RAUDHA Page 41 to 50

“Ok ku mu je ku kai Ni”. Yafaɗa yana miƙe wa tsaye da hanzari
Tare suka fice suka shiga motar Suhaib, Rayyan ne ya ja su zuwa asibitin.
Suna isa ɗakin da aka kwantar da RAUDHA, Daddy yayi saurin ƙarisawa wajen ta, zama yayi ya ɗaura tafukan hannayen sa biyu saman fuskar ta yana shafa wa, ji yake yi tamkar yayi ta kurma kuka sabida tsananin tausayin ɗiyar sa. Wai yau RAUDHA ce kwance cikin wani hali na taɓin hankali, duk a sabida sakacin su
Lumshe idanu yayi yana sake sauke wa akan kyakkyawar fuskar ta, wanda ya rame sosai, sai haske da ta sake yi, barci take yi har yanzu sabida alluran barcin da aka yi mata. Ahankali Daddy ya saka hannun sa ya ɗauke hawayen da ya silalo masa a kuncin sa, sannan ya juyo yana kallon su yace, “ina ne Office ɗin doctorn dake duba ta?”
“Daddy bari in Kai ka”. Rayyan yayi saurin faɗar haka
Gyaɗa kai kawai yayi yabi bayan sa
Shi kuma Suhaib ya koma kusa da ita ya zauna a gefen gadon, ya riƙe hannun ta ɗaya wanda akayi mata ƙarin ruwa aka cire.
Wajen mintuna ashirin da fitan su Daddy kafin suka dawo, dayake magriba tayi, sai suka wuce gaba ɗaya masallaci, har bayan sallan isha’i suna nan a asibitin, har sannan kuma RAUDHA bata farka ba, dole suka taho gida suka bar ta cikin kulawar likitoci, tunda dama asibitin ba kasafai suke barin mutane suna kwana da mara lafiya ba. Daddy ya so ya kwana amma sai su Rayyan suka taushe shi akan ya koma gida, tunda shima yana buƙatar hutu a wannan lokacin
Sai da suka mayar dashi gidan sa, kafin suka wuce su ma, da zummar gobe Suhaib zai kawo mishi Haneep da Farida, sai su gaisa tunda yau basu samu sun haɗu ba.
A taƙaice ranan Daddy be iya runtsa wa ba, kwana yayi a zaune yana nema wa ƴar sa samun lafiya daga wurin mahaliccin mu.
Washe gari tare suka taho da Farida gidan Daddy ɗin, anan suka gaisa, Daddy ya amshi Haneep yana ta faman mishi wasa, sosai soyayyar yaron ya shiga ransa, kuma ya tausaya mishi da rashin lafiyan da yake yi, yayi masa addu’a sosai kafin ya miƙa ma Farida shi, sannan suka fito suka nufi asibitin, daga can Rayyan ya wuce wurin aikin sa.
Wajen awanni biyu da zuwan su, sannan ne RAUDHA ta farka, amma kuma gaba ɗaya ta rikita su da koke-koken ta, kuka take yi sosai tana surutu kamar zautacciya, ba ma ta gane wanda ke kanta
Sosai tashin hankali ya sake bayyana a wajen Daddy da Suhaib, sun rasa ya zasu yi, har kuka sai da Suhaib yayi, shi kuma Daddy sai faman sharan ƙwalla yake yi, musamman da ya riƙo ta yana faɗin, “shi ne Daddyn ta, tayi shiru”. Yana rarrashin ta
Sai tahau zagin sa, daga ƙarshe ta soma ɓaɓɓaka masa dariya tana tokarin sa da ƙafa, wai sai ya sake ta ta hau saman silling
Da gudu Suhaib ya fice yana sharan hawaye
Itama Farida dake riƙe da Haneep ta zauna a gefe tana kallon RAUDHA dake jikin Daddy, bata san sanda hawaye yayi ta kwarara a saman fuskar ta ba, sabida tsantsan tausayi
Hauka tuburan RAUDHA take yi, an rasa yanda za’a yi da ita, tunda tuni Suhaib ya kira likitoci sun duƙufa akanta
Ƙiri-ƙiri Daddy ya ƙi fita a ɗakin koda suka buƙaci su ba su wuri
Yanda suka ga hankalin Daddy yayi ƙololuwar tashi, dole suka tausaya mishi suka bar shi a cikin ɗakin, haka suke iya yin su wajen taimaka wa RAUDHA, sai da suka yi mata alluran barci sannan suka samu lafiya, amma ta karaɗe ɗakin da waje da ihun ta
Daddy kasa jure wa yayi ya faɗi ƙasa a sume, ai nan hankalin su Suhaib ya sake tashi da jin abinda ke faruwa
A wani ɗakin aka kai Daddy aka soma ba shi taimakon gaggawa, sosai jinin sa ya hau, ga shi yana buƙatar hutu, dole suka yi masa alluran barci don ya samu ya huta ko jinin sa zai sauka
Abun tausayi idan ku ka ga Suhaib, ya hana kansa sukuni duk ya tsangwami kan sa, shima ba don jarumta da ƙarfin hali ba; da tuni ya zube, sai Farida da ke ƙarfafa masa gwiwa tana masa nasiha akan ɗaukan ƙaddara. tabbas haka Allah ya so ƙaddaran RAUDHA ce, dole wannan ciwon sai ya same ta, sai dai su yi wa Allah godiya tare da roƙon Allah ya taƙaita abun haka.
