Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 75

ALLAH ka shiga tsakaninmu da maƙiyanmu????????????.

       Take a wajen ma ALLAH yay ma Inna Rasuwa, dan sai gawarta aka nufi asibiti da ita. Driver da Muneera ne kawai ke numfashi. Shima driver ko mintuna biyar basu cikaba ya rasu.
    Karaɗewar labarin wannan hari da aka kaima Alhaji Hameed Taura cikin kanƙanin lokaci yasa ko zama basuyi a gidan Adda Asmah dake a mawuyacin hali itama suka taho. Hakama Raudha da Ramadhan da su Aunty Zuhrah duk sun rikice a government house. Dan kuwa babu abinda kake gani a yanzu akowane gidan tv sai harin da aka kaiwa Alhaji Hameed Taura. Amma abinda yaba mutane mamaki kamar yanda yan jarida ke faman shelantawa babu shi a motar duk da kuma daga government house kowa yaga motar ya shiga har shugaban ƙasa yay masa rakiya.
     Zamu iya cewa a wannan dare gaba ɗaya NAYA a hargitse ta kasance. Dan ba’a samu damar bizne gawar Inna ba saboda jami’an tsaro sun rike. Kuka Raudha take tana sambatu da ambaton “Su din azzalumai ne. Dama sun ce sai sun kashemu, miyay musu, mi kai musu kaima mijina?. Na tsanesu, da ace sun samu nasara kan Bappi yau da kaina zan kashesu, amma ko yanzu karka ƙyalesu Ya Ramadhan. Na rokeka karka barsu suma su dukansu”.
     Kalaman Raudha sun girgiza Ramadhan, dan haka ya tsareta ta sanar masa suwaye? Mita sani? Mi take boye musu. Shi tun sanda ta karema Bappi hari ya tabbatar tasan wani abu.
     Cikin kuka ta shiga girgiza masa kanta. “Wlhy bansan komai a sannanba Ya Ramadhan, sannan bansan su wanene ba. Nayi hakane saboda shima ya taimaki wani tsohon daya fisa shekaru a filin idi. Amma badan na sanshi ba. Badan nasan komai daga garesaba. Sai dai zan faɗa maka abinda na sani nima, amma wlhy ka yarda dani, ban yarda da aurenka saboda su ba. Nayine kawai dan yima mahaifina biyayya da gujema mahaifiyata tsinuwa da Gwaggo tace zatai mata inhar ban yarda da aurenka ba………..”✍

[/indeed-social-locker]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button