YARIMA FUDHAL 11-20

*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
11
Har cikin kwakwalwar kanta ta jiyo rad’ad’i da zafi na ruwan tea d’in, ta kafe Yarima da idanuwa cike da kallon mamaki mai d’auke da tambayar me nayi maka?.
Shima Yarim ita ya kafe da idanuwa yana karantar yanayinta can ya kau da fuska gefe yana mai naushin hannunsa na hagu da hannun da mansa game da furzar da iska daga bakinsa mai zafi.
Aynu kuwa ta kasa magana illa hawaye dake zarya bisa kuncinta kawai tarik’e hannun da d’ayan da babu k’unar.
Yarima yayi k’asa da kansa ya dafe da hannu na d’an wani lokaci, kafin ya d’ago ya sake kafeta da ido a karo na biyu, tsaki ya d’anja kad’an yana mai sanya hannunsa ya kamo nata daya k’ona ya dubi hannun tare da duban fuskarta.
“Am so sorry…nayi hakanne domin ki fahimci irin k’unar da na keji a duk lokacin dana ganki da Jalil, why me yasa kika kasa fahimta har na kai da yi miki wannan hukuncin?”.
Ita dai Aynu kallonsa kawai take domin ko kad’an bama ta fahimtar me yake fad’i, azaba ta isheta hawaye kawai take fitarwa domin kuka mai sauti ma k’in fita yayi daga bakin ta a wannan lokaci.
Kai hannu yayi kan fuskarta da niyan share mata hawayen sai kuma ya fasa, ya dubeta yana fad’in.
“Da zafi sosai ne?”.
Kai ta kyad’a masa alamun ehh.
“Sannu yi hak’uri !”.
Abin da yace da ita kenan yaja hannunta suka fito zuwa waje, haka yayi ta janta har suka isa b’angaren Fulani Bingel duk inda suka wuce sai a bisu da kallo amma kasancewar Yarima Fudhal ne kowa yasan babu wasa da sun had’a ido da mutum zaiyi k’asa da kansa yana gaishe shi.
Shi kuwa Yarima bai cika niba har sai da muka isa cikin falon mahaifiyarsa, Fulani Bingel na ganinmu ta mik’e tsaye tare da fad’in.
“Lafiya Magaji?”.
“Hajiya kira doctor d’inki “.
Fulani Bingel ta bishi da kallon mamaki cike da tambaya.
“Mai ya faru da ita?”.
Yarima neman guri yayi ya zauna ya dubi sauran masu aikin dake d’akin.
“Ku bamu waje”.
Sum-sum ko wacce ta fice ya rage daga ni sai Yarima da Hajiyarsu.
Fulani dai ta kafeshi da idanuwa tana jiran amsar sa.
Yarima yad’an yatsina fuska kafin ya bata amsa da fad’in.
“K’onata nayi”.
“Subhanallah ! garin yaya?”.
Cewar Fulani kenan tana mai k’arasowa wajena, taga hannuna yayi jawur ta mai da dubanta kan Yarima.
“Akan me ka aikata wannan d’an yan aikin?”.
“Hajiya ita ta jama kanta fa !, na gaya mata bana son ganinta da Jalil ba ta ji ne yarinyar !”.
“To dan baka son ganin ta da Jalil sai kayi mata wannan mugun hukuncin ?, mai yasa bazaka fad’amin ba ko kayi mata hukunci dai-dai misali”.
“Abin da nake ji araina ne !, shine na gwada mata taji yanda nakeji ko tafi fahimta”.
Fulani Bingel sakar baki tayi tana duban sa cike da mamaki ko mamakin me take yi oho?, sai dai ta kalleni ta kalleshi.
Ajiyar zuciya tayi tana fad’in.
“Mai zai hana ka kira likitanka?”.
“Haba dai Hajiya Namiji ne fa?”.
“Dan namiji ne bazai duba taba”.
“Ina ! A’a gaskiya ki taimake ni dai ki kira likitarki dan Allah Hajiya kinji?”.
Ya k’arashe maganar kamar zaiyi kuka, ni dai ina zaune ina jin ikon Allah tun da nake da Yarima yaune karo na farko da yayi doguwar magana kuma duk a kaina, ga shi kuma babu ko kunya ko nauyi ko shakka bare jin tsoro yana sanarwa mahaifiyarsa da kansa ya k’ona ni !, nidai sai na nemi hawaye na rasa tsabar mamaki da al’amarin Yarima Fudhal.
Hajiyarsa girgiza kai kawai tayi tana dubana ta d’auki waya bugu d’aya tayiwa likitan bayanin abin da yake faruwa, muna ji likitan ta amsa da cewar ga tanan zuwa da yake wayar a free ta sanya ta.
Hajiya ta ajiye wayar tana kallon Yarima da yayi ta gumi yana kallonta, ta jima tana nazarin Yarima Fudhal ba tare da tace komai ba, haka shima bai kuma fad’in komai ba, baka jin k’arar komai a d’akin sai k’arar A.C da ajiyar zuciyata jefi-jefi sabida kukan da nayi.
Muna haka har Doctor Hafsat ta shigo ta tadda mu, ta gaishe da Hajiya da Yarima Hajiya tayi mata bayanin nice na k’one da ruwan zafi, nan da nan tayimin allura tare da bani magani domin k’unar bata tashi ba bare ace za’a wanke, tayiwa Hajiya sallama ta tafi domin tana bakin aiki ne ta tawo.
Tana fita Hajiya tace.
“Ka da ka sake mai-maita hakan kana jina?”.
“Insha Allah”.
Abin da yace da ita kenan, yana mai kwanciya kan kusun, Hajiya tace.
“Mai yake shirin faruwa tsakaninka da yarinyar nan?”.
Yarima ya mik’e ya zauna tare da dubana yana fad’in.
“D’an bamu waje”.
Na mik’e na fice abina dama duk a takure nake jina.
“Ka da dai kacemin sonta ka ke?”.
Murmushi Yarima yayi yana sosa k’eyar kansa jin tambayar da Hajiyan tasa take yi masa.
Fulani Bingel tayi ajiyar zuciya domin ta fahimci komai tun farkon tattauna warsu.
“Ka da kamance ‘yar aikin kace, ‘yar aiki kuwa a gidan nan tamkar bayi ne ko ka mance ne?”.
“A’a”.
“Kasan ko Mai Martaba bazai tab’a yarda ba idan ni na amince !”.
Dammm gaban Yarima ya buga amma ya dake ba tare da yace komai ba, Fulani ta cigaba da fad’in.
“Duk bama wannan ba, kasan cewa ana nema maka auren Gimbiya Safiyya kuwa?”.
A firgice Yarima ya dubi Fulani.
“Safiyya kuma ni nace ina sonta ne har da za’a nema min aurenta?”.
“A’a zab’in mahaifinka ne, to ita wannan d’in tasan kana son tane?”.
“A’a amma ai zan fad’a mata lokaci nake jira, amma Hajiya da gaske kike akan maganar Safiyya?”.
“Na tab’a yi maka wasa ne ?”.
Yarima ya girgiza kai alamun a’a, yayin da kuma zuciyarsa ke ta aikin bugawa da sauri da sauri hankalinsa idan yayi dubu ya tashi, har sai da Fulani Bingel ta fahimci haka ta dafa kafad’arsa tana fad’in.
“Kada ka d’aga hankalinka Magaji ka nemi zab’in Allah kawai, domin kafi kowa sanin waye Mai Martaba”.
“Amma Hajiya ki fahimtar dashi mana nifa gaskiya bana sonta”.
“Kai mai zai hana ka sanar dashi, zaifi fahintar maganarka akan tawa ma”.
Yarima ya dubi Mahaifiyartasa kafin ya kau da kai gefe zuciyarsa na cigaba da k’una, gefe guda kuma yana tunanin mafita akan wannan batun.
***
Aynu kuwa na fita inda ta saba zama taje ta zauna ta had’a kai da gwiwa tana kuka, ji tayi an dafa kafad’arta ta baya ta d’ago da sauri dan ganin waye?.
Zainab ce ta zagayo ta zauna tana fad’in.
“Subhanallahi !, Aynu mai ya faru kike kuka ya akayi kika k’one ke da ba a kitchen kike aiki ba?”.
“Yarima ne Zainab, Yarima ne !”.
Aynu ta sake fashewa da kuka tana mai d’ora kanta kan cinyar Zainab, Zainab ta d’an bubbuga bayanta alamun rarrashi tana fad’in.
“Mai kikayi masa?”.
“Wai akan Yarima Jalil…”.
Nan dai ta kwashe dukkan abin da yafaru ta sanar mata, Zainab tayi ajiyar zuciya tana fad’in.
“Kece bakyaji ai na gaya miki waye Jalil kin k’i yarda, amma abin tambaya kenan Yarima Fudhal yana kishin ganinki da Yarima Jalil?, Idan har kishi yake kenan sonki yake ko?”.
“Oho nima nasani jeki tambayeshi”.
Zainab dariya tayi domin wasu lokutan tasan Aynu ‘yar rigimace ta k’arshe, a fili kuwa cewa tayi.
“A’a mai da wuk’ar bani nakar zomon ba ratayarma ban d’auka ba”.
Aynu tad’an kaiwa Zainab dukan wasa, tana fad’in.
“Ni ko sona yake Allah bazan soshi ba mugune wallahi na k’arshe”.
Zainab tayi murmushi tana fad’in.
“Ki godewa Allah Aynu samun irin su Yarima Fudhal wuya garesu a yanzu, wallahi nayi miki murna sosai Allah tabbatar mana da alkhairi, ni yanayin soyayyar tashi ne ma ta fara burgeni !”.
Wani kallo Aynu ta jefi Zainab da shi mai dauke da harara.
“Wai ke waya gaya miki sona yake ?, nifa bai fad’amin ba”.
“Daga jin yanda labarin ya fara kowa kika sanarwa Allah yasan al’amarin so ne yaja hakan, domin idan ba so ba mata nawa ne suke harka da Yarima Jalil a gidan nan amma bai da muba sai a kanki, nasan wata rana zai fad’a miki yana sonki”.
“Tab..Allah ma ya kiyaye, dubi fa hannu na wanda yayi maka haka kuma yazo yace yana sonka?”.
Cewar Aynu kenan tana mai k’arewa hannunta kallo cike da takaici, ba tayi aune ba sai ji tayi ruwan hawaye na bin fuskarta.
Nan sai suka Zauna Zainab na k’ok’arin ganar da ita amma ita tana faman botsewa da haka har k’arfe biyu tayi basu sani ba, a gurguje suka had’a inasu inasu sukayi gida, dan Aynu ko part d’in Yarima k’in komawa tayi dan kada wani abun ya sake faruwa.
