BAKAR INUWA 61-62
suka tabbatar komai ya watse. Wannan shine dalilinsu na tafiya gidan boka bayan tun dare sun kirashi yanata faɗa akan abinda tunkan su sanar masa yace musu
ya sani tunda aljanin daya turama Ramadhan yaci ubansa hanun Raudha da Pa da ayar ALLAH. Tun tafiyar da sukai da asubahin nan suna can har yanzu anata sake
tsumo Aynah da shaiɗanci kala-kala akan Ramadhan kawai….
To bara muga wazaiyi winning anan kuma????????????.
_________________
Ƙarfe biyar na yamma dai-dai tawagar shugaban ƙasa Ramadhan ta iso Taura house bisa rakkiyar jami’an tsaro da wasu na jikinsa. Kamar wancan
hutun tako ina anguwar ta zama ƙarƙashin mulkin mallakar jami’an tsaro ne. Sauƙin ma dama can anguwar manyace bawai hayaniya ko yawan shigi da fici ake samu
ba. Sai dai abin ya shafi masu tururuwar zuwa biki. Dan duk waɗanda suka iso yau dasunci karo da jami’an tsaron nan sai tsoro ya kamasu duk da sunsan yanzu
Taura house yana da wani sabon girma bayan wanda kowa yasan gidan da shi.
Babu wanda yaga Ramadhan, domin motar da yake ciki har jikin ƙofar falon Bappi ta baya aka kaita, yana fita kuma ya shige ciki abinsa.
Raudha na bedroom ɗin Anne kwance ta gama ƙwallar shan kunu da Annen ta tsareta tayi Bilkisu ta shigo ɗakin da sallama. Wayar ta dake hanunta tana
game ta ajiye, dan dama game ɗin kawai takeyi amma hankalinta naga mijinta da tunanin miyake ciki yanzun? Yana ina? Jikinsa da sauƙi ko babu?.
“Sai a daina mana shagwaɓa ga boss nan ya iso”. Bilkisu daba sanin abinda ya faru da Ramadhan ɗin tai jiya ba ta faɗa tana dariya bayan takai zaune
kusa da Raudha. Murmushi kawai Raudha tayi da faɗin, “Kai aunty ni shagwaɓar mi nayi?”.
“Ai ba abun jayayya bane bara na lissafa miki yanzu kuwa ɗaya bayan ɗaya ta Brothe……”
Ta kasa karasawa saboda wanda ya shigo ɗakin. Da farko tsoro taji sosai ita kanta Bilkisun, sai dai yanda taga yanayinsa kamar a sanyaye ya sata ɗan
sassautawa ta gaisheshi zata mike. Sai dai Raudha tai saurin riƙo hanunta idanunta na cika da ƙwalla. Sosai yanzu tsoronsa takeji, tsoro mai tsanani dan ita
kaɗai tasan azabar da taci a hanunsa har sau biyu da bazata taɓa iya mantawa ba.
Raunanannun idanunsa ya sauke akan hannayen da Raudhan ta sarƙe. Sai yaji wani irin tausayinta mai tsanani yana dirar masa daga tsakkiyar kai har
tafin kafa. Da ido yayma Bilkisu alamar ta fita. Dan haka tai saurin son zame hanunta cikin dabara tana faɗin, “Aunty Raudha bara na dawo tanan sai Yaya ya
zauna nan”.
Sam Raudha bata yarda ba, saita ƙara ƙwaɓe fuska zatai kuka. Bilkisu da ita kanta tausayinta takeji tunda batasan ko yayan nasu bai dawo cikin
hankalinsaba har yanzu ta zame hanunta ta gudu. Sosai jikin Raudha ya fara rawa ganin ya maida ƙofar ya kulle harda key. Babu shiri ta miƙe a kan gadon tana
ƙoƙarin sakkowa. Sosai tayi ƙiba, tako’ina komai yayi zam, damma doguwar rigar jallabiyace a jikin nata baƙa. A hankali ya lumshe idanunsa tare da harɗe
hannayensa duka a ƙirjinsa, sai kuma ya sake buɗesu ya zuba mata. Yanda take rawar jiki yasa ko’ina nata ke motsawa, ga rigar mai santsi ce, sai hakan ya
ƙara taimakawa wajen motsawar jikin nata.
Murmushin takaici da tausayin kansu ya saki. Baiga laifinta ba, dan yasan dolene taji irin wannan tsoron nasa. Ya ɗan furzar na numfashi tare da
warware hannayensa daga ƙirji ya fara takowa gareta cike da nutsuwarsa da kasalar yanayin rashin jin daɗi da yake a ciki……..✍