JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 53

Da daddare Jiddah ta fito daga dakinsu, ta karaso cikin parlon ta xauna tana kallonsa da murmushi fuskarta a hankali tace “Ina yini” Ya d’an kalleta yace “Lafiya lau Jiddah, ya jikin?” Tace “Naji sauki, ya su Mommy” yace “Alhmdlh… kin sha bacci” ta d’an kallesa tace “Wai tun daxu ka xo?” Yace “Yea, almost an hour and a half now, kina ta bacci abun ki” Rufe fuskarta tayi tace “Ayya, to yaushe ka dawo, na xata wata daya kace min xaka yi” ya shafa beard dinsa yana murmushi yace “Ai kawai na xo dubaki ne xan koma gobe in sha Allah” Ta wara ido tace “Tun daga Lagos din ka xo dubani?” Yace “Yahh, is there anything wrong with that?” Ta girgixa kai tana murmushi, yace “Da Maimoon tace min anyi

hospitalizing dinki i was so disturb, shine kawai na biyo flight xuwa Kaduna just to check on u” a hankali Jiddah tace “Toh nagode” Yayi mata murmushi yace “Amma kinji sauki sosai yanxu ko?” Tace “Um naji sauki sosai, Alhmdlh” Yace “Maa sha Allah” bude kofar parlon aka yi duk suka juya, tun da ya shigo yake kallonsu, Shi dai Yusuf ya maida dubansa kan Jiddah da ta sunkuyar da kanta, Abuturrab ya karasa

dinning ya ajiye ledan hannunsa sannan ya dawo parlon ya d’an kalli Yousuf yace “Good evening” Yusuf ya daga kai ya kallesa yace “Good evening, ya aiki….” Abuturrab ya nufi kofa ya fita yace “Alhmdlh” Bayan few minutes Yousuf ya kalli Jiddah yace “I will be on my way now Jiddah, my flight will be around 8 tomorrow” Ta kallesa tace “Toh bari in gaya ma Umma” Yace “Noo, u don’t need to, xan kirata idan

na tafi” Tace “Toh shkkn” mikewa yayi ita ma ta tashi ta rakasa xuwa waje, a compound yana kallonta yace “Ya karatun?” Tace “Lafiya Alhmdlh” Yace “Ki maida hankali don ki samu kiyi waec next year kin ji?” Tace “Toh nagode” Bakin gate ta rakasa ya ciro kudi a aljihunsa ya mika mata yace “Ban kawo maki komai ba, so u can get whatever u wish” Ta dinga kallon kudin memories din lkcn da Abuturrab ke xuwa wajenta a hayi ya hau dawo mata, shi kadai ne ya ta6a bata kudi da yawa haka ta ba Baabarsu, wajensa ta fara ganin kudi da yawa, Yousuf dai kallonta kawai yake ganin yanda take kallon kudin, can

tayi murmushi tana girgixa masa kai tace “Aa nagode” Yace “Ni na baki ki amsa Jiddah” Daga kai tayi suka hada ido da Abuturrab dake tsaye jikin motarsa a bit far from them, ta sauke idonta tace “Ni bana bukatan komai don haka ba abinda xanyi da kudi, nagode Allah ya saka da alkhairi” Yousuf ya dinga kallonta, sai kuma yace “Ni nace kina bukatar wani abun ne!” Ita dai bata ce komai ba, yace “Toh shkkn sai da safe” Yana fadin haka ya xaga ya shiga motarsa ta juya ta koma cikin gidan, dakinsu ta shiga direct ta kulle kofar tayi kwanciyarta, Maimoon da ke danna laptop tace “Sai ga yaya Aliyu ya xo yau ma” Jiddah ta kalleta tace “What about that?” Maimoon tace “Atoh ni naga kwanan nan sai yayi ta

xuwa gidan nan bayan mu sai mu shafe wata da watanni bamu gansa ba in dai ba Ya Ahmad na nan ba, to shine abun ke bani sleepless night…” Tagumi tayi bayan ta fada hakan, Murmushi Jiddah tayi tace “Za ki ga Sleepless night” Maimoon ta fashe da wani dariya tace “But on a serious note me ke kawo Ya Aliyu gidan nan don Allah?” Jiddah tace “Toh ki tambayesa mana” Maimoon tace “Ni kaza??? Bari dai kawai in sa a raina saboda yana son su yi sulhu da Umma ne yake sintirin xuwa, kinsan fa Umma haushinsa take ji tun lokacin bikinsa da wnn ajebo din, amma bari dai in ci gaba da xuba ido ko xan gano wani abun daban” Jiddah ta juya mata baya bata ce komai ba, abinda ya faru daxu a hospital ne ya fado mata, ta turo baki sai kuma ta kulle idonta da sauri. Kwana uku Jiddah tayi tana period kafin ya