Yarima na dawowa sallah yahau nemanta amma sama ko k’asa ya rasa ta sai Jakadiyya ke sanar dashi sun tafi gida, kwafa yayi yana duban maganinta da aka bata yana tunanin yanda za’ai ta sha domin kada k’unar ta tashi kafin gobe, hankalinsa idan yayi dubu ya tashi, sai dabara tazo masa ya baiwa Jakadiyya ta kai mata domin yaga ta san ta, ba musu Jakadiyya ta karb’a ta nufi gidan su Aynu domin kai mata maganin lokacin kuwa daf da maghriba ne.
***
Ko da Aynu ta koma gida k’in sanarwa Ummanta abin da ya faru tayi, duk da cewar Umman taji muryarta ta canja tayi tambayar duniya akan meya sata kuka?, Aynu tace .
“Babu komai Umma kawai tari na d’anyi”.
Nan dai ta k’ok’arta tayi dukkan abin da zata iya ta nufi Islamiyya dawo warta kenan ta shiga d’aki ta cire hijab taji sallama, ta fito domin ganin waye sai taga ashe Jakadiyya ce har Umma ta bata gurin zama.
Aynu ta fito suka gaisa tamik’awa Umma ledar maganin tana fad’in.
“Gashi Aynu maganin naki, Yarima duk ya tashi hankalinsa yace kisha kafin ki kwanta, Allah ya k’ara sauk’i ni zan koma”.
“To mungode Allah saka da alkhairi ki gaida gida a yiwa Yarima godiya sosai abisa d’awainiya”.
Cewar Umma kenan dake zaune gefen tabarmar da Jakadiyya ta zauna.
Jakadiyya tayi musu sallama ta tafi, Aynu dai mutuwar tsaye tayi tana jira taji mai Umman zata ce da ita.
“Zo nan Aynu”.
Taji muryar Ummanta Aynu ta k’arasa kusa da ita ta zauna tana fad’in .
“Gani Umma”.
“Fad’amin gaskiya mai ya faru?”.
“Dama….dama fa…dama Umma ruwan zafi ne ya zubomin a hannu”.
“Amma shine zaki min k’arya kice ba komai tari ki kai”.
“A’a Umma kawai banaso hankalinki ya tashi ne “.
Murmushi Umman tayi tana fad’in.
“Aynu kenan, bani hannun inyi miki tofi”.
Aynu ta mik’a mata hannun, Ummanta ta kama tayi mata addu’a kafin ta saki hannun tana fad’in.
“Da ace kina k’onewa ansamu gasarar koko anzuba akai ba zata tashi ba, domin k’una sanyi take so, da zarar ansanya gasarar iska na kad’awa har ta bushe shikenan ba zata tashi ba”.
“Umma ai yanzuma bata tashi ba kawai dai ja hannun nawa yayi”.
“To Allah sauwak’e ya kiyaye gaba ki dinga lura da kyau dai”.
“To ummata”.
[22/07, 20:22] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN)
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
12
Washe gari wayar gari akai Mai Babban d’aki wato Mahaifiyyar Mai martaba babu lafiya, baki d’aya hankalin kowa ya tashi da ka shiga gidan zaka san babu lafiya musamman Yarima Fudhal da Mai Martaba sunfi kowa shiga damuwa da ciwon Mai Baban d’aki.
Ciwo anwayi gari da shi rana d’aya amma kai kace tayi shekara tana yi, tuni aka d’ebeta sai asibiti likitoci uku ne akanta amma sun kasa gano musabbabin ciwon nata bare har asan abin da za’ayi akai.
Ni dai tun da muka doshi gidan ni da Zainab mukasan babu lafiya agidan, muna shiga kuwa muka samu bayanin Babar Mai martaba ce ba lafiya tana asibiti, Yarima ma nacan hospital d’in Zainab ce ta tayani gyara b’angaren Yarima sabida k’unar dake hannuna muna gamawa na nufi gida kuwa domin Saima ma da tazo ta tadda abin da yake faruwa bata zauna ba ta koma gida abinta.
***
Daf da maghriba kuwa Hajiyar Mai Martaba tace ga garin kunan, ba Sarkin ba duk wanda yaji mutuwar baiwar Allahn nan dole yayi kuka mace kamila mai hak’uri da dattako mai son addini da son iyalinta ga uwa uba barkwanci da faram-faram.
Gaskiya bak’aramin rashi su Yarima sukayi ba gari ya d’auka kaf da rasuwar baiwar Allahn nan, ni dai ina zaune a gida najiyo a babban masallacin unguwarmu ana sanarwa cewa za’ayi jana’izar ta da safe idan Allah ya tashemu da rai da lafiya, ba wani shak’uwa mukai da ita ba amma naji mutuwarta sosai babu abin da yafara fad’omin arai irin so da shak’uwa dake tsakaninta da Yarima fudhal koya zaiji aransa oho?
“Allah sarki Yarima Allah baku hak’uri da dangana !”.
Abin da nace kenan ina yankewa Ummata farce ta amsa min da.
“amin Aynu mutuwa ai dole ce sai dai in lokaci baiyi ba duk kuwa irin so da shak’uwar da kukai da mutum dole wataran zaka barshi”.
Jikina yayi sanyi da kalaman Ummata sai naji hawaye nabin gefan fuskata har dai da na tuna Ummata da Baba na su kad’aine duniyata sune farin cikina su kad’ai na sani sune nake kalla inji dad’i, yanzu dole watara zan barsu ko su barni, duniya kenan babu matabbata Ubangiji Allah kasa mu dace ka kashemu da imaninmu amin.
***
Ka sancewar rasuwar da akai nasan kuma cin koso da jama’a yanzu sun cike gidan hakan ya saka nak’i zuwa washe garin da akai rasuwar, nayi zamana agida amma wunin ranar nayi shine cike da tunanin gidan.
washe gari kuma ranar biyu da rasuwar nayi niyar zuwa kodan inyi gaisuwa sai dai na tashi da wani irin matsanancin ciwon kai, Zainab data biyomin mu tafi har da ita asa bakin inyi zama duk da cewar naso zuwa amma Umma da Zainab suka kafe kan in zauna har zuwa gobe inga yanda jikin nawa zaiyi.
“Haba Fudhal kayi hak’uri kad’au dan gana abisa rashin Hajiya da mukayu mutuwa kasan dole ce amma sai da hak’uri, muma da muke mata munyi hak’uri bare kai namiji ?”.
Cewar Yayarsu Aunty Sadiya kenan data iske Yarima d’akinsa shi kad’ai kwance kamar wani mara lafiya.
Falonsa abokansa ne cike amma shi ya wuce bedroom ya kwanta kamar mai bacci amma azahiri ba baccin yake ba domin duk abin da ake yana ji.
Ta gaji da magana amma ko d’ago kai baiyi ya kalleta ba, ta tashi ta fice daga d’akin ta koma wajen mahaifiyyarsu Fulani Bingel tana sanar mata.
Fulani tasan Yarima ya shak’u da Hajiya sosai amma tasan akwai wani abu daban da yake damunsa domin tasan waye Yarima tasan halayyarsa sarai, hakan yasa tayi murmushi kawai ta dubi Aunty Sadiya tana fad’in.
“Rabu dashi kawai akwai abin da dai yake damunsa, kar ki damu”.
“Kamar ya ! Wanne abune yake damunsa haka?”.
“Zanyi miki bayani wani lokacin”.
Fulani Bingel ta wuce ta koma falo inda tabar jama’arta ke jiranta, ta bar Aunty Sadiya nan d’akin tana tunanin me yake damun d’an k’anin nata?.
Yarima kuwa gani yayi kwanciyar babu abin da zata haifa masa illa tarin damuwa mai yawa, hakan yasa shi mik’ewa ya fito harabar gidan yana dube-dube kome yake nema oho?.
Duk inda ya wuce sai gai dashi ake wani ya amsa wani ya wuce kawai da haka ya isa har filin shamaki inda bayi da ma’aikatan gidan ke zaune, suka durk’usa baki d’aya suna gai dashi ya amsa tare da k’urawa Zainab ido, yana tunanin indai bai mance ba tare yafi ganinsu da Aynu may be zata iya sanin wani information akanta.
“Ke zo nan”.
Yayi nuni da Zainab ta mik’e da sauri tabi bayansa domin har ya bada baya ya tafi.
Wani guri yaja ya tsaya inda babu mutane yayi shiru kansa a k’asa bai ce da ita komai ba, har Zainab ta gaji da tsaiwa taji kaman zata fad’i, amma babu daman zama can ya d’anyi ajiyar zuciya ba tare daya d’ago kai ba yake fad’in.
“Ke kinsan Aynul-hayat ko?”.
“Ehh Yallab’ai?”.
“Ok mai yasa 2days bata zoba, ko gaisuwa ma tak’i zuwa ?”.
“Ba tajin dad’i ne”.
Yarima Fudhal ya d’ago kai da sauri yana dubanta, jin maganar da ta doki kunnensa.
“Me yake damunta?”.
“Tace dai ciwon kai ne”.
A jiyar zuciya ya saki mai k’arfi wadda har sai da Zainab ta dubeshi, ya cigaba da fad’in.
“Bani address d’inta”.
Nan da nan Zainab ta bashi bayanin gidansu Aynu, tana gamawa ya juya ya tafi ya barta nan tsaye babu ko godiya Zainab tabi bayansa da kallo aranta tana fad’in.
“Ikon Allah maganar minti biyar amma ashafe awa guda da wani abu anayi, lallai Yarima na musam-manne Matarsa na da aiki kuwa”.
Ta juya abinta itama tabar wajen ta koma inda ta taso.
•••
Aynu dai bata samu ciwon kan ya lafa mata ba sai dare wajen k’arfe takwas bayan sallar isha’i kenan, ta tashi tayo alwala ta hau gabatar da sallolin da bata samu ta iyayi ba, ta idar kenan tana addu’o’in data saba ko yaushe sukaji sallamar Yaro a tsakar gidansu.
Umma dake zaune gefe daga inda Aynu take sallah ta amsawa Yaron Sallama, ya gaishe da Umma yana fad’in.
“Wai ana kiran Aynu a waje”.
“Aynu kuma da daren nan?”.
“Ehh haka yace min Aynu yake nema”.
Aynu ta sallame addu’ar tana fad’in.
“Kace ina zuwa”.
Yaron ya fice Aynu ta dubi Ummanta tace.
“Yanzu haka Ya Sayyadi ne dan yaga yau banje Islamiyya ba”.
“Ehh nima nayi tunanin hakan !, tashi kije kada ki jima dan kinga dare yayi”.
“To Umma ni dama bana jin dad’i, tsayuwarma bazan iya ba muna gaisawa zan dawo”.
Aynu tasa takalminta ta fice.
Dake dare ne kuma unguwar duhu basu da wadatar nepa, hakan yasa bata iya shaida kowane ba, yana tsaye jikin darbejiyar k’ofar gidan cikin k’ananun kaya daya tabbatarwa da Aynu ba ya sayyadi bane domin ta sanshi gwanine wajen shigar jallabiyya yau kuwa taga sab’anin haka, ta waiga bata ga kowa ba illa dai wanda ke tsaye jikin bishiyar.
