Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

Kodinetan hadin gwiwar jam’iyyun siyasar ne ya bayyana hakan bayan buda baki da shugaba Buhari a Abuja
Kodinetan ya ce, ya gamsu shugaba Buhari ne gwarzon dimokradiyya, kuma mai son ci gabanta a Najeriya
Nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.
Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam’iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.
Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.
Kodinetan na IPAC ya kuma bayyana shugaban a matsayin dan dimokradiyya na gaskiya.
Ya ce taron buda baki da kuma gayyatar da shugaban kasar ya yi masa ya kara tabbatar da ‘nuna amana da mutuntawa a harkar siyasa’’.
A cewarsa:
“Kasancewa da shugabannin siyasa na jam’iyyun siyasa daban-daban a zaune tare da kai a yau ya nuna cewa da gaske kai mai bin tafarkin dimokuradiyya ne kuma ka yi imani da tsarin bunkasa dimokradiyya a kasar nan.”
Kodinetan na IPAC, wanda ya yabawa INEC kan kirkire-kirkire da gyare-gyare domin tabbatar da sahihin zabe, ya kuma roki shugaban kasar da ya duba rawar da hukumomin tsaro za su taka a zabukan da ke tafe.
Ya kara da cewa:
“‘Yan kungiyar IPAC sun damu da shirin INEC na cewa zababbun ‘yan takara za su shafe watanni 10 suna kamfe a fadin kasar nan. Wannan aiki ne babba.”
Yabagi, shawarci a kafa ofishin da zai zai tabbatar da samun daidaito tsakanin ofishin shugaban kasa da jam’iyyun siyasa, inda ya kara da cewa:
“Muna kuma son shugaban kasa ya duba batun nadin jami’in hulda da jama’a na siyasa.”
A ruwayar Peoples Gazette, wakilin ‘yan kasuwa da kungiyar Sahara Group GMD Kola Adesina ya yi tsokaci game da irin jagoran da Najeriya ke bukata bayan Buhari, ya ce dole ne mutum ya rike “tuta na fata gasabuwar Najeriya, ba tutar son kai ba.
Asali Hausa Legit
[ad_2]