JIDDATUL KHAIR

JIDDATUL KHAIR 46

Ad

_____

Bayan kwanaki kadan da Umma tayi magana da Ahmad sai gashi ranan wata Asabar ya shigo gida rike da admission form na Jiddah da receipt na kudin makarantar, Umma ta gama duba takardan da ya mika mata tsaf sannan ta kallesa tace “Ba nace maka makarantar yayi nisa ba Ahmad?” Yace “Umma kece fa kike ganin da Nisa amma ba wani nisa, sannan kan hanya ne ai…” Umma tace “Toh yanxu biya mana kudin makarantar kayi?” Yayi dariya yace “Ehh tawa gudunmawar kenan” Umma tace “Toh Allah yayi albarka,

mun gode” Yace “Ameeen” Tace “Ina Ramlah?” Yace “Na ajiyeta gidan Captain” Umma tace “Ohk, yana nan kenan” Ahmad yace “Ehh yana gari, jiya ya shigo” Tace “Toh madallah” Ahmad yace “Xuwa monday sai a kaita schl din for documentation, in sha Allah hopefully xa su saka ta ss1, kinga in dai ya kara maida hankali a ss2 kawai sai tayi waec dinta” Umma tace “Toh Allah ya kai mu, da kana gari ne sai ku je tare ai” Yace “Ina nan har Tuesday” Umma tace “Toh shkkn sai ku je tare din xai fi” Yace “Allah ya kai mu” Daga

[indeed-social-locker sm_list=’fb’ sm_template=’ism_template_9′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’true’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=2 locker_template=8 sm_d_text=’

This content is locked

Share This Page To Unlock The Content!

‘ enable_timeout_lk=1 sm_timeout_locker=1200 reset_locker=1 locker_reset_after=1 locker_reset_type=’days’ ism_overlock=’default’ ]

haka ya nufi kofa ya fita. Karfe biyu Maimoon da Jiddah suka shigo gidan daga saloon sun je kitso, Umma ce xaune parlor tare da Hajja da ta yafa uban mayafi ga jakarta a gefe, daga ganinta kasan bata jima da shigowa ba, A tare Jiddah da Maimoon suka gaisheta, Hajja tace “Har anyi kitson?” Maimoon tace “Ehh” Hajja ta kalli Umma tace “Toh kince sai yamma xa su dawo kuma gasu ko minti ashirin ba ayi da shigowata ba sun dawo” Maimoon da Jiddah dai suka wuce dakinsu, Umma ta ajiye wayarta da take

dannawa tace “Dama ba ce maki nayi in dai da layi saloon din xa su iya kai wa har yamma ba? Idan kuma babu layi xa su dawo da wuri? Haka fa muka yi dake Hajja” Hajja tace “Atoh A masar dai magana daya ake, ko don baki son ta rakani ne kika fadi hakan wa ya sani, ni fa nan da kike gani na Allah ne ke daura min son mutum ba wani mahaluki ba, ga can gantalalliyar can Nafeesah me yasa bance ta rakani ba? kice saboda bata gaisheni, sannan wannan bakar yarinyar Aisha sace sace take min a daki, komai aka kawo ta wawura ta boye, shi yasa bata da fasali wllh, to ni ba ruwana ta kaina nake bana biye su, yau dai ina tashi da sassafe nace ma Usman tunda wannan yaro Aliyu yayi aure muka kai masa amarya ban sake komawa gidan ba, kuma ko yanka ni xa ayi idan na hadu da amaryar a hanya yanxu dai ba ganeta xanyi ba wllh,

Ad

Usman ya fahimceni yace in shirya in je to, barin ma yau Asabar yana gari yana hutu, to ni a gaskiya bana son tafiya ni daya kamar mayya, shine nace kawai direba ya kawoni nan in samu wannan yarinya Jiddah ta rakani muje, ita dama yar ki Maimuna tun wani fada da nayi mata ta daina gaisheni sai yau da taga idonki, banda jiddar babu me mun biyayya yanxu wllh tllh” Umma dai ci gaba da danna wayarta tayi kawai, Jin

Hajja tayi shiru tace “Banda abunki Hajja ai jiya juma’ah da babu Islamiyya ya kamata ki xo ba yau da xa su tafi Islamiyya ba” Hajja tace “Toh yau Allah ya bani ikon bude baki ince xan je gidan amarya, ke fa Ramlah wani lokacin Sai in rasa gane inda kika dosa, sannan ni Usman bai wani ce in xo in nemi izininki in tafi da yarinya ba, kawai cewa yayi direba ya kaini in dauketa mu tafi, ni fa ba tsohuwar banxa bace Ramlah, banda tsautsayi babu abinda xai dawo dani daga Masar wllh, a can banda ganin girmana da mutuntani babu abinda larabawa ke yi, don dai Nafisah ta tafi gun mijinta a Habuja ne da ta baki labari da kanta, amma ku banda raini babu abinda ke tsakaninku da babba a kasar nan” Umma tace “Yanxu dai Hajja ga ki ga Jiddah, ni bance kar ki tafi da ita ba, maganan Islamiyya nake, malaman basu yarda da fashi ba” Hajja ta kundumo wani xagi tace “Su malaman Allah ne su da sai ace lallai sai abinda suka gindaya xa a bi? Ni

me iya xuwa makarantar ce yanxu ince masu Jiddah baxata je ba sbda wani uzuri da ya taso” Umma tace “Toh rana dai na yi, sai ku tashi ku tafi” Hajja tace “Xuwa xa kiyi ki sanar mata ni ba ruwana duk an ma bata min rai, kamar warce xanje in siyar da Jiddar, ni da na sani ma ban yadda na dawo kasar nan ba wllh, yaushe xa a ga haka a Masar” Umma tace “Wannan Masar din dai Allah ya kai mu muga yanda ake yi a can din Hajja” Da sauri Hajja tace “Aa, ba ko wani gantallale ake bari ya shiga kasar ba ma, nima da yaya suka yarje min na shiga, ke dai kawai a bar kaza cikin gashinta” Dariya Umma tayi ta mike ta wuce dakinsu

Maimoon, har sun fara shirin Islamiyya, Umma na kallon Jiddah da har ta saka uniform tace “Jiddah xaki raka Hajja gidan amarya wai” Jiddah tayi shiru tana kallon Umma tana son sanin wace amaryar tukun, Maimoon tace “Wace Amaryar Umma?” Umma ta ta6e baki tace “Gidan Aliyu wai” Sosai gaban Jiddah ya fadi, lkci daya mood dinta ya canxa har hakan bai boyu a fuskarta ba, Umma duk ta lura da hakan kuma, Umma tace “Kina kai ta dama xan baki kudin mota ki lallaba ki dawo, ko minti ashirin kar kiyi a gidan” A sanyaye Jiddah tace “Umma Islamiyyar fa?” Umma tace “To na gaya mata ta hau ni da fada, kawai kiyi hakuri ki rakata din, kuna isa gidan ki juyo abun ki” Jiddah tace “Toh Umma mu je da Maimoon idan ya so kawai sai mu wuce makarantar daga can” Umma tace “Ehh kuma haka ne, ku shirya ku fito, hakan ma

Ad

_____

1 2 3 4 5Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button