Dake wa tayi tare da k’arawasa sai dai tun kan takai da isa wajen zuciyarta tahau bugun uku-uku ga kuma k’amshin turarensa daya doki hancinta wanda bata iya manceshi ko a wane yanayi taji shi zata gane nasa ne.
Shi kuwa tun fitowarta ya kafeta da idanuwa yayin da wani sanyin dad’i ya mamaye zuciyarsa, har yanaji aransa kamar yaje ya d’aukota don hutar da ita daga tafiyar da take.
Ta k’arasa wajen da sallam cikin siririyar muryarta ya masa mata ta d’an rissina ta gaisheshi tare da fad’in.
“Kayi hak’uri ban d’auka kai bane…”.
Sai kuma tayi shiru, shima baice komai ba yayi shiru tare da nad’e hannunsa bisa k’irjinsa, a hankali ta d’ago kai duk da a duhu ne amma ta fahimci kallonta yake.
“Ya k’arin hak’uri kuma?, Allah yaji k’anta ya gafarta mata”.
“Amin nagode sosai”.
“Mai ya hanaki zuwa kwana biyu?”.
Aynu ta gyara tsayuwarta sosai tana wasa da yatsun hannunta, ta bud’e baki ta bashi amsa.
“Banajin dad’ine”.
“Shine dalilin da yasa kika k’i zuwa?”.
“Ehh”.
“Ko dai kinajin haushi nane akan k’onakin da nayi”.
“A’a wallahi bani da lafiya sosai musamman yau yanzune ma nad’anji sauk’i”.
“Ok”.
Ya fad’a yana mai mik’o mata ledar dake ajiye gefansa Aynu ma ko lura da ita batayi ba.
Batayi magana ba haka kuma bata karb’a ba, shima kuma baice komai ba illa kafeta da idanuwa da yayi.
“Dole fa ki dinga karb’an kome na baki banason gaddama kamar yanda banaso inyi kyauta adawomin da ita”.
Aynu tasa hannu ta karb’a tare da fad’in.
“Nagode sosai Allah k’ara girma da arzik’i yaji k’an hajiya”.
Murmushi ne ya kufce masa wanda yasa fararen hak’oransa baiyana waje sosai yaji dad’in addu’ar Aynu agareshi, kamar yanda yake jin dad’in sautin muryarta akunnensa yana kuma jin dad’in kasan cewarta atare da shi ko da ba zaice da ita komai ba yanaso ya dinga kallon beauty face d’inta any time.
Aynu tsayuwar tafara isarta har k’afafunta na kakkarwa, amma ta gaza iya furta masa zata shiga gida.
“Kije gida sai da safe”.
Taji muryarsa ta doki kunnenta, domin batayi tsammanin zai sallame ta ba a yanzu.
“To nagode sosai, a gaida su Hajiyarku”.
Ta juya ta tafi domin tasan ba lallai ya amsa ba, shi kuwa bin bayanta da kallo yayi har ta shige cikin gidan nasu ya jima anan tsaye kafin ya nufi wajen da yayi parking motarsa ya shige ciki ya zauna yana tunanin da baisan kona mene ba haka kawai yaji zuciyarsa tab’aci duk da baya raba d’ayan biyun tafiyar Aynu ce taja masa hakan.
Aynu nashiga gida samun guri tayi kusa da Ummanta ta zauna tana fad’in.
“Ashe Yarima ne ba Ya Sayyadi ba”.
“Yarima kuma Allah sa lafiya dai?”.
“Lafiya k’alau Umma wai yazone yaji lafiya ko k’unarce take damuna banjeba kwana biyu”.
“Allah sarki yaron na da kirki kuwa”.
Aynu ita dai ajiyar zuciya tayi ranta tana fad’in.
“Dan bakisan waye shi bane kikace haka Umma”.
A fili kuwa cewa tayi.
“Kin ga harda kaya yazomin da shi kona mene oho, bari in duba ingani”.
Ta fad’a tana mai jawo ledar ta bud’e magunguna tana gani aciki sai kayan snack a ciki da juice gefe guda kuma taga wata guntuwar ta kadda ta bud’e aranta tana fad’in.
“Ko mene a ciki?”.
“Kisha kowanne da k’aidarsa maganin ciwon kannaki ne”.
Aynu tayi shiru tana sake karanta takaddar tare da tunanin inda yasan kanta na ciwao sai kace aljani?.
Ta fad’a aranta.
“Umma magani ne ashe tare dasu snack !”.
“Allah sarki sai kisha maganin to, kyasamu sauk’in ciwon angode masa sosai Allah saka masa da alkhairi”.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
Ina kike ne? Miemie Bashir (Queen) matso kusa wannan page d’in naki ne domin jin dad’inki kawai.
13
***
WASHE GARI
Cikin ikon Allah Aynu ta wayi gari lafiya k’alau kamar ba tayi ciwo ba.
“Umma gaskiya maganin nan yana da kyau kinga k’unar hannun sab’a takeyi har ta warke kenan?”.
“To masha Allah haka ake so ai, Allah ya k’ara lafiya”.
“Amin Ummata”.
Sallamar Babanta ce ta katse su daga hiran da suke ya shigo ya nemi waje ya zauna, Aynu tayi masa sannu da zuwa tana mai mik’ewa domin kawo masa kunu da k’osansa na karyawa, taje ta d’auko ta ajiye a gabansa ya bud’e kwanun ya kurb’i kunun kafin ya dubi Aynu yana fad’in.
“Ya k’arfin jikin naki?”.
“Naji sauk’i sosai Baba”.
“Allah k’ara lafiya, haka akeson ji dama”.
“Amin Baba”.
“Yau ba zaki je gidan Sarkin ba ne?”.
Ummanta ta fad’a tana mai duban gefan da Aynu ke zaune, Aynu ta d’an yatsina fuska kafin tace.
“Ban jin fita wallahi yau Umma ki bari har gobe naje”.
Babanta yayi murmushi yana fad’in.
“Kiyi zamanki ki huta ‘yar gidan Umma ki k’ara samun sauk’i sai kije”.
“To Baba”.
Baban nata ya sake dubanta karo na biyu fuskarsa fal murmushi yana yinsa da komai Aynu ta d’auko kama ce kawai ta d’auko ta Ummanta kamar antsaga kara.
“Ina Umar Faruq kuwa Aynu?”.
“Ohh Baba Ya Sayyadi Umar wai? yana nan”.
“Yaron na da kirki sosai kullum ya ganni har k’asa yake gaishe ni yauma fitar nan da nayi kinga naira d’ari biyar ya bani wai ayi cefane, nayi-nayi ya barta amma yak’i dole na karb’a”.
Aynu tad’anyi murmushi tana wasa da yatsun hannunta take fad’in.
“Ai yana da kirki sosai akwai shi da kyauta ko a islamiyya”.
“Bashi ne nake gaya maka yazo har gidan nan wancen satin ya gaishe ni ba”.
Umma ta fad’a tana mai wasa da sandar hannunta.
“Ai inaji araina kamar akwai wani abu da yaron yake b’oyewa”.
Cewar Baba kenan yana mai kallon fuskar Aynu cike da murmushi, itama murmushin take duk da kuwa fad’uwar gaban da taji ya tsanan ta a cikin zuciyarta, haka kawai taji hiran ta fara gundurarta tamik’e tsaye tana fad’in.
“Bari ingyara d’aki Umma”.
Ta wuce ta barsunan suna ta tattaunawa, daga k’arshe sukabar hiran Ya Sayyadi Umar aka koma ta Yarima, Aynu duk tana jinsu tayi luf a d’aki domin duk cikin su babu wanda take ji hirarsa nayi mata dad’i, sun jima suna hirar kafin Baba yamik’e ya fita waje yabar Umma nan zaune.
Sai sannan Aynu ta fito domin sama musu abin da zasuci da rana kuma.
°°°
Yarima kuwa ranar wuni yayi yana zuba idon ganin Aynu amma har dare shiru, haka ya wuni kamar mara lafiya jama’a da dama suna d’auka alhinin rasuwa ne, amma anashi b’angaren abun da yakeji aransa game da Aynu shiyafi komai d’aga masa hankali da kuma mamaki.
Har ya yanke shawaran zuwa k’ara dubota domin ya zaci ko ciwon ne har yanzu ya hanata zuwa, amma sai dai ya share domin bayaso zak’ewarsa tayi yawa ta rai na shi.
Hakan na d’aya daga cikin abin da yasa Yarima k’in yin soyayya duk cikin shekarun da suka wuce, domin shi mutum ne mai son girma mai son a girmama shi baya son raini ko kad’an, a ganinsa da zaran ya furtawa budurwa yana sonta to raini zai iya shiga ciki shiyasa yake kau da kansa akan duk wata ‘ya mace.
Amma kuma abin mamaki sai gashi rana guda ya kamu da son ‘yar aikinsa kuma ‘yar miskinai so mai tsanani kuwa, duk da yasan abune mawuyaci Aynu ta rainashi domin yarinyar nada tsoro sosai duk da k’arancin shekarunta ya fahimci yarinyar nada hankali da nutsuwa da sanin ya kamata, uwa uba kuma ya yaba da tarbiyarta, ba kamar sauran ‘yan matan da suke son saba.
Murmushi yayi yana mai dafe kansa da yaji yana masa ciwo kad’an-kad’an, ya san hakan na faruwane sabida rashin ishash-shan bacci da kuma hayaniya domin shi baya son hayaniya ko kad’an shine dalilin da ya sama yake wuni a d’aki abinsa.
Maganin da ke aje gefan katifarsa ya d’auka yana mai bud’e robar faron da ya aje gabansa yasha maganin ya koma ya kwanta nan da nan kuwa bacci yayi awon gaba dashi. (ASUBA TA GARI YARIMA).
***
Washe gari tun da wuri kaman yanda ta saba tayi dukkan abin da ya kamata ace tayi kafin ta tafi, tayiwa iyayenta sallama ta kama hanya domin yau alhamis suna azumine bata tsaya bata lokacin neman abincin safe ba.
Ko da ta biyawa Zainab harta tafi sai sannan taga lokaci ashe har takwas ta kusa setting agogonta ya goce kenan? ta gaida Babah Tasallah ta fito a gurguje ta nufi gidan domin bata son yin late ko kad’an.
Bata tsaya ko ina ba sai cikin falon Yarima Fudhal tayi mamakin ganin falon fes dashi kamar jama’a basu zaunaba kai tsaye cikin d’akinsa ta nufa da sallamarta ta tura k’ofar d’akin tasa kai.
