BAKAR WASIKA 16

“Hello Leila”
“Ali ya weekend?”
“Alhamdulillah”
“Am akan maganar da kuke da Talba ne yanzu”
“Okay…”
Yayi shiru yana jiran yaji abun da zata ce, sai ta rasa ta inda zata fara ta san duk irin wayon da zata yi ba zai taba fada mata sirrinsa da Talba ba, sai dai idan ba sirri ba ne.
“Ban fahimci abun da kuke magana akai ba, kuma na ga kamar ransa a bace”
“Leila”
“Na’am”
“You should feel free to ask when ever kika ga Talba a damuwa ko matsala, shi ne fa mijin da zaki aura a tare zaku gina rayuwa idan kuna irin wannan zaman rayuwarku ba zata taba yin dadi ba”
“Na sani, amman ka san halin abunka, zan iya tambayarsa ya ki fada min ni kuma na damu ne kawai”
“Ki saka a rayuwarki ba ki da wanda yafi Talba, idan har kin damu da damuwarsa ya kamata ki tambaye shi”
“Zan yi haka, amman for now ina jin akan wata yarinya ce da na nuna masa jiya tana bukatar taimako, yar gudun hijira ce”
Shiru tai kamar mai tunani.
“Subhanallahi, tana ina yanzu?”
“Asibitin mu”
“Okay Allah ya bata lafiya, amman idan ana bukatar taimako Ali kai na gida ne, ka san yadda komai a Foundation din mu yake, ba sai ka sake yi masa magana ba, domin ba zan taba lamunta Talba ya kwana da tausayin wata a ransa ba, an yi na farko kuma na karshe, bana son ya kwana da kowa a cikin ransa sai ni”
“Ameen”
Ya amsa addu’ar da tai a farko yana murmushi, sannan ya aje wayar ba tare da ya sake ce mata komai ba domin ya san kishi ne.
Sai ta sauke ajiyar zuciya tana dan jin sauki a ranta.
“Ranki ya dade, Hajiya ta ce a kira ki”
Ta juyo da sauri ta kalli Mairo, sai kuma ta rufe da masifa domin ba karamin razana ta tai ba.
“Wai miyasa komai ba ku iya yinsa a cikin natsuwa ne? Mi yake damunku ne? Wannan ya zama na karshe da zaki sake kira sunana da karfi I’m not your mate”
Ta karasa tana jan tsaki sannan ta nufi hanyar shiga babban falon, bata ko tsaya kula Mairo b dake aikin bata hakuri. Ko da ta isa dinning din kowa ya hallara har sun fara cin abinci.
“Ina kika je?”
Momy ta tambaya tana kallonta.
“Waya na amsa”
Ta fada sannan taja kujera ta zauna tana mikawa Daddy gaisuwa. Sai da suka nisa da cin abincin sannan Daddy yai gyaran murya ya ce.
“Ina son na yi wata magana mai muhimmanci, Shiyasa na bukaci a shirya mana abun karyawa a nan, musamman mahaifiyarku”
Jin hakan tasa kowa ya kalleshi har Momy.
“Allah yasa ba laifi na yi ba”
“Laifi kika yi kuma babba, laifin da ban saka ran zaki yi ba a matsayinki na uwa, sam ban tsammaci haka daga gareki ba, ban yi zaton rana zata zo da zaki dubi dana ki fada masa cewar ba ke kika haife shi ba…”
Talba ya tsaya da cin abinci ya dago ya kalli Daddy dake maganar cikin tsananin bacin rai, Momy kuma tana kallon Talba a tunaninta shi ya fadawa Daddy abun da ya faru.
“Again?”
Momy ta tambaya tana cigana da kallon Talba rai a bace.
“Ba shi ya fada min ba wacan karon ma ba shi ya fada min ba…”
Kamin Daddy ya karasa Amal ya karba tana kallon Kabir.
“Ni na fadawa Daddy, ni kuma Ya Kabir ne ya fada min”
Momy ta kalli Amal kamin ta kalli Kabir.
“Na ji na yi laifi amman Amal bata fada maka danka yana wuce gona da iri ba?”
Da wani irin karfi da fusata Daddy ya daki teburin cin abinci.
