BAKAR WASIKA 16

“Ina yara?”
“Lafiya Kalau Gwauro”
Ali ya amsa masa yana kallonsa fuskarsa da dariya. Talba be sake cewa komai ba har suka kusa isa sannan Ali ya dauko masa zancen Aminatu.
“PA ka ya turo kudi dazun Allah ya saka da alheri”
Nan ma Talba be ce komai ba, har sai da Ali ya dauko masa zancen kiran da Leila tai masa dazun yana murmushi, sannan ya kalleshi.
“Da kai tai waya da safe kenan?”
“Yeah kishi take wai ba zata iya daukar ka kwana da wata a rai ba”
“And…”
Ali ya kalleshi.
“And she’s right”
Tabe baki Talba yai be sake cewa komai ba har suka isa gidan marayun, tun kamin ya karasa harabar yaran suka nufoshi a guje suna murna da zuwansa, murmushi ne ya cika fuskarsa farinciki marayu na daga cikin abun da yake faranta ransa, musamman kananan domin Talba mutum ne mai matukar son yara. Da sauri ya bude motar ya shafa kansa yana tambayar lafiyarsu, sannan ya mika hannunsa ya dauko alawar daya siyo musu ya bude ya fara raba musu.
“Uncle ni dai chocolate nake so”
Wata yar karamar yarinya ta fada, sai ya amsa mata in a funny way yana dariya kamar ba shi ba.
“Noooo chocolate dai anjima idan zan tafi”
Ali ya bude dayan side din ya fita yana amsa waya.
“Subhanallahi gani nan zuwa”
Ya fada sannan ya saka wayar aljihu ya zagayo side din da Talba yake zaune a motar.
“Zan barka nan na tafi asibiti”
Wani kallo Talba yai masa wanda ke nuna alama ce ta tambayar lafiya.
“Wai yarinyar nan aka samu ta suma hannunta nata zubar da jini kuma robar karin ruwa murde a wuyanta kamar an shaketa”
Shiru Talba yai fuskarsa da mamaki sannan ya fito cikin motar gaba daya.
“You can go with my car”
“Thank you”
Ali ya fada sannan ya shiga motar da sauri, Talba ya bude baya ya dauko ledar chocolate din sannan ya rufe har lokacin fuskarsa dauke take da mamaki, bin motar yai da kallo har sai da Ali ya fita gate din sannan ya maida dubansa gurin yaran sai dai gaba daya hankalinsa ya tafi akan dalilin da zai saka yarinyar ta aikata haka, he don’t even think zata ma iya aikatawa kanta haka sai dai idan wani ne ya kashe ta ko kuma yake kokarin kasheta.
Be wani dade sosai kamar yadda ya saba yi ba domin hankalinsa gaba daya ya tafi gurin yarinyar, and baya son azahar tai masa a nan saboda a tare suke cin abincin rana da duka Family kamar yadda suke yi da safe on every weekend sai dai idan akwai wani uzuri. After like 2 hours da wucewar Ali ya turawa direbansa sakon inda yake. Sannan ya bude chocolate din ya shiga raba musu yana Murmushi kamar ba shi ba.
Bayan ya gama yai musu bankwana suka rakoshi har gurin da direban ya faka motar, domin ya dade a zaune cikin motar yana jiran Talba. Kamin ya karaso direban ya fito ya bude masa motar bayan ya shiga ya rufe, ya ya zagaya da gudunsa ya shiga driver side ya ja motar suka nufi gida.
Tafiyar minti talatin suka iso unguwar
shimkafi Quarters, Talba na hakimce cikin motar har direban ya faka motar a kusa da entrance din kofar Momy. Kamar ya bude baki ya ce ma direban ba bangaren Momy zai fara shiga ba, sai kuma ya ji ba zai iya ba, sai da direban ya bude masa motar sannan ya fito ya nufi bangarensa.
Yana shiga ya bedroom dinsa ya bude bathroom yai alwala ya fito yana rike da agogon hannunsa, a inda ya saba aje shi ya aje sannan ya nufi inda Capet dinsa ta sallah take shimfide yai ikama ya fara gabatar da sallah nafila. Kamin ya sallame limamin gidansu ya fara kiran sallah hakan yasa yana sallamewa ya fito daga bangarensa ya nufi masallaci gidansu inda dukansu suke sallah da kuma ma’aikatan gidan.
Bayan saukowa daga sallah azahar ya nufi bangaren Momy sai kamshi turare yake kamar wanda ya lullube jarkar turaren a jikinsa. Sai da ya danna door bell din sannan kuma yai knocking sai ga Zulai da gudunta ta bude masa.
“Sannu da zuwa ranka ya dade”
Kai kawai ya daga mata sannan ya nasa kafarsa cikin falon, saman sofa ya zauna yana kallon Plasma dake ta aikinta, babu kowa a falon sai Leila dake zaune a dinning rike da waya, yana shigowa sai duk hankalinta ya tattara ya koma kansa. Be yi minti biyar da zaman ba aka sake danna door bell din, Mairo dake kitchen ta fito da gudu ta nufi kofar ta bude, daman idan ba yan aikin gidan ba ko Kabir sai Amal sune kawai suke iya bude kofa idan ana kwankwasa, Leila tana ganin ta fi karfin haka, Talba kuma jin kai ba zai bar shi ba.
“Baaba na nan?”
“Ban santa ba gaskiya”
Shiru yai yana kallon sabuwar yar aikin domin be taba ganinta ba, duk kuwa ba da yawan zuwa yake gidan ba amman dai akan aikoshi daga kauye gurin Kakarsa Baaba dake aikin gidan, hakan yasa police din dake gadin gidan suka san shi basa hana shi shiga a duk lokacin da ya zo.
“To Hajiya fa?”
Ya sake tambaya, sai Mairo ta amsa masa.
“Eh tana nan wa za a ce mata?”
“Ki ce mata Shamsu ne jikan Baaba”
“Toh”
Ta saki kofar falon dake bude ta nufi hanyar upstairs. Leila a hango shi ta mike tsaye da sauri.
“Ki ce masa Baaba bata nan”
Ta fada kamar wanda ya rikice. Mairo ta juya da sauri da zimmar fada masa, sai Talba ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu. Mikewa yai tsaye ya nufi kofar Leila na ganin haka ta nufi upstairs da gudu.
Shamsu na ganin Talba ya dan risina masa yana gaishe shi.
“Shamsu”
“Na’am ranka ya dade ya gida?”
“Alhamdulillah, lafiya dai?”
“Lafiya Kalau, daman daga can gida ne suka ce na zo na duba Baaba ko lafiya kwana biyu ba a samun wayarta”
Kamar an dasa ice haka Talba ya tsaya jikin kofar yana kallon Shamsu da mugun mamaki, kwakwalwarsa ta cika da tarin tambayoyi, sai ma ya rasa abun da zai ce wa Shamsu.
Yawun bakinsa ya hade a hankali yana kallon Shamsu har ya bude baki zai yi masa magana sai ya ji muryar Momy dake saukowa tana kiran sunan Shamsu da far’arta, abun da bata saba yi ma talaka ba musamman wanda yake karkashinta.
Khadeeja Candy
Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa
Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660