Yana kwance abinsa lullub’e da bargo ya takure waje guda kaman mai jin sanyi hakan yasa ta kashe AC dake ta famanyi ita kad’ai a d’akin har lokacin baccinsa ya ke hankalinsa kwance bai ma san ta shigo ba, ta wuce toilet tahau aikinta har ta gama bai farkaba ta fito tashare d’akin ta goge amma bai ta shiba ta wuce falon ta sake sharewa ta goge, ta lek’a d’akin taga baccinsa yake har lokacin ta dawo falo ta zauna, ganin baccin nashi bamai k’arewa bane yasa ta fito daga part d’insu zuwa cikin gidan.
Taje tayiwa Jakadiyya gaisuwa tare da Uwar soro, sannan ta wuce wajen Fulani Sokoto tana shiga cikin falon ta tadda Fulani zaune tare da Yarima Jalil da Jalila suna ta hiransu ta durk’usa ta gaishe su tare da yi musu gaisuwa, shi kuwa Yarima Jalil tun da tashiga ya kafeta da idanuwa ko k’iftawa ba yayi, ciki-ciki Fulani ta amsa ki dan taga ba ‘yar aikin wajenta bace? Oho.
Aynu ta mik’e ta fito daga b’angaren ta nufi wajen Fulani Bingel itama falon cike ta taddashi tayi musu gaisuwa suka amsa Fulani na fad’in.
“Kwana uku kenan ban ganki ba, ko k’unarce ta dameki?”.
“A’a k’una ta warke ma banajin dad’i ne dai, sai yau naji dama-dama”.
“Allah k’ara afuwa”.
“Amin”.
‘Yan d’akin suka amsa banda Aunty Sa’ida da take ta faman banka mata harara ita dai Aynu kanta na k’asa batama san tanayi ba.
Aunty Sadiya ta dubi Fulani da murmushi tana fad’in.
“Wannan ce Aynul-hayat d’in?”.
“Ehh “.
Fulani ta bata amsa, murmushi ta ya fad’ad’a a fuskarta tace.
“Kai amma taci sunan nata wallahi Hajiya”.
Ita ma Fulani murmushi tayi tana fad’in.
“Sosai kuwa”.
Aynu ta mik’e tana fad’in.
“Zan koma aiki”.
Ta fice daga d’akin suka bita da kallo, Aunty Sa’ida taja tsaki.
“Kai wallahi Aunty Sadiya da kayan haushi ki ke !, meye wani abin kyau anan yarinya bak’auya yar talakawa”.
“Ke ! banson jin wannan sha shancin anan kinji ko ina ruwanki to”.
Aunty Sa’ida taja tsaki, tare da cizon leb’e.
Fulani tace “Allah ya shiryeki Sa’ida meye wani abu ajikin talaka da har zai zama abin k’i, ka da insake jin wannan maganar abakin ki”.
Tafiya take kanta ak’asa tana wasa da yatsun hannunta sai ji tayi anjata gefe guda ta d’ago kai da sauri domin ganin waye?, ajiyar zuciya tayi tare fad’in.
“Zainab kin ban tsoro wallahi !”.
Zainab tayi murmushi taja hannunta gefe guda suka zauna tana fad’in.
“Ke kinsan abin da yafaru kuwa?”.
“A’a sai kin fad’a !”.
Aynu ta bata amsa, Zainab ta cigaba da fad’in.
“Gaskiya Aynu Yarima na sonki sosai, bakiga yanda hankalinsa ya tashi ba kwana biyu da baki zoba”.
Tsaki Aynu taja kad’an tare da fad’in.
“Amma ke kam kin fiye zato wallahi !, daga kinga ya shiga damuwa sai ki ce akai nane, mutuwafa akai musu kuma kinsan yanda suka shak’u da ita fa?”.
Zainab abin ya bata dariya sosai ta kanne tana fad’in.
“Ba wani wallahi, shifa ya nemeni na bashi kwatancen gidanku, kuma wallahi bakiga yanda hankalinsa ya tashi ba sanda nace masa baki da lafiya, sai da yaji ciwon kai kike sannan naga hankalinsa ya d’an kwanta ko bai zo gidan naku ba ne?”.
Aynu shiru tayi tana duban Zainab har sai da Zainab tad’an zungureta sannan ta dawo daga tuanin da take.
“Dama a wajenki yasan ciwon kai nake?”.
“Ehh mana, yazo gidan naku kenan?”.
“Ehh yazo da dare har da magun guna da kayan snack ya kawomin”.
Zainab ta fad’ad’a murmushinta cike da sonjin bayani .
“To mai yace da ke?, fad’amin dan Allah yace yana sonki ko?, ki ke wani b’oyemin !”.
“Sai kiyi kuma !, ke kam kina da matsala wallahi, ke nifa ko yace yana sona banjin zanso mutum irin sa”.
“Sabida me?”.
“Haka kawai”.
“Aynu kenan ke kam baky fahimta wallahi”.
“Ehh naji kinga mubar wannan maganar, kinsan kuwa Ya Sayyadi Umar sai faman zarya yake a gidanmu nifa har ya fara bani tsoro”.
“Meye na tsoro kuma?, ta tsuniyar gizo dai bata wuce k’ok’i, amma nidai nafi sonki da Yarima !”.
Zainab takai maganar tana dariya, Aynu ta mik’e tana turo baki wai ita adole fushi tayi ta wuce tabar Zainab nan zaune, ganin da Zainab tayi da gaske tafiya za tayi shine yasa ta mik’e itama ta bi bayanta da sauri tana kiran sunanta, amma Aynu ta toshe kunnuwanta tayi tafiyarta.
Ko da ta koma d’akin ya farka daga baccin yana zaune gefan katifarsa ya had’a kai da gwiwa, da sallama ta shiga d’akin ya d’ago da sauri yana dubanta, sai kuma ya kau da kai gefe guda kamar bayason ganinta a can k’asan zuciyarsa kuwa farin cikin ganinta ne fal ransa.
Har gabansa tazo ta durk’usa tana gaisha shi ya amsa can k’asan mak’oshi, Aynu ta d’an gyara zamanta sosai tana fad’in.
“Ya k’arin hak’uri kuma?, nagode sosa da kulawa, nazo na tadda kana bacci ne shine nak’i tashinka fatan banyi laifi ba?”.
Bai ko kalle taba bare ya nuna mata ya san dashi take magana, bata damu ba ta cigaba da fad’in.
“Ko kana buk’atar wani abu ne?”.
Shiru yayi na wani lokaci kafin yabud’e baki a hankali ya fara magana kamar wanda ake yiwa dole.
“Kije falo”.
Aynu tamik’e ta fito falo ta zauna tana jiran fitowarsa, ya shafe kusan mintuna talatin kafin ya fito falon sai faman tashin k’amshi yake cikin wani farin yadi mai shara-shara ana iya hango singlete d’insa ta ciki baisa hulaba illa taje sumarsa da yayi takwanta luf yaune karo na farko data ganshi cikin kayan hausawa tun dawowarsa.
Ya zauna gefan kusun yana duban Aynu, can ya kau da kansa ya mai dashi kan screeng d’in wayarsa da ke ringing.
SAIMA DARLING
Yagani bisa screeng d’in wayar tasa yasa hannu ya d’aga ahankali tare da sanyata a headfree.
Daga can b’an garen tanaji ya d’aga tahau fad’in.
“Haba Yarima !, ashe yanda na d’auke ka baka d’aukeniba!, mai yasa kake wulak’anta mai son kane?”.
“Sabida banayin abu a rufe”.
Ya bata amsa, cikin d’aga murya kad’an tace.
“Kamar ya kenan?”.
“Kamar yanda ki kaji na fad’a”.
“Ok amma mai yasa tun ran birthday d’inka baka nemeni ba, ni ina nan ina zaman jiran kiranka”.
“Na manta ne”.
Daga can b’arin Saima ajiyar zuciya tayi, domin ba kad’an takejin ciwon maganar da Yarima keyi mata ba duk da tanajin dad’in sautin muryarsa, ya katseta da fad’in.
“In kin gaji zan aje wayar?”.
“A’a kawai banajin dad’in reply d’in kane”.
“Time d’in breakfast d’ina yayi zaki iya kira anjima?”.
Ya kashe wayar ya ajiye gefe, duk maganar da yake idonsa na kan Aynu yana karantar yanayinra, ita kuwa kanta na k’asa tana wasa da wani d’an k’aramin zobe kod’ad’d’e dake hannunta.
Duk tanajin maganganun da suke amsar k’arshe daya bayar da kuma kashe wayar shi yafi komai bata mamaki da Yarima, amma data tuna waye shi?, sai mamakinta ya kau domin tasan zaiyi fiye da abin da yafi haka indai Yarima ne, b’an garan jiji da kai, girman kai da d’agawa ga shegen miskilanci da wulak’anci tun da take bata tab’a ganin mutum irin yarima ba abin nasa yayi yawa.
Ya katseta da fad’in.
“Yau wannan banjin zata zo?, inaga zan koreta aiki ne kawai !, jeki kawomin breakfast “.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRSAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITES ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
Wannan page d’in naki ne *Ashnurpyar* Nagartacciya Allah yabar zumunci amin.
14
BAYAN KWANA BIYAR
Zaune take can gefe daga inda yake yanata aikin danne dannan wayarsa, tafiya take sonyi amma ya hanata ko da fita cikin gidan ne.
“Zo nan Aynu”.
Taji muryarsa yana kiranta tamik’e ta k’arasa wajen da yake zaune nesa da shi kad’an.
“Matso mana”.
Ta d’an kuma matsawa kad’an, murmushi yayi yaga alamun bata da niyan zuwa kusa dashi mik’ewa yayi yazo daf da ita ya mik’a mata wayar hannunsa yana fad’in.
“Kalli ki gani”.
Aynu takai dubanta bisa screeng d’in wayarsa wata farar mace ta gani kyakykyawa ajin farko tana sanye cikin alkyabba pink data k’ara bayyanar da kyanta.
“Gimbiya Safiyya kenan”.
Ya fad’a yana mai duban fuskarta.
Murmushi tayi Aynu tare da furta.
“Amma ta had’u sosai tayi kyau wallahi”.
Yarima Fudhal ya kafeta da idanuwa yana dubanta kafin yad’anyi murmushi kad’an.
“Ita ce ake son had’ani aure da ita !, nan da 3days zatazo gidan nan, amma ni gaskiya bana sonta !”.
“To amma kuma kake ajiye hotonta?”.
“Meye ra’ayinki akanta?”.
Ya tambayeta ba tare daya bata amsar tambayar ta ba, Aynu ta dube shi da murmushi saman fuskarta.
“Ta dace da kai sosai kuwa”.
“Uhmmm haka ki kace?”.
“Ehh mana”.
“Wannan zab’in iyayena ne, amma ni bata daga cikin zab’ina”.
“Sai kabi zab’in iyayen naka ai, domin nasan basuyi maka zab’in tumun dare ba”.
Tsaki Yarima Fudhal yaja yana mai duban Aynu cike da takaicin amsar da take bashi, dubanta ya sakeyi a karo na biyu yana fad’in.