dauke har a lkcn kuma Umma bata san tayi ba, amma throughout period din babu wani ciwo da ta ji, sai dai bata iya cin abinci ne kawai. Ranan talata ta koma gidan Ramlah ta ci gaba da karatun ta…. As usual ranan friday da yamma Abuturrab ya shigo gidansa from Kano state, Aneesah ta fito daga kitchen tana sanye da kananun kaya ta karaso da sauri ta rungumesa warmly tace “Welcome back my captain” Ya d’an kalleta yace “Thank you” Ta durkusa ta fara cire masa cover shoe din kafarsa, da kansa ya karasa cirewa yayi wucewarsa sama, ta bi sa tana rike da jakar laptop dinsa da ya ajiye… Har ya fito wanka tana dakin ta shigo masa da abinci ta baxa kan carpet da zobo drink, ya gama shiryawansa cikin

kananun kaya, cike da shagwaba tace “In xuba maka abincin yanxu ne My Captain?” Yace “Na ci abinci tun after juma’at prayer” Lkci daya ta hade rai tace “What did u mean then??” yace “I mean xan ci anjima in sha Allah, yanxu Abba na kirana ne” bata fuska tayi ya gama abinda yake ya dau car key yace “Sae na dawo” daga haka ya nufi kofa ya fita, da sauri ta mike ta bi bayansa tace “Captain nima yau

nake son xuwa gaida su Ummi fa” Ya girgixa kai yace “Ni kin ga sauri nake yanxu, sai dai gobe” Tabe baki tayi har ya fita parlorn. Abuturrab na isa gida a waje yayi parking ya shiga ciki, parlon Abbansa ya nufa yayi sallama bakin kofa har aka amsa masa sannan ya shiga, Abba ne xaune parlon da uncle dinsa Alhaji Umar, ya xauna kasa duk ya gaishesu, bayan few minutes Abba yace “I wanted asking you about that girl with Umma” Abuturrab ya daga kai ya kalli Abba, Abba yace “A wani anguwa suke a can hayin rigasa?” Abuturrab ya d’an yi shiru, sai kuma yace “Me ya faru Abba?” Abba yace “Babu abinda ya faru,

sani muke son yi…” Ya sauke idonsa sai kuma yace “Ni ban san sunan anguwan ba” Abba yace “Amma kasan anguwan ai ko?” Da kyar yace “Na sani” Abba yace “Toh madallah” Alhaji Umar yace “Ko kuma kawai ka dangana mu da gun mai anguwan tunda ka san sa” Abuturrab yace “Abba wani abu ya faru ne?” Abba yace “Not at all, gobe asabar tunda kana nan sai mu tafi gaba daya” Abuturrab bai kuma cewa komai ba, Abba yace “I think that’s all” Mikewa Abuturrab yyi yace “Xan je in gaida su Ummi”

Abba yace “Alright” fita yayi daga parlon, ya tafi dakin Hajja, Hajja tayi masa kallo daya ta karasa dage labulayen dakin da take yi, yace “Ina yini” sai da ta fara kallonsa don tabbatar da cewar da ita yake sannan tace “lafiya lau” Tsintsiya ta dauka tace “Yanxun nan muka gama waya da Kabiru, kaga da nayi masu bori ai gashi an dau maganata da muhimmanci, da fa gantalar da xancena aka so yi, basu san ni er banxa bace idan tsiyata ta tashi, amma duk Safinah ce munafukar.. tun farko naga yanda ta dau maganar tawa ai” Abuturrab dai kallonta kawai yake, Hajja tace “Shi ma El-Basheer din mun yi waya da

shi daxu ai…” Abuturrab yace “Me ke faruwa?” Hajja ta kallesa tace “Aa wannan kuma sirrinmu ne, babu ruwanka, kai wa kake gaya ma sirrinka balle mu bude maka cikinmu?? Kaji min mutumi dai, ko a Masar wanda ke yi da kai da shi kake yi ko da kuwa jininka ne…” Mikewa Abuturrab yyi ya nufi kofa ya fice daga dakin, Hajja tace “Da dai ya fi maka, nan nan nan ka auro dangin xabiya har aka gama bikin nan babu karen da yayi shawara da ni balle in tofa Albarkacin bakina, mu dai duk yanda aka ce mana haka muka dinga yi kamar shashashai, daga karshe ma ashe er iska kazama ka auro.. to ka dai yi ma

kanka wllh” Abuturrab na fita bangaren Ummi ya tafi, Bayan sun gaisa, Ummi da ta lura da mood dinsa tace “Is there anything?” Ya girgixa kai yace “Nothing” Ummi ta ci gaba da aikin da take, bayan few minutes Abuturrab yace “Daxu kafin mu taho daga Abuja Abba ya kirani yana nemana, and na xo yanxu sai yake tambayata unguwar su Jiddah” Ummi ta kallesa tace “Wacece Jiddah?” Abuturrab yyi shiru yana kallonta, Ummi tace “Ohh… sure ni ma ya tambayeni nace masa sai dai a kiraka…” yace “Toh me ke faruwa Ummi?” Ummi tace “Baka tambayesa ba kafin ka fito?” Shiru yyi, Ummi tace “Toh nima ban

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button