu karowa taji sautin karatun Raudha da
Pa. Wani irin kunci da duhu zuciyarta ta sake shiga najin tsantsar tsanar Raudha da batasan yaya akai tazo gidanba ya riketa. Tunanin ko dama tare da
Ramadhan sukazo ya sata juyawa ta fasa shiga baki ɗaya ta koma sashenta tana haɗiyar zuciyarta data cika kirjinta fam kamar zata fashe.
★★★_★★_★
Da asubar fari Bappi ya fita raka Ramadhan government house, kamar yanda ya fita ta barauniyar hanya yanzun ma tanan yabi da taimakon odilan
nashi da shi kaɗai dama yasan da fitar. Tunda yaga bai dawo akan lokaci ba hankalinsa yake a tashe. Shi kansa yasan irin waɗannan fitar da shugaban ƙasar
keyi akwai haɗari a cikinta. Sai dai shi ko’a jikinsa. Ko’an nuna masa illar fitar ɓadda kamar baya nuna damuwa ko hango wata matsala. Amma har cikin rai
odilan ɗin nasa na tsoron randa wani zai farga a cikin gidan ko waje.
A taura house kam koda aka wayi gari babu wanda ya tada zancen. Musamman daga sashen Anne. Ita kanta gimbiya Su’adah tana son ma Pa magana tanajin
tsoron a yanda ya tashi yau fuska kamar hadarin gabas. Amma har cikin rai tana buƙatar jin halin da yaronta ke ciki. Ta kira wayarsa amma ba’a ɗaga ba, ta
rasa inda zata tsoma ranta ta huta har baƙi dai suka fara isowa irin su Safina da tawagar ƴaƴanta. Sai daga masarautar Bina kuma.
Zuwa Azhar gidan ya fara ɗaukar baƙi sosai. Hakan ne ya tilasta Gimbiya Su’adah fasa fita gidan Addah Asmah dan tun jiya da suka bar gidan bataji daga
garesu ba. Ta kira duk wayoyinsu a kashe. Ta aika Muneera ta dawo ta sanar mata Aynah da Addah basa gida wai tun safe suka fita baƙi ma daketa isowa babu
wanda ya samesu a gidan sai ma’aitan gidan keta saukesu. Wannan zance ya sake tada hankalin gimbiya Su’adah matuƙa dan haka ta kira fulani da suke shirin
tahowa da yamma ta sanar mata. Duk da fulani tasan komai sai ta ɓoye mata akan ta kwantar da hankalinta zata bincika. Amma tasan Addah Asmahn bazataje wani
waje ba daban. A sanyaye tace to.
Fulani ta sauke wayar tana taɓe baki. Dan yanzu sun ƙudiri aniyar daina faɗa gimbiya Su’adah komai akan shirinsu. A ganinsu sakacintane ya lalata
komai a daren jiya kokuma akwai abinda take son gujemawa. Itako fulani burinta da alwashinta sai ta nunama Anne ba itace kaɗai keda iko da Ramadhan ba,
yayinda Addah Asmah ke nuna itama shine burin nata. Sai dai acan kasan rai ba haka bane. Baƙar hassadar ƴar uwartace kawai ke cinta akan ta fita komai na
rayuwa. A ganinta mallakar Ramadhan matsayin mijin ƴarta, zaisa abinda Gimbiya Su’adah ke takama da tinƙaho da shi ya dawo tafin hanunta ƙarƙashin ikonta.
Faruwar komai a jiya yasa Aynah kwana kuka akan bazata iya haƙuri da Ramadhan ba a yanzu. Ita duk ma yanda za’ai ayi ƙoƙarin gyara matsalar nan da