“Bawai na nuna miki bane domin ki bani shawara akan zab’in da zanbi, na nuna miki ne domin…….”.
Sai kuma yayi shiru maganar ta tsaya a mak’okwaronsa, dai-dai da shi gowar Saima ya d’auke dubansa daga kan Aynu ya karb’i wayarsa tare da fad’in.
“Tashi kije”.
Aynu ta mik’e da sauri ta fice dama ta takura da al’amarin Yarima sosai, Saima ta bi bayanta da kallon tuhuma, har sai da Aynu ta fice sannan ta dawo da kallonta kan Yarima tana fad’in
“Kana buk’atar wani abu ne?”.
“A’a jeki kawai”.
Ya bata amsa batare daya dubeta ba.
DARE
8:20PM
Da dare misalin k’arfe takwas da mintuna ashirin Aynu na zaune bisa tabarmar da tayi sallah gama cin abincinta kenan akai sallama tare da fad’in.
“Wai Aynu tazo inji Yarima”.
Dammm gabanta ya buga har sai da tad’an lumshe ido tare da karanto addu’a cikin ranta afili kuwa ta furta.
“Yarima kuma !, me zaiyimin da daren nan?”.
“A’a tashi kiji tunda kiga mutum ya tako har inda kike yazo yana da abun da yakawo shi mai muhimmanci ne musamman manyan mutane ai sai da babban dalili suke zuwa wajen mutum”.
Umma ta fad’a tana mai duban inda ‘yar tata take zaune duk da ba gani take ba.
Aynu tayi ajiyar zuciya gami da tashi daga cin abincin dama ta gama ta wanko hannu ta zari hijabi ta fice.
Yana tsaye jikin katangar gidan nasu hannunsa rik’e da wayarsa yana dannawa d’aya hannun kuma na cikin aljihun wandon jeans d’insa, aranta ta furta.
“Ko ina dai ba’a gajiya da sana’ar”.
Da sallama ta k’arasa wajensa Yarima ya amsa tare da fad’a d’a murmushinsa yana duban ta, Aynu tayi saurin yin k’asa da kanta sabida irin kallon da Yarima Fudhal yake ji fanta dashi idanuwanta bazasu iya d’auka ba.
Shiru ne ya ziyarci wajen kafin Yarima yayi k’arfin halin katse shirun da fad’in.
“Ke na keson aura Aynu !, zuciyata tafi aminta dake akan wacce iyayena suka zab’amin amma…”.
Sai kuma yayi shiru yana mai haska fuskarta da hasken wayarsa domin ganin yanayin ta, Aynu dai kanta yana k’asa amma zuciyarta na bugun uku-uku wanda ta rasa dalilin faruwar haka.
“Ko bakya so na?”.
Taji saukar muryarsa akaro na biyu yana tambayarta, maimakon ta bashi amsa kawai juya wa tayi tabar wajen ta shige gida ta barshi nan tsaye.
Yarima yabi bayanta da kallo ba tare da yayi yunk’urin da katar da ita ba yanaji zuciyarsa nayi masa zafi, tare da jin haushin abin da tayi masa.
***
Kwance yake bisa lallausar katifarsa sai faman juyi yake yana son yin bacci amma hakan ya gagare shi, tunanin abin da Aynu tayi masa d’azu shine yake damunsa, amma babban abin da yafi damunsa bai wuce jin tsoron kada Aynu tace bata son saba.
Lokacin ya jawo wayarsa ya duba agogo k’arfe biyu da kusan rabi, ya d’an ja tsaki tare da cigaba da danna wayar da alamu akwai abin da yake nema.
Can ya danna wata number tare da karawa akunnensa, sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan aka d’aga tsaki Yarima yaja tare da fad’in.
“Kai fa d’an rainin wayo ne Anwar !, mai kake nufi ?, da ba zakayi picking bane?”.
Cikin muryar bacci Anwar ya amsa da fad’in.
“Kai fa prince kafi kowa matsala wallahi ban da ni wa zaka kira da tsakad daren nan ya d’aga”.
Yarima Fudhal yaja dogon tsaki kamar ya yanke wayar sai kuma ya fasa yana fad’in.
“Kaga malam maganace mai muhimmanci ka tashi daga baccin”.
“Akan me?, fad’i maganarka kawai ina jinka”.
“Mene ma’anar idan ka furtawa mace kan sonta tayi tafiyarta batare data baka amsa ba?”.
Daga can b’angaren Anwar dariyace ta kwace masa har da rik’e ciki, ba k’aramin k’ok’ari yayi ba wajen saita kansa domin tambayar tazo masa a bazata da kuka mamakin wanda yayi tambayar, bai kai da baiwa Yarima amsa ba yaji ya katse wayar yasan dama za’ayi hakan, kira ya sakeyi harta katse Yarika yak’i dagawa sai da ya kira sau uku sannan ya d’aga batare da yayi magana ba.
Anwar cikin dariya ciki-ciki yahau fad’in.
“Am sorry Prince kawai naji mamakin tambayar da kayi min ne wallahi, da gaske soyayya kake son sanar dani ka fara ko kuwa me?”.
“A’a kawai inason jin amsar ne”.
Anwar yayi murmushi tare da fad’in.
“To kabari har gobe mayi magana mana”.
“A’a yanzu nake so shiyasama na kiraka ai, da naso har gobe ai sai goben zan neme ka”.
“Hakane, amma gaskiya a gani na duk macen da kace kana so tayi tafiyarta ta barka nan batare da amsa ba to d’ayan biyu ne ko kunyar baka amsa take ji ko kuma bata son ka…”.
Kafin ya kai da k’arasa maganar Yarima Fudhal ya katse wayar ya wullata can k’arshen katifarsa tare da yin tsaki, sai kuma yamik’e ya zauna maganar Anwar nayi masa yawo akai.
“Aynu kunyata take ji, ko kuma so nane batayi ?”.
Kai ya girgiza yayin da zuciyarsa ta tsinke tsoro ya ziyarce shi, sai ya samu kansa da fad’in.
“Allah yasa kunyace ta hana ta bani reply !”.
Hhhhhhh to fa !, su Yarima Fudhal anshiga taskun soyayya, to amma aganinku Aynu zata so Yarima Fudhal kuwa?.
Nabar muku wannan amsar Reader.
Kuyu hkr da wannan page d’in babu yawa, nagode sosai masoyana kuna raina koyaushe.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATIONS®
15
8:00am
Zaune Anwar yake gefen kusun yana duban Yarima Fudhal cike da tsokana yake fad’in.
“Amma dai kowa ya ganka yaga wanda yajik’e da mayen so, amma kace min kai ba soyayya kake ba?”.
Yarima dake kwance gefe ya dora hannunsa na dama bisa fuskarsa kamar bacci ko motsi baiyi ba, bare ya kula da maganar da Anwar yake masa.
Aynu ce ta fito daga cikin bedroom hannunta rik’e da moopa ta d’an risina tana fad’in.
“Na gama zan gyara nan”.
Yarima ya mik’e ba tare daya dubeta ba ya wuce cikin d’akin yana fad’in.
“Sai ka ta so ko”.
Anwar yabi Yarima da kallo kafin ya dawo da dubansa kan Aynu yana fad’in.
“Mene sunanki”.
“AYNU”.
Ta bashi amsa kai ya gyad’a tare dayin murmushi yana fad’in.
“Nice name, a wacce unguwa kike?”.
Yarima ne ya banko labulan d’akin ya fito cike da b’acin rai, kallon daya watsawa Aynu shine yasa ta shan jinin jikinta tayi k’asa da kai ba tare data baiwa Anwar amsa ba.
Anwar ya sanya dariya mai sauti tare da mik’ewa yabi bayan Yarima cikin d’akin yana fad’in.
“Abin da nayi zato ya tabbata Prince, wai me yasa kake b’oyemin ne?, tun da nazo nake karantar yanayin ka akan yarinyar nan”.
“Sabida kamai da zancena gist mana !, kasan ni bana wasa a cikin al’amura na”.
“Ehh to zancen wasa ya wuce, amma ka da dai kacemin wannan Yarinyar kake so?, domin naga kishinta k’arar bisa fuskarka”.
“Ehh ita nake so !, wani abun ne?”.
“A’a amma fa yarinyar tayi wallahi, duk da dai kanta ba’awaye yake ba”.
“Ehh naji koma dai mene, amma kasan wani abu ?”.
“Menene fad’amin inajinka”.
Saima ce ta shigo da Sallama tare da fad’in.
“Breakfast d’inka yayi ready”.
“Ok ina zuwa”.
Ta juya tafice, Anwar ya dubi Yarima tare da fad’in.
“Ina jinka”.
“So nake kajawo hankalin wata yarinya, ma’ana kayi soyayya da ita”.
“Ban fahimce kaba?”.
“Ok abin da nake nufi, inaso kasa wata yarinya ta soka, ni so nake hankalinta ya tashi daga kaina ya koma kanka, Yarinyar tana so nane hakan na neman jawomin matsala “.
“Wacce matsala kenan?, amma kuma wacce yarinya ce?”.
Yarima Fudhal yayi murmushi tare da kau da kansa gefe.
“SAIMA ‘yar gidan Alhaji Buba, ita nake so kayi soyayya da ita, so nake kamar yanda ta furta tana sona inaso ta furta da bakinta bata so na !”.
“Amma mai yasa ka yanke wannan hukuncin, Yarinya kamar Saima mai tsada tace tana sonka amma kace a’a?”.
“Yes bana ra’ayin ‘yan mata irin tane, jiya da Yamma Mai martaba ya kira ni ya sanarmin Baban ta Alhaji Buba da kansa yazo nan wajen Mai Martaba akan yana so ya had’a zuri’a da mu, wato dai yana so ya auramin ‘yarsa, bayan kuma anmin zab’in Safiyya, amma kasan amsar da Mai Martaba ya bawa mahaifinta?”.
“A’a sa ka fad’a”.
“Cewa yayi ai namiji mijin mata hud’u ne, babu komai sai a had’amin mata biyu in aura aini Yarima ne kuma magajin gobe, wannan dalilin yasa na kasa daure zuciyata har sai da naje na furtawa Aynu ina sonta, sai dai bata bani amsa ba har yanzu, hakan namin ciwo sosai jiya ko bacci kasa yi nayi”.
“To ka had’asu duka ukun mana”.
“Bana ra’ayin hakan, kawai ka yimin abin da nagaya maka”.
“To amma idan Saima ta dawo kaina, ita Safiyyan ya zakayi da ita?”.
“Banyi tunani akan taba, sai na gama da wannan”.
“Amma kuma idan ta furta bata sonka ni take so, rabuwa zanyi da ita kome?, dan nima gaskiya ba lallai ya kasance in so ta ba”.
