BAKAR WASIKA

BAKAR WASIKA 17

Ad

_____

“Shamsu ne?”

“Eh Hajiya ina wuni?”

“Lafiya kalau shigo mana”

Talba ya juyo tana kallon Momy dake amsa masa da far’arta kamar ba ita ba. Sai kuma ya juya ya kalli Shamsu dake kokarin shigowa.

“Baaba ka zo nema…?”

Kamin Shamsu ya ce komai Momy ta daka masa tsawa.

“Talba ka barshi ya huta ya sha ruwa mana, Mairo akai shi karamin falo a kawo masa ruwa”

Momy ta karasa tana kallon mai aikinta Mairo, sai Mairo ta amsa a ladance.

“Toh Hajiya”

Ta wuce gab Shamsu ya bi bayanta, Momy ta gyara tsayuwarta tana kallon Talba.

Ad

“Bangaren Mahaifinku zaku yi lunch”

Ya gyada mata kai yana bin Shamsu da kallo.

“Zulai ta kai komai a can Engineer kai kawai yake jira”

Ta fada tana juya wayarta a hannunta, yanayin yadda tai maganar yana nuna masa son take ya bar mata falon. Ya san ba zai iya nufar falon ta ce akai Shamsu ba, idan ma yaje ba zata bari yai magana da shi ba, idan kuma ya ce zai musa mata zata yi korafi.
Juyawa yai ya fice daga falon gaba daya zuciyarsa cike da tambayoyi kala kala, a entrance ya tsaya yana kallon harabar gidan, sai kuma ya nufi gate din ya fice daga gidan gaba daya.
Yana fita falon Momy ta rufe kofar da kanta tana sauke ajiyar zuciya. Lumshe ido tai ta bude tana kai hannu ta dafa kirjinta dake mugun bugawa da karfi, sannan ta bar jikin kofar ta nufi karamin falon inda Shamsu yake zaune, yana ganinta sai ya sauka daga kan kujerar ya zauna a kasa abun ka da mutunen kauye akaai girmama mutane.

“Shamsu ya gida ya kowa?”

Ta tambaya bayan ta zauna.

“Lafiya kalau Hajiya”

“Maa Shaa Allah, fatar su Baaba ma suna lafiya?”

“Eh… Ai ita aka ce na zo na duba, kwana biyu an ta kiran wayarta baya shiga”

“Ah ah Subhanallahi, Baaba ai yau kwananta tara ko takwas da tafiya gida”

Shamsu ya kalleta da sauri.

“Gida Hajiya? Wallahi bata je gida ba”

“Subhanallahi Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, lallai tabbas ni ma nayi ta kiran wayarta bayan tafiyarta ban samu ba, amman ban saka ran komai ba saboda na san kauye wani lokacin akwai matsalar network ko nepa, kaga ai shiyasa binciken yake da dadi Allah yasa ba mugun hannu ta fada ba, amman ka bincika aka ce bata je ba?”

“Wallahi bata je ba, ai idan tana can dole zan sani saboda a gidan nake, kuma bata fada miki dalilinta na zuwa ba”

“Eh to gaskiya bata fada min ba, na san dai kamin ta tafi tana dan jin jiki, domin da kaina ma na dauke ta muka je asibiti aka ce zazzabi ne da hawan jini, bayan mun dawo da kwana biyu tace min tana son taje kauye ta ga kowa hankalinta ya koma can a yanzu, ta inda nai kuskure ban tambaye ta me take tunani ba, domin hawan jini baya tasowa haka siddan sai da damuwa ko bakinciki har ma nake cewa ba zata kira ta fada a kauye ba tace bata son ta tashi hankalinsu”

Wani kalar tashin hankali ne ya cika Shamsu, jin cewar Baaba bata gidan ga wayarta ma idan an kira ba a samu, Momy kuma ta fada masa cewar yau kwananta tara da tafiya. A gabansa Momy ta nemo number Baaba ta kira ta saka wayar a speaker, daga ita har Shamsu suka ji cewar wayar a kashe take. Shamsu ya mike tsaye

“Wallahi haka nima suke ce min idan na kira, su ma can haka suka ce wayar a kashe take, amman yanzu zan kira na fada musu halin da ake ciki”

“Gaskiya kam kara a dage da addu’a kuma a saka cigiya, ni ma Inshallah zan bada sanarwa gidan radio ko Allah zai saka a dace”

“Zan tafi Hajiya”

“To Shamsu bari na baka number na duk yadda kake ciki sai ka kirani”

Ta fada tana karanto masa number ya saka sannan ita ma ta mike tsaye.

“Bari na kawo maka wani abu ka hau mota”

Tsaye a falon cikin tashin hankalin kamin Momy ta kawo masa 5k din har ya matsu domin hankalinsa gaba daya ya koma gurin inda yake tunanin Baaba zata iya zuwa. Ya karbi dubu biyar din data bashi yana godiya ya fice da saurinsa kana ganinsa kasan bayan cikin natsuwa. Har bakin kofar babban falon Momy ta raka shi tana ta masa addu’ar Allah yasa a gane ta ya amsa da Ameen sannan ya fice ta maida kofar ta rufe. Sannan ta hau sama da sauri ta nufi dakin Leila, Momy na turo kofar Leila ta zabura ta mike tsaye da sauri tana hawaye jikinta har rawa yake.

“Miye haka? So kike idan ya gani ya fara zargin wani abu”

Leila ta kama hannayen Momy ta rike tana kuka.

“Momy tsoro nake ji”

“Ki daina jin tsoro, babu abun da zai faru, idan kina nuna irin wannan hallayar sai ki tonawa kanki asiri, amman idan kika cire komai a ranki sai ki samu kwanciyar hankali”

“Momy har yanzu ina mafarkinta Wallahi, kuma ina jin kamar asirina zai tonu”

“Idan ma asirin ki ya tonu sai mu zuba miki ido akaiki gidan yare? Ko ayi miki wani hukunci? Noooo babu abun da zai same ki, je ki kwanke fuskarki ki shafa hoda ki same ni a bangaren Daddynku”

Ta gyada kai wasu hawayen na sauko mata.

“Momy akwai CCTV a gidan nan, Talba zai iya bincikawa, kuma idan ya gane zai iya cewa ba zai aure ni ba”

“No kul bakinki ya daina furta wadannan kalaman, Talba ba shi da mata sai ke, ki kwantarta hankalinki zan saka a cire CCTV cameras din, je ki wanke fuskarki”

Ta saki hannayen Momy ta nufi bathroom dinta Momy kuma ta fice daga dakin, tana saukowa ta nufi kofar da zata sadata da part din Daddy.

Kamar zai tashi sama haka Shamsu ya nufi gate yana ciro karamar wayarsa ya ciro karamar wayarsa domin kiran yan’uwansa ya sanar musu halin da ake ciki, police din dake gadin gate din ya bude masa ya fita hankali a tashe. Talba dake tsaye wajen gate din ya kalleshi yana karantar irin tashin hankalin da yake ciki.

Ad

_____

1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button