“Da na be yi komai ba Amina… Wannan dalilin ne yasa na tara ku duka anan, saboda Leila ba zan yarda ki rika batawa Mu’azz rai ba, ko da rana daya bana jin ya taba miki wani abu da zai banban taki da uwar data haife shi, akan me zaki zabi raba kan yarana? Ko bana da rai shi zai yanke hukunci a gidan nan kuma shi zai dauki dawainiyar komai, na tara ku a nan ne saboda na ja miki kunne kuma. Yaranki su daina kokarin wuce guri ko da mafarki ban tsammaci zaki iya furta kalaman da kika furtawa dana ba, saboda abun da Amal ta fada min jiya ban samu bachi da kyau ba, ko kadan bana son abun da zai raba kan yayana kuma bana fatan Allah ya nuna min ranar da Talba zai ji bakincikin rashin uwa”
Yana kawai nan ya mike tsaye a fusace ya nufi dakinsa, kowa shan jinin jikinsa yai har Talba din da Daddy yake masifa saboda shi, domin ya san indai akansa ne tsab Daddy zai iya fushi da shi ko yai masa fada. Amal ma tashi tai da sauri ta bi bayan Daddy, domin ta san sakamakonta gurin Momy.
Momy da hawaye ke sauko mata ta kalli Talba tace.
“Mutum baya kuskure ne? Ni kaina na ji cewar ban kyauta ba, na ji cewar be kamata na furta kalaman nan ba”
Talba yayi saurin girgiza mata kai.
“Haba Momy kamar baki san halin Daddy ba? Yanzu zai hau kuma yanzu zai sauko, be kamata wannan ya dame ki ba, kin mu sanin Daddy fa, muma a tare muka bude ido muka ganku please ki yi hakuri dan Allah”
“Ka yi hakuri kai ma, ban kyauta ba na sani, Allah ya muku albarka”
Ameen. Duk suka amsa har Leila sannan ta mike tsaye ta nufi hanyar bedroom din Daddy, hakan yasa Leila ma ta tashi ta nufi hanyar fita daga part din gaba daya.
“Daddy’s Boy?”
Kabir ya fada yana kallon Talba, sai Talba yai murmushi kadan.
“Har yanzu Daddy be yarda na girma ba, yana ganina kamar jariri”
“Maybe sai ka yi aure ka haihu ya ga ka fara bawa yayanka kulawa”
Ya dan tabe baki kadan.
“Ni ma ina son ganin haka, you know i love children alot, but before then ya kamata ka iya bakinka, Amal parrot ce ba komai ake fada mata ba, yanzu kaga abun da taja mana”
“Da gangan na fada mata ai, saboda na san zata tseguntawa Daddy, sincerely speaking Momy bata kyauta ba, she shouldn’t say that, we’re one family be kamata tai haka ba, rai na be taba baci irin jiya ba”
Cewar Kabir with serious face. Talba ya dauki tea gabansa ya sha kadan.
“You know mata suna da rauni Kabir, kuma tunaninsu gajere ne, shiyasa ba a zure musu kuma ba a kuresu, idan bama dauke kai ga wasu abubuwan zamu yi ta ji da ganin abun da bama so, ya kamata ace muna yafiya da manta kuskure, no body above mistake”
“Yeah wani lokacin kuma muna yin abu saboda ya zame mana darasi so that kar mu sake aikata shi nan gaba”
Murmushi kawai Talba yai be sake cewa komai ba, ya cigaba da cin abinci har sai da ya koshi sannan ya mike tsaye ya dauki wayarsa ya nufi kofar fita yana jin wani irin kaunar Daddy, ji yake yafi kowa sa’a a duniyar domin ba kowa ke samu uba kamar yadda shi ya samu nasa ba, kaunar da Daddy yake masa bata misaltuwa shi kansa ya sani.
Fitowa yai daga bangaren gaba daya ya nufi bangarensa, yadda ya tsaya yana kallon harabar gidan sai rantse da Allah yau ya fara ganin gidan, sai hankalinsa na can wani gurin daban ya dade a tsaye sannan ya karasa entrance din ya murda kofarsa ya bude. Yana shiga yai wanka ya fito ya shirya cikin shadda milk color ya saka hula sannan ya saka wallet dinsa da wayarsa aljihu da ya fito rike da makulli mota ya ja kofar.
Leila na tsaye jikin window dakinta tana kallonsa da murmushi a fuskarta har ya shiga motarsa ya danna horn aka bude masa ya bar gidan.
Sai ya fara biyawa ta shagon da yake siyen sweet da chocolate din da yake zuwa da su gidan marayu sannan ya wuce gidan abokinsa Ali domin a tare suka saba zuwa, wani lokacin Ali zai zo ya dauke shi wani sa’in kuma shi yake zuwa ya dauki Ali kamar dai yau. A bakin gate din gidan ya faka motarsa sannan ya ciro wayarsa ya kira Ali, Ali na yin picking sai ya kashe wayar ya aje. After like 5 minutes Ali ya fito ya bude motar ya shiga, Talba yai reverse sannan suka hau titi.