“Wannan ya rage naka karabu da ita ko ka aure ta, inkaso zaka iya son ta bai dame ni ba, amma nidai buk’ata ta tace bata so na”.
Anwar ajiyar zuciya yasaki mai k’arfi yana mai kallon Yarima cike da tunanin al’amarinsa, shikam yasan tun yana yaro tare suka taso da Yarima amma har yanzu ya gaza fahimtar halayyar Yarima, shi wani irin murd’ad’d’an mutum ne, sai ka kasa gane inda yasanya gaba.
“Kayi shiru ko kana buk’atar lokaci ne?”.
“A’a zanyi yanda kace, amma kana ganin ita wannan Yarinyar zata so ka?”.
“Ban dai sani ba?, amma shirun ta na bani tsoro”.
Anwar ya girgiza kai da murmushi saman fuskarsa yana fad’in.
“Babu komai Allah ya shige mana gaba”.
“Amin”.
Suka mik’e suka fito zuwa falon, komai ready kai tsaye wajen abinci suka nufa sukayi breakfast, suna ci suna tattaunawa domin falon babu kowa sai su kad’ai.
Zaune take bisa da kalin dake farfajiyar Shamaki babu kowa wajen sai ita, tayi zurfi cikin tunani domin ba tasan ma Yarima Fudhal na tsaye bisa kanta ba, ya kira sunanta yafi sau a k’irga amma bata amsa ba.
Hakan ya sashi zama kusa da ita tare da sanya hannu yad’an girgiza kafad’arta, firgigit ta farka tare da mik’ewa da sauri tana duban Yarima, Yarima Fudhal murmushi yayi mata yace.
“Zauna mana”.
Aynu ta koma ta zauna amma duk ata kure take jinta.
“Me kike tunani?”.
Ya tambayeta Aynu tayi k’asa da kanta tana duban tafin hannunta.
“Babu komai”.
Ta bashi amsa, girgiza kai yayi alamun bai yadda ba.
“Bana son k’arya kodai tunani na kike?”.
“A’a !”.
Ta kuma bashi amsa, Yarima yayi ajiyar zuciya tare da kafeta da idanuwa har lokacin murmushin fuskarsa bai d’aukeba.
“Aynul-hayat !”.
Ya kira sunanta da wata irin murya wadda tasanya tsigar jikin Aynu tashi, har tad’an rintse ido kad’an, hannunsa ya sanya bisa tafin hannunta yarik’e, ya cigaba da fad’in.
“Ki fad’amin mana, ko kunyata kike ji?”.
Aynu ta girgiza kai, tana mai k’ok’arin janye hannunta amma yarik’e kam.
“Bafa zan cika ki ba, har sai kin bani amsar tambayar da nake miki”.
Aynu dai tayi shiru sai motsa bakinta take amma kuma maganar tak’i fitowa, su Zainab ta hango suna nufo wajen kusan su biyar da dukkan alamu sungama aikin sune sunzo su huta domim duk a wajen suke hutawa.
Ta kafe su da idanuwa tsoro ya k’ara kama ta, jikinta har wani rawa yake Yarima ya juya yana duban inda take kallo murmushi yayi yana fad’in.
“Indai baki bani amsa ba sai dai su taddamu ahaka, danni kinsan babu ruwana !”.
Aynu tahau girgiza kai kawai, bai zata ba sai jin saukar ruwa yayi akan hannunsa ya kalleta da sauri yana mai sanya hannu ya d’ago fusakarta, afili ya furta.
“Kuka kuma?, Yi hak’uri share hawayen kada suzo su gani wasa nake maki fa n”.
Ya cika mata hannun yana murmushi, ya mik’e tsaye ya zuba hannuwansa cikin aljihun wandonsa yana kallon yanda taketa k’ok’arin share hawayen amma wasu na zubowa, sosai abin yake burgeshi sai yaji dama su dauwama haka yana kallonta.
K’arasowar su Zainab ce tasan yashi barin wajen yana fad’in.
“Zaki zo kisame ni ne”.
Zainab tak’arasa wajen Aynu tana fad’in.
“Lafiya Aynu?”.
Harara ta sakar mata tare da juyar da kai gefe, sosai take jin zafin rik’e hannunta da Yarima yayi.
“Wai ke mene yake damunki ne?”.
“Babu komai”.
Ta bawa Zainab amsa, Zainab tace.
“A’a wallahi nasan da wani abun, yanzufa naga Yarima yabar wajen nan, wannan ruwan hawayen kuma fa?”.
Tsaki Aynu taja tana fad’in.
“Ke kam kin shiga uku da tambaya”.
“Ehhh naji, ai ni dake iya wuya muna tare”.
Aynu tayi murmushi ta juyo ta kalli Zainab tana mai bata labarin abin da ya faru, ajiyar zuciya Zainab tayi tare da fad’in.
“To ke mene ra’ayinki akan Yarima Fudhal, son shi ne ba kyayi ?”.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A (QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
16
Hello makaranta
Hope na sameku lafiya?
Ya komai, ya kowa?
Kuyi hak’uri dan Allah zaku dinga ganin post d’ina ko yaushe insha Allah amma ban da ranar Friday sabida wani dalili.
Nagode sosai da sosai.
“wai ni ya zanyi ne Zainab !, Yarima ya matsamin akan lallai sai yaji ina sonsa ko bana sonsa?”.
“To wai ke mene ra’ayinki akansa ne !, nima kaina na kasa gane maki ko son sane bakyayi?”.
Aynu ta girgiza kai cike da jimami.
“Nima har yanzu nakasa tan-tancewa ina sonsa ko bana sonsa, abin da kawai nasani ina jin tsoro ne sosai?”.
“Tsoson me kuma?”.
“Yarima yafi k’arfina Zainab !, mai Yarima zaiyi da ni?, ‘yar miskinai kuma baiwarsa niba ‘yar kowa bace Zainab !, Yarima yana tak’ama da kud’i da mulki mafiya yawan al’ummarmu na yanzu musamman masu kud’i da masu mulki sunfi son AURE KWARYA TABI KWARYA, ina jin tsoron abin da zaije ya dawo ne”.
Zainab dogon tsaki taja cike da takaicin maganganun da Aynu ta fad’a.
“Toke mene zai dame ki, bafa ke kika ce kina son saba shine yace yana sonki, ni dai shawarata agare ki kada ki bari damarki ta wuce ki, kiyi ‘kok’arin yin amfani da damarki, ki sanarwa Yarima kina sonsa, sauran lamarin ki barwa Allah komai kiyi ta addu’a da yardar Allah komai zaizo cikin sauk’i”.
Zainab ta nisa tana mai kallon Aynu dake share kwallar dake k’ok’arin zubo mata bisa fuskarta ta cigaba da fad’in.
“Aynu kina son Yarima !, ki yarda da hakan kuma, kawai tsoro da fargaba ne sukafi tasiri a zuciyarki shiyasa kika kasa fahimtar cewa kina son sa !”.
Aynu murmushi tayi tana mai duban Zainab, Zainab kai ta gyad’a mata itama fuskarta d’auke da murmushi ta dafa kafad’ar Aynu tana fad’in.
“Zan tayaki da addu’a sosai, amma kada ki bari Yarima ya sub’uce miki, domin ke kikafi dacewa da Yarima Fudhal”.
Sosai Aynu taji dad’in shawaran Zainab agareta, rik’o hannun Zainab tayi tana fad’in.
“Nagode ! Nagode !! Nagode !!! Zainab Allah yabar mutare”.
“Amin”.
Shela aka hauyi a cikin gidan na cewar tawagar Gimbiya Safiya ta sauka aje a tarbota.
Da sauri su Aynu suka mik’e suka nufi waje.
Jerin motoci goma ne sukai parking a k’ofar gidan, wani dogari ya taka da gudu yaje ya bud’e k’ofar motar, cike da tak’ama da izza Gimbiya Safiyya ta sako k’afa ta fito, mace doguwa fara kyakykyawa ajin farko tana sanye da farar alkyabba wacce ta rufe dukkan jikinta, inbanda hannunta da k’afarta sune kawai a waje, takalimin k’afarta mai gashine shima fari iya had’uwa ta had’u k’arshe.
Aynu sai taga tafi kyau afili ma fiye da a hoto data ganta, take taji wani abu ya ziyarci zuciyarta taji ta raina kanta sosai domin babu abin da zata nunawa Gimbiya Safiyya indai kyaune zai sa aso mutum to tabbas da Yarima baice yana sonta ba, domin Gimbiya Safiyya kyakykyawace ta k’arshe.
Tana fitowa aka hau yi mata ruwan fure tare da tawagarta bayi mata biyar ke biye da ita, kai tsaye wajen Mai Martaba dake tsaye ta nufa tayi gaisuwa, sannan muka rufa mata baya zuwa cikin gidan.
Kai tsaye muka nufi b’angaren Fulani Sokoto da ita, tana tafe anayi mata ruwan fure tare da kirari har zuwa cikin falon Fulani Sokoto.
Yarima Jalil da Jalila duk suna zaune falon tare d ma’aikatan Fulani, muna shiga Fulani ta fito daga cikin d’akinta tana yiwa Gimbiya Safiyya sannu da zuwa, rungumeta Gimbiya Safiyya tayi tare da yinn kiss d’in kuncinta tana fad’in.
” I Miss u my Mom !”.
Ta juya kan Yarima Jalil shima abin da tayiwa Fulani haka tayi masa, sannan ta juya kan Jalila itama haka tayi mata, mudai sakar baki mukayi muna kallon ikon Allah dan wannan ya zame mana saban al’amari aganinmu idan zata rungumi Fulani da Jalila ai bai kamata ta rungumi Yarima Jalil ba?.
Neman guri tayi ta zauna tana fad’in.
“Ku bamu waje ko?”.
Duk kanmu muka mik’e muka fito zuwa waje, kowa ya kama gabansa, ni da Zainab neman waje mukayi muka zauna muna hira, bamu jima ba akayi kiran Zainab a b’angaren Fulani Bingel, ta barni nan zaune gashi ni inba Zainab ba bana shiga harkar kowa nan nayi ta zaune har zaman ya isheni na mik’e nima na nufi b’angaren Fulani Bingel tunanina inje intaya Zainab aikin da take, ko ba komai yafi zaman da nake ni kad’ai.
Ina tafe ina ‘yan wak’e-wak’ena sai ji nayi anjawo hannuna cike da tsoro na bud’e baki zanyi ihu yasa hannunsa ya rufan bakin yana fad’in.
“Sarkin tsoro !”.
Fuskarsa d’auke da murmushi, ajiyar zuciya na saki tare dayin k’asa da kaina, Yarima Fudhal ya tsareta da idanuwa yana fad’in.
“Yau dai kinga kishiyarki ko?”.
Aynu batasan sanda ta jefeshi da wat uwar harara ba, Yarima yayi murmushi yana mai cigaba da fad’in.
“Mene na kishi a kaina kuma?, bayan bakya sona?”.
