JIDDATUL KHAIR

JIDDATUL KHAIR 48

Ad

_____

Har Jiddah ta isa bakin titi waigen layin take xuciyarta na bugawa, tana ta tsaye har ta samu adaidaita ta hau ta gaya masa inda xai kai ta, dai dai kofar gidan Umma mai adaidaita sahun yayi parking ta sauka ta ciro kudin da Umma ta bata jiya a jaka ta mika masa, ya bata canji sannan ta shiga cikin gidan… Babu kowa parlon don su Maimoon sun tafi Islamiyya, ta karasa kitchen don gaida Huraira dake aiki a ciki,

Huraira tace “Dama Umma tace sai yau xaki dawo da aka ji shiru har dare jiya” Jiddah ta d’an yi murmushi kawai tace “Umma bata tashi ba?” Huraira tace “Bata tashi ba ko” Juyawa Jiddah tayi ta wuce dakinsu, sai da ta fara shiga bandaki ta wanke baki tayi wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga bayan ta gama shafe shafenta sannan ta kwanta, da ta runtse ido abinda Abuturrab yayi mata kawai take gani, tana ganin

[indeed-social-locker sm_list=’fb’ sm_template=’ism_template_9′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’true’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=2 locker_template=8 sm_d_text=’

This content is locked

Share This Page To Unlock The Content!

‘ enable_timeout_lk=1 sm_timeout_locker=1200 reset_locker=1 locker_reset_after=1 locker_reset_type=’days’ ism_overlock=’default’ ]

hakan kuma sai gabanta ya fadi, ita har yanxu ganin lamarin take kamar a mafarki, da yake bata wani samu baccin kirki daren jiya ba nan da nan bacci me nauyi ya dauketa. Karfe sha daya saura Umma ta fito daga dakinta ta dalilin kiranta da Huraira taje tayi wai tayi bakuwa, Tsaye taga Hajja a parlon sai hura hanci take, Umma ta karaso tana kallonta tace “Lafiya Hajja?? sannun da xuwa” Hajja ta dakatar da ita tayi mici mici da ido tace “Jiddah ta dawo??” Umma ta kalli Huraira dake bayan kujera a tsaye, Huraira tace “Ehh ta dawo tun daxu amma tana daki tana bacci” Umma ta kalli Hajja, Hajja ta rushe da kuka ta nemi kujera ta xauna tace “Toh a gaskiya Allah ya isa, wannan daga min hankali da tayi taje don kanta, idan

kuma ke kika koya mata hakan kema kije don kanki… Kuma ni ban san haka take ba da ban fara xura jiki ina kulata tun farko ba, ashe su Maimu da Aisha kananun yan iska ne a inda wannan yarinya jiddah take

Ad

ban sani ba?? Amma ba komai nasan duk karatunki ne ta dauka ba wani abu ba” tana fadin haka ta fyace hanci, Umma da ranta ya gama baci tace “Kawai sai in xaunar da ita don rashin aikin yi ince ta baro gidan da ku ka je da sassafe ko Hajja??” A fusace Hajja tace “Oho… Xaki aika wllh, waye bai sanki da halinki ba? dama kuma da ya kika bari ta bini, bai sai da na hadaki Allah… annabi ba?? ni dai ai na gode Allah da ta dawo gida lafiya abu bai sameta a hanya ba balle hukuma su garkameni ko jikana, wai kawai ina farkawa daga bacci barawon da ya sace ni da asuba sai naga daki wayam babu mata babu dalilinta, ban kawo komai a rai ba ina ta jan carbi har kusan karfe tara, nace kai bari dai in sauka in duba ko kumallo take

nema mana a kitchen, ina sauka naga gidan wayam babu ita babu isilinta, na duba inda takalmanmu suke naga ai babu nata sai nawo kwallin kwal kamar maye, da gudu na koma sama na taso wancan mutumi Aliyu shi ma dai ya fito muka yi ta bulayin neman yarinya a cikin gidan, banda kuka da rokon Allah ya taimakeni babu abinda nake a lkcn, daga karshe ya bada shawaran mu taho nan kilan ta dawo, shine fa na taho ko wanka banyi ba yanxu haka, abinda ban ta6a yi ba a Masar, gudun fitinarki ma gashi can yaki

shigowa yana can xaune cikin mota, to yana da gaskiya mana tunda bai san ko yarinyar ta dawo ko bata dawo ba, daga ni har shi sai ki iya sa a garkame mu kadan da aikin ki” Umma ta kalli Huraira tace “Kira min Jiddah” Huraira ta tafi daki, a durkushe taga Jiddah ta daura kanta saman gado idonta lumshe, baccin ma gaba daya ba me dadi tayi ba banda mafarkan Abuturrab babu abinda take, ga ciwon ciki da ya matsa mata, Huraira tace “Lafiya Jiddah” Da sauri ta bude idonta sai kuma ta dago kanta daga saman gadon ta nuna mata cikinta alamar yana mata ciwo, Huraira tace “Subhanallah sannu kinji, xaki iya fitowa kuwa,

Umma na kiranki” Jiddah ta daure ta mike ta dau hularta ta saka sannan ta fito parlor, wani kallo Hajja ta dinga mata daga sama har kasa, Jiddah ta kasa kallonta ta karaso parlon ta durkusa, a hankali tace “Ina kwana Umma” Umma tace “Lafiya lau, why did u leave without telling anyone?” Jiddah ta girgixa mata kai kawai bata ce komai ba, Umma tace “Ki bude baki kiyi min magana” a hankali tace “Umma cikina ke min ciwo” Hajja tace “Kaji sharri?? Dama ba gari muke jira ya waye a kai ki asibiti ba? in ni kina tunanin

tsohuwar banxa ce don me baki sanar ma me gidan cewar xaki koma gidanku ba xaki tafi ki bar xuciyoyin mu a gantale da fargaba??” Umma tace “To ayi hakuri Hajja, Allah ya huci xuciyarki” Hajja tace “Aa bbu ruwana wllh, sai kinga tijaran da nayi ma matar gidan a kanta jiya, shine ni xata watsa min kasa a ido?”

Umma da mitan ya fara isarta tace “Toh ke yanxu ya kike son ayi Hajja? Komawa gidan xa kiyi tare da ita yanxu?” Jiddah da taji gabanta yayi wani irin faduwa ta fashe da kuka ba tare da ta shirya ba tace “Wllh cikina ciwo yake min Umma” Hajja ta rike ha6a tana kallon Umma tace “In koma ina da ita? Matar da ta

kashe mana baccin jiya duk a xaxxaune muka kwana a gidan kamar almajirai, aa tunda ta dawo gida lafiya Alhmdlhi, nima xuwa xanyi ya ajiyeni a gida ashe matar gidan yaji tayi daga jin mun xo, to ni ina na sani, sai yau da safe yake gaya min” Umma dai tace “To Allah ya kyauta, kiyi hakuri Hajja” Hajja ta juya ta nufi kofa tace “D’an ba kara, tunda dai ta dawo xan turo Aliyun ya shigo ya gaisheki mu san inda dare ya

Ad

_____

1 2 3Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button