Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 76

       Daga Hutawa Bina suka nufa cikin masarauta. To anan dai kam daga mai-martaba ta samu tarba ta ƙwarai. Fulani ce dai kadaran kadahan. Dan ko Abdull ƙin cewa a bata tai sai da Aunty Zuhrah ta ɗauka da kanta ta bata tace a sanya masa albarka. Sai kuma duk taji kunya. Mai-martaba kam acan suka baro masa Abdull, ba’a dawo musu dashi ba sai da ya fara ƙananun kukan yunwa.


     Anan ɗin ma dai shatara ta arziƙi mai-martaba da sauran matan sarki suka bama Raudha dan Ramadhan yana girmamasu shidai. Babu ruwansa da wata aƙidar dake tsakanin iyayensa da su.. Ganin sunzo har Bina ta kira Ramadhan ta roƙesa zuwa gaida Aunty Halima itama. Bai hana ba, dan tun farko ma daya san Aunty Haliman a Bina take itama da kwanan akai mata.

Sai dai gsky a matse yake da matarsa, burinsa kawai ta dawo. Aunty Halima taji matuƙar daɗi dayin farin cikin zuwan na Raudha. Hakama yaranta. Kasancewar Ramadhan yace sukai har dare sai su biyo jirgi yasata baje kolinsu sosai a gidan Aunty Halima. Dan sai kusan tara suka nufi airport jirgin 9:30 zasu bi.

     Ƙarfe goma bataiba ma suka iso Bingo. Motocin da suka tafi tarbarsu da securitys suka kwasosu sai government house. A ranar ma dai Ramadhan yayi kawaicin kauda idonsa saboda yasan da gajiya tattare da su. Dan ko keɓewa bai yarda yayi da Raudha ba. A ɗakin da take jego ya shigo suka gaisa da su Aunty Zuhrah itama Raudha ta gaisheshi ya ɗauka Abdull ya fita. Kusan mintuna talatin yay kiran Basma a waya tazo ta ɗakko Abdull ɗin ta dawo da shi.


       Washe gari su Hajiya Mama suka tarkata yan kayansu kafin Ramadhan haƙurinsa yakai karshe ya fara rashin ta ido. Shatara ta arziƙi suma ya haɗa musu suka tafi Raudha na matsar kwalla. Tsabar ya shiryama wannan weekend suma su Basma cayay zuje Taura house suyi weekend. Raudha zatai magana ya dinga zuba mata harara da mintsini. Doleneta tai shiru……….✍

[/indeed-social-locker]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button