Sai lokacin Aynu ta lura da abin da tayi kunya ta rufeta sosai, murmushi yayi mai sauti.
“To yau dai sai kin fad’amin kina sona ko bakya so na?”.
Aynu tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta.
“Baki ce komai ba?, ko bakya so na?”.
Ta girgiza kai alamun a’a.
“To kina so na?”.
Ta gyad’a kai alamun ehhh, tana mai rufe fuskarta da tafin hannunta, murmushin dake kan fuskar Yarima ya sake fad’ad’a, sosai yake jin wani sanyin dad’i na ratsa dukkan sassan jikinsa, har yanajin kamar ya rungumeta tsabar farin ciki.
“AYNU…!”.
Ya kira sunanta da wata irin murya, bata d’ago kanta ba illa amsawa da tayi kawai tana jiran taji mai zai ce.
BAN HAK’URI
Ku k’ara hak’uri dani dai, naso nayi muku typng mai yawa sakamakon jiya banyi muku post ba, sai dai Allah bai yarjemin ba wlh bbu chaji awayana yanzu kuma kunata jirana shiyasa na k’ok’arta nayi muku wannan zuwa anjima insha Allahu indai na samu chaji zaku sake jina nagode sosai da kulawa.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jeebour.
17
Ya cigaba da fad’in.
“Tabbas naji dad’i sosai da jin amsar data fito daga bakin ki, yau rana ce ta musamman agare ni da bazan tab’a mancewa da ita”.
Yayi shiru yana mai cigaba da kallonta, har lokacin Aynu bata iya d’ago kanta ba, sanya hannu yayi ya d’ago kan nata yana mai duban fuskarta cike da so da k’auna, Aynu ta rintse ido domin bata iya juran kallonsa, sakin fuskarta yayi ya ce.
“Hak’ik’a kin bani farin ciki wanda nake fatan d’orewarsa har aba da !”.
“Bari inje Mai Martaba na kira na, zan zo yau da dare gidan ku !”.
Kai kawai Aynu ta gyad’a masa ya tsaya yana kallonta kamar kada ya tafi, da k’yar dai ya juya yabar wajen.
Aynu tabi bayansa da kallo tafiyarsa kanta abar burgewa domim Yarima idan yana tafiya da gaba d’ayan jikinsa yake tafiya, gyaran muryar da ta jine ya sanyata juyawa da sauri domim ganin waye?.
Yarima Jalil ne tsaye yana binta da kallo ya nad’e hannunsa ak’irjinsa fuskarsa babu yabo babu fallasa.
Aynu tad’an risina ta gaishe shi, ya amsa tare da fad’in.
“Ya had’u ko Yayan nawa?”.
Yayi maganar yana mai d’aga mata gira, murmushi Aynu tayi ba tare data iya cewa dashi komai ba.
“Anyi masa mata to !, dama kin barshi kindawo wajena Beauty”.
Aynu dai batace komai ba, ya d’an matso kad’an zuwa wajenta adai-dai kunnenta ya rad’a mata.
“Dani kika fi dacewa, nine zan baki dukkan k’auna !, duk naji abin da yake fad’a miki ki watsar da batunsa, ki fuskanci batuna domin dai ga matar da zai aura nan, bayan ita kuma akwai wacce akayi magana su biyu zai aura ya angwance !”.
Ya k’arashe maganar cikin dariya ciki-ciki.
Aynu da sauri ta dubeshi da kallon tuhuma tana son tabbatar da maganarsa, gira ya d’aga mata tare da wani guntun murmushi a saman fuskarsa.
“Ko baki yarda dani bani?”.
“A’a na yarda mana, amma ni nace maka akwai wani abu atsakanin mune ?”.
“Baki fad’aba amma idanuwanku sun shaida hakan, kiyi tunani sosai akan Fudhal dani Jalil waye zaifi dacewa da rayuwarki ?, indai har zaki yarda da soyayyata zanbar dukkan wani abu mai muni da nake aikatawa kuma zan rayu dake ke d’aya babu wata “.
Yayi shiru yana karantar yanayinta kafin yad’an cije leb’e ya cigaba da magana.
“Shin aganinki wanda zai auri mace kamar Safiyya zaiyi tunanin kuma auren wata ‘ya mace ne, ki tuna bayan ita akwai wata, itama kuma ba baya ba wajen kyau da kud’i da komai n”.
“Zan barki kiyi tunani akan hakan duk shawaran da kika yanke zaki iya fad’amin”.
Ya juya yabar Aynu da jijiyoyin jikinta baki d’aya sun tsinke tsoro ya ziyarci zuciyarta sosai, take taji zuciyarta nayi mata zafi wajen Zainab d’in da bataje ba kenan tayi tafiyarya gida aganinta zatafi samun nutusuwa da kwanciyar hankali idan ta koma gidan.
Sai dai ba anan gizo yake sak’arba ko da ta koma gida kasa aikata komai tayi inbanda aikin tunani babu abin da take yi, aranta tanaji Yarima Fudhal ya cuceta, duk da k’asan zuciyarta ya kasa gasgata hakan.
Ummanta tayi tambayar duniya ko akwai abin da yake damunta amma Aynu tace babu komai, daga k’arshe da taga Umman ta damu sai tace kanta ne yake ciwo tasha magani tayi kwanciyarta.
***
Haka Aynu ta kwana bacci sai dai b’arawo, amma a cikin daren sai da tasamawa kanta mafita, duk da wani b’angaren na zuciyarta ya kasa yarda da hukuncin data yankewa kanta.
Washe gari kuwa ko da takoma aiki abin da ya kaita kawai tayi, kuma daman ta tarad su Yarima sun fita tun asuba hakan ba k’aramin dad’i yayi mata ba, amma tana gama aikin da zatayi neman guri tayi falo ta zauna tare da fuskantar wani k’aton frame na hoton Yarima Fudhal da aka d’aukeshi gaba d’ayansa yana sanye da farar coat da wando fari hatta takalmi da agogon hannunsa fari ne, sosa Aynu takeson hoton tun ba yanzuba haka kawai takanji dad’in ta zauna tana kallon hoton domin kamar kace Yarima ya amsa hoton ya d’auku sosai.
11:30am.
Basu dawo ba sai k’arfe sha d’aya da mintuna ya turo k’ofar d’akin ya shigo cike da sallama, Aynu bama tasan ya shigo ba domin tayi zurfi cikin tunani, wani dad’i yaji alokacin da idonsa yakai inda Aynu take kallo murmushi yad’anyi tare da k’arasawa wajen da take zaune ya dafa kafad’arta.
A firgice ta d’ago kai sai kuma ta saki ajiyar zuciya ganin Yarima.
Turo k’ofar da akaine ya sasu juyawa baki d’ayansu, Gimbiya Safiyya ce ta shigo cikin takun k’asaitar nata tabisu da wani kallo wanda Aynu takasa tan-tance kona menene?.
“Wace wannan?”.
Ta jefawa Yarima tambaya, Yarima Fudhal ya nemi guri ya zauna batare daya bata amsaba, sai ma fad’i daya hauyi.
‘kawomin breakfast Aynu”.
“A’a ta barshi ai tafe muke da shi, Larai…!”.
Gimbiya Safiyya ta kira wata mai aiki dake bakin k’ofa, Larai ta shigo hannunta d’auke da tire ta ajiye gaban Gimbiya Safiyya data nemi waje kusa da Yarima Fudhal ta zauna.
Larai ta juya ta fice, Gimbiya Safiyya ta d’auki Apple ta kai masa baki Yarima ya kau da kansa gefe yana fad’in.
“Tea nake buk’ata Aynu zoki zuba min”.
Gimbiya Safiyya ta kaiwa Aynu wani kallon wulak’anci tana fad’in.
“Au dama baki fita ba, fita ki bamu waje !”.
“Babu inda zata domin kafin zuwanki ita ke ci da ni”.
“To yanzu tun da nazo ba sai ta huta ba?”.
Takai maganar tana hararar Aynu, Aynu tayi k’asa da kanta ba tare da tace komai ba.
“Zo ki serving d’ina”.
Ya sakewa Aynu magana, Aynu tamik’e tazo tayi serving komai ta koma gefe ta zauna.
Gimbiya Safiyya tad’auki kofin tea d’in takai masa bakin wai zata ci da shi ya d’auke kansa tare da fad’in.
“Na gaya miki bana buk’ata”.
“Amma kasan aure zamuyi?, mene danna ci da kai tun yanzu ai treaning nake yi”.
Yarima tsaki yaja yana mai kau da kansa gefe cike da takaici, Gimbiya Safiyya ta sake duban Aynu cike da masifa tana fad’in.
“Wai ke wacce irin macace akace ki fita ko?”.
Aynu tamik’e ta fice aranta tana jin zafin wulak’ancin da Gimbiya ke yi mata, amma ak’asan zuciyarta sai taji babu komai domin ita ‘yar aiki ce kuma baiwa ita kuwa ‘ya ce ga Sarki guda.
Yarima Fudhal bai yi magana ba har Aynu ta fice tana goge kwallar dake gefan idonta, ransa idan yayi dubu yab’aci take yamik’e ya fito shima yabar mata d’akin.
Ran Gimbiya yab’aci sosai ta fito itama ta nufi b’angaren Fulani Sokoto tana kuka wai Yarima Fudhal yafifita Baiwa akanta ?.
Rarrashinta Fulani tayi tare da fad’in.
“Ki kwantar da hankalinki zan san abinyi dani yake zancen !”.
Jalila dake zaune gefe tsaki taja tace.
“Kema dai Aunty Safiyya kin manta waye Fudhal ne?, tun da kin taka kinje wajensa ai kuwa sai abin da kika gani !, shi Allah na tuba baka shiga harkarsa ba ma ya wulak’anta ka bare kuma ka shiga….!”.
“Ke gidanku nace !, rufemin baki dan taje wajensa meye a ciki?, ina nan da kwanaki kad’an mijin tane?”.
Cewar Fulani kenan cike da fad’a, Jalila tsaki taja tana k’uk’uni.
“Nifa Momy ba haka nake nufi ba, Allah ya baku hak’uri”.
Ta fad’a tana mai mik’ewa ta fice daga cikin d’akin.
Yarima Fudhal na fitowa neman Aynu yahauyi lungu-lungu amma bai ganta ba, sai da ya gaji da nema ya tsaya jikin windown wani d’aki sai yadinga jiyo shash-shek’ar kuka bayan d’akin, zaga yawa yayi domin ganin waye yake kukan?, Aynu ya gani ta had’a kai da gwiwa a hankali ya taka zuwa wajen tare da kiran sunanta yana mai kama kafad’unta ya d’ago ta, fuskarnan shab’e-shab’e da hawaye hannu yasa yahau share mata yana fad’in.
“Yi hak’uri kinji !, mene abin kuka kuma?”.
