BAKAR INUWA 69-70

tunaninsa kenan sai dai babu mai bada gamsashiyyar amsa akai zaman jiran isowarsu.
★Kusan awa guda suna zaman jira dan sai da Pa yay jan ido suka yadda suka taho dalilin ita gimbiya Su’adah na tsoron nata mijin, itako Adda Asmah
ta raina nata. Wujiga-wijiga suka shigo musamman gimbiya Su’adah da sai da Safina ta bata taimakon gaggawa acan amma da yanzu labarin ba wannan ake ba kuma.
Kowa hankalinsa ya tashi da yanayin nasu, musamman ma Ramadhan da cikin rawar jiki yaje ya taya Safina riƙo Maah dake tafiya kamar zata zube ƙasa sai hakki
take sama-sama. Shidai Bappi uffan baiceba, binsu kawai yake da kallo hakama mai-martaba. Pa kuwa yanayinsa na nuna ko’a jikinsa dan dama irin wannan ranar
yake addu’ar tazo duk da bai san mike faruwa ba shima har yanzun.
“Inaga muyi abinda ya taramu kamar zaifi”.
Cewar Pa da alamun ɗaci a muryarsa. Bappi zaiyi magana Mai-martaba ya katsesa.
“Gaskiya Basheer ya faɗa dan nima sonake na wuce akan lokaci”.
Bappi ya haɗiye abinda yay niyyar faɗa kawai yana girgiza kansa. Daga haka aka buɗe taro da addu’a sannan aka fara abinda ya tara ɗin game da sauya
maganar auren Ramadhan da Aynah.
Bayan dawowar Ramadhan hayyacinsa, adare ranar Bappi ya sanar masa duk abinda ake ciki, amma sai ya dage akan shi bai taɓa jin son wata Ayna’u ba.
Bakuma zai fara a yanzu ba bayan so na ƴan uwantaka dake tsakaninsu. Ya kuma tabbatar masa komi za’ai shi bazai aureta ba matarsa ta ishesa. Babu irin
lallashin da Bappi bai masaba a wannan dare amma yace shifa yana akan bakansa.
Washe gari ma daya dawo gidan kafin yaje ga Raudha maganar da suka fara tattaunawa da Pa da Bappi da Anne harma da su Yafendo da Mai-martaba a waya
kenan amma Ramadhan yace yana kan bakansa. Baice zai auri Ayna’u ba kuma ayanzu bazai amsa ba. Dagiyarsa ya sake tabbatar musu akwai sihiri tattare da shi
sanda ya dinga musu hauka akan auren Ayna’u garda ɓatawa da su Anne. Wannan dalilin ya sakasu sallamarsa suka tattauna abinda ya dace a tsakaninsu. Mahaifin
Aynah shine ya kawo shawarar a rufe komai iya su ranar ɗaurin aure yanada wanda zai aurama Aynah dan a raba gardama komai ya zama ƙarshe basai anta jan
zancen ba. Wannan shawara tama kowa, dan haka suka rufe komai hatta Ramadhan baisan da haka ba sai da aka ɗaura aure da wani daban ba shi ɗin ba.
“ALLAH na gode maka da hakanma ta kasance, Ramadhan ka yafemin, duk halin daka shiga akan Ayna’u hardani a ciki, daban basu goyon bayaba da ba’a
nema sabautamin rayuwarka har gashi yau ana iƙirarin kashemin kai ba…”
Gimbiya Su’adah ta faɗa cikin kuka hanunta riƙe dana Ramadhan. Tsitt falon yay cikin rashin fahimtar kalaman nata……….✍