Wajen awanni uku Daddy yayi a kwance, sannan ya farka. duk yanda likitoci suka so ya zauna ya sake huta wa a ɗaura masa drip amma yaƙi, nan ya soma buga waya ya hau yi mata cuku-cukun yanda za’a yi a fita da ita Abroad, sai dai basu samu ba, tunda ko wani ƙasa ance a dakata da zuwa, shi kansa Nigeria an rufe, dole Daddy ya bar ta anan asibitin, sai dai ya samu an yi masa hanyar likitoci ƙwararru waɗanda za su iya kula da RAUDHA
Abun ka da ma su kuɗi, a washe gari sai ga likitocin sun iso, nan aka duƙufa wajen duba RAUDHA, sosai take samun kulawa wajen likitoci, sai dai kamar ma ƙara haukan take yi, domin ciwon ci gaba yake ba baya ba, ta kai yanzu ɗaure ta ake yi a jikin ƙarfen gadon, sabida idan ta tashi daga alluran barcin da ake mata, ta rinƙa hauka kenan tana fashe-fashen kayan ɗaki, ko kuma tayi yinƙurin guduwa dole sai an kamo ta, har kayan jikin ta take yagawa, sai dai a sauya mata wani.
Bazan iya misalta muku halin da bayin Allan nan suke ciki ba, har wani rama suka yi sabida tashin hankali, babu abinda su Daddy da Suhaib suke yi sai dana-sani, dana-sanin barin RAUDHA cikin shaye-shaye, ga shi yanzu ta haukace suna ji suna gani, kuma kuɗin su be iya ba ta lafiya ba, babu yanda za su yi yanzu sai bin ta da addu’ar samun lafiya, wuni kuwa cikin yin ta suke yi, duk idan suka zo asibitin nan sai sun zubar da hawaye
Gefe ɗaya ma Rayyan duk ya shiga matsanancin damuwa sosai, duk a sabida ciwon RAUDHA, sosai yake matuƙar ƙaunar ta, ko barci ba ya iya yi sabida tunanin ta, da shi ake yin duk wani zirga-zirga na neman maganin ta, ya kasa hankalin sa gida biyu, a hankali shima a tsaye yake rame wa duk a sabida damuwar da ya ɗaura wa kansa.
Yanzu haka dole aka mayar da RAUDHA asibitin mahaukata tunda abun yafi ƙarfin asibitin, an ware mata ɗaki daban a matsayin ta na ƴar gata, sai dai su Daddy su je can su riƙa duba ta, su kansu likitocin ma su kula da ita daban ne aka ajiye mata.
Wasa-wasa sai ga RAUDHA ta shafe watanni huɗu a asibitin mahaukata, tana fama da mugun ciwon da ba ya baya sai dai gaba, kullum-kullum gaba ciwon nata yake yi ba baya ba, duk wani magani an yi mata amma har yanzu ba’a dace ba, ba’a taɓa samun ranan da aka wayi gari an samu nasarar ci gaba wajen samun lafiyan ta ba, sai dai gaba abun yake yi, da sarƙa ake ɗaure ta, abun mamaki kuma sai da safe a zo aganta a kwance. likitan da ke duba ta sosai yake mamaki idan ya zo ya ganta a kwance tana zaune tayi ta ɓaɓɓaka masa dariya.
Yau ma kamar kullum a kwance ya ganta, sai dai kuma abun mamaki a saman cilling ya hange ta tana ta kwasan dariyan dake fita tamkar na mutane goma, ga shi ɗakin yayi duhu sosai sai uban sanyi tamkar ƙanƙara
Da sauri likitan ya kunna wutan ɗakin yana me mamakin “ta ya ɗakin zai yi duhu bayan yanzu yamma ne ba dare ba?”