Aynu ta janye jikinta daga nasa tana yi masa wani mugun kallo ta juya masa baya, k’ara juyo da ita yayi ta kuma juyawa masa baya ganin da yayi tana k’ok’arin barin wajen ne yasa shi shan gabanta yana fad’in.
“Wai lafiya kuwa?”.
Tsaki tad’anja tana mai ratsewa ta gefansa tabarshi nan tsaye bin bayanta yayi da kallo, zuciyarsa na k’una akan abin da tayi masa yaso binta amma kuma sai ya fasa.
D’aki ya koma ya kwanta yana tunanin laifin da yayi mata har tayi fushi dashi, jiya dai sun rabu lafiya amma kuma yau tana fushi dashi kodan yace zaije bai jeba?.
Sai kuma tunanin abin da yafaru d’azu ya fad’o masa arai.
“Safiyya ce tajawo komai kenan?”.
Ya fad’a cikin ransa mik’ewa yayi zaune tare da fad’in.
“May be kishi ne !, zanyi k’ok’arin shawo kanta”.
Abin da yafurta afili kenan ya mik’e ya fito daga d’akin zuwa waje, ya sake dubawa amma bai gantaba daga k’arshe ya tambayi Jakadiyya tace masa ta tafi gida tun d’azu, tsaki yaja aransa ya nufi b’angaren Mahaifiyarsa.
Wunin ranar haka Yarima yayi shi sukuku da shi, b’angaren Aynu ma haka abin yake.
Ya so ya bari har dare yaje wajenta ko yasamu nutsuwa cikin ransa, amma kuma ya kasa daurewa zuciyarsa nata faman azalzalarsa k’arfe hud’u da mintuna a shirin yayi parking motarsa bakin layin gidansu Aynu.
Ya fito ya kulle motar ya taka har zuwa k’ofar gidan tun kafin ya k’arasa ya hango ta tsaye da wani zuciyarsa sai da ta buga yayi k’arfin halin k’arasawa ya tsaya nesa dasu kad’an.
Yan da suke hiran Aynu na d’an murnushi abin sosai yake sosa ran Yarima, ji yayi kaman yaje ya shak’e wanda suke tare, amma dai ya daure ya cigaba da tsaiwa har sai da wani yaro yazo wucewa yace masa ya kirawo masa Aynu.
Aynu na sane dashi tunfarkon shigowarsa layin ta ganshi amma ta kau da kai suka cigaba da hirar da suke da Yasayyadi Umar.
“Aynu kije inji wancan mutumin”.
Yaron ya fad’a yana mai nuna Yarima Fudhal.
Tare suka d’ago ita da Yasayyadi suka dubi inda Yarima yake tsaye ya had’e girar sama data k’asa.
“Waye wancan d’in?”.
Ya Sayyadi ya jefa mata tambayar yana mai kallonta, Aynu ta k’ak’alo murmushi tana fad’in.
“Shine wanda nake yiwa aiki ai !, Yarima Fudhal ne”.
Kai kawai Ya Sayyadi ya gyad’a yana fad’in.
“Jeki dawo to zan jiraki domin akwai maganar da zamuyi”.
“To”.
Abin da tace kenan, ta taka zuwa wajen Yarima wanda tun tawowarta ya kafeta da idanuwa yana kallonta, da sallama tak’arasa wajen tana mai kau da kanta gefe, mai makon ya amsa sallamar sai cewa yayi.
“Waye wancan?”.
“Ya Sayyadi Umar kenan, malamin islamiyyar mune”.
Ta bashi amsa, Yarima ya cize leb’ansa na k’asa yana mai cigaba da fad’in.
“Anan ma Islamiyyar kuke kenan?”.
“A’a yazo duba Ummata ne”.
“Dubiyar anan waje ake yinta?”.
“A’a rakoshi nayi zuwa waje”.
“Kinsan tsayin lokacin danayi anan, nasan kuma kafin zuwana may be kun jima tsaye”.
“Ehh nasan kazo mana !”.
Da sauri Yarima Fudhal ya dubeta jin amsar k’arshe data bashi, cikin kasa lallliyar murya ya furta.
“Meke faruwa ne Aynu?”.
“Babu komai n, yi hak’uri na barshi tsaye bari inkoma”.
Bata jira mai zai ce ba ta juya kawai ta barshi nan tsaye, Yarima binta yayi da kallo yama rasa mai ya kamata yayi.
Ya bita ko ya rabu da ita ne????.
Hello makaranta
Sai dai fa kuyi hak’uri dani domin alk’alamina bazai iya zayyane muku irin son da Yarima Fudhal ke yiwa Aynul-hayat ba, kamar yanda girman kai da jiji da kai ba zasu bar Yarima Baiyyanawa Aynu irin son da yake yi mata.
Kawai sai dai ku ayyana irin son a cikin ranku….!.
ASHA KARATU LAFIYA.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jibour.
18
Yana cikin wannan tunanin wayarsa dake hannunsa tayi ringing, ya d’aga yakara a kunnensa ba tare daya duba yaga waye mai kiran ba.
“Haba My…! Abbana yazo har gida anyi magana fa !, amma ko ka kirani mu tattauna batun auren mu…!”.
Cire wayar yayi daga kunnensa ya duba screen d’in wayar sunan Saima ne d’od’ar bisa screen d’in, guntun tsaki yaja tare da mai da wayar kunnansa, ta cigaba da fad’in.
“Duk da ance mu biyu zaka had’amu zan amince ne kawai sabida son da nake maka…. !”.
Cikin b’acin rai ya katse ta yana yana fad’in.
“Duk naji amma ki sani duka ku biyun babu wacce nakeso aciki, zaki iya kashe wayar !”.
Ya fad’a yana mai kashe wayar ya jefata cikin aljihun wandonsa, ya mai da kallonsa kansu Aynu dake tsaye har lokacin suna hira.
Tsaki yaja ya juya kawai ya bar wajen zuciyarsa cike da sak’e-sak’e da kokwanto kala-kala, tare da dumbin tunanin nemawa kansa mafita tunkafin lokaci yak’ure masa.
Saima kuwa yana kashe wayar hawaye ya fara zarya bisa kuncinta zuciyarta na zafi da k’una, a haka Momynta tazo ta tadda ita, dafa kafad’arta tayi tana fad’in.
“Haba Saima !, har zuwa yaushe ne zaki samawa kanki mafita abisa muguwar damuwar dakika d’orawa kanki !, nad’auka damuwarki ta kau tunda har iyaye sunyi magana ?”.
Saima ta fad’a bisa cinyar Momynta da ta zauna kusa da ita cikin kuka ta hau fad’in.
“Momy Yarima Fudhal ne !”.
Tsaki Momyn tayi tana fad’in.
“Me kuma yayi miki yanzu?”.
“Yace duka mu biyun wai baya sonmu !, Momy ji nake kamar zan iya mutuwa wallahi indai har na rasa Fudhal arayuwata !”.
A jiyar zuciya Momyn tayi tana mai d’ago da ‘yar tata zaune, ta kalli fuskarta sosai.
“Haba Saima kamar ba ‘ya mace ba, kamarki ki zauna kinayi namiji kuka !, ni anawa ganin tun da har ya furta baya sonku ki hak’ura da auren sa kawai, ki danne zuciyarki akan Yarima ki barshi bari na har abada !”.
“Momy taya hakan zai yiyu?, ina son Yarima sosai wallahi Momy ki taimake ni dan Allah !”.
“Bani da wani taimako da zan iya yi miki wanda ya wuce addu’a, sannan zan sanar dake wani abu da baki saniba arayuwa, Saima..! akan ki auri namijin da baya sonki ke kike sonshi, gara ki auri wanda yake sonki ko da bakya sonsa, domin shi zai iya jure dukkan abin da zakiyi masa na b’acin rai, sab’anin wanda kike so, kuma ba lallai auren yaje ko inaba kuskure kad’an zaki zai iya rabuwa dake rabuwa ta har aba da !”.
Saima zaune tayi tana sauraren Momynta kawai, lokaci-lokaci tana share hawayen fuskarta, wayarta dake kusa da Momyn tayi ringin Momy ta d’auka ta kara a kunnensa sabida ganin number da tayi babu suna, daga can b’arin aka hau fad’in.
“Please Saima gani nan tsaye cikin gidanku !, dan Allah yau dai kifito ko gaisawa muyi kada ki shanyani kamar ko yaushe”.
Momy ta kashe wayar tana mai kallon Saima tare da mik’a mata wayar tana tambayarta.
“Waye wannan?”.
Saima ta b’ata rai kafin ta bata amsa.
“Momy wanine wallahi duk yabi ya takuramin”.
“Har tsawon wane lokaci ya d’auka yana zuwa gidan nan?”.
“Inajin dai zuwansa uku”.
“Amma shine kike wulak’anta mutum Saima !, duk wanda yace yana sonka arayuwa ya gama maka komai fa !, tashi ki fita”.
“Momy nidai ki rabu da shi dan Allah”.
Tayi maganar cikin shagwab’a har ragowan hawayen fuskarta na fitowa.
“Ki tashi kije nace !, tum kafin ranki ya b’aci, bana son musu kin sani “.
Saima ta mik’e cike da k’uk’uni ta shige toilet ta wanko fuskarta ta fito, dama doguwar rigace a jikinta ta janyo wani yalolon mayafi ta yafa akanta ta fice.
Momy ta bita da kallo tana fad’in.
“Saura kuma inji kin wulak’antashi “.
Yana tsaye jikin motarsa cikin wata sky blue d’in shadda wanda tasha d’inki d’an ubansu, hular kansa da takalminsa duk iri d’ayane farare, kansa na kan wayarsa dake hannunsa yana daddan nawa, iya had’uwa ya had’u son kowa k’in wadda ta rasa lol.
Saima tun da ta fito take binsa da kallo aranta taji ya burgeta sosai, yanayin tsayuwarsa da sajen fuskarta tamkar na Yarima, ba da ban zuciyarta ta tsumu da soyayyar Yarima ba da babu abin da zai hanata aminta da wannan gayen, abin da ta aiyana aranta kenan.
Da sallama ta isa wajen ya d’ago kai cike da murmushi yana amsa mata tare da fad’in.
“Yau wace rana ce?, rana mafi sa’a agareni…ranar da bazan mance da ita ba….domin nayi to zali da mafi haske a cikin mata…..yau ta amsa sallamar d’an talikin da baya da zuciya akanta ko yaushe !”.
Saima bata san sanda murmushi ya sub’ucewa fuskarta ba, dubansa tayi akaro na biyu kamar zatayi magana sai kuma ta kau da kai gefe.
“Yi hak’uri Madam kada dai incikaki da surutu, sunana ANWAR SALISU MAI KUD’I, nasan zaki iya sanin mahaifina ko kiji sunansa?”.
Kai Saima ta gyad’a tana fad’in.
“Ehh na sanshi kace kai na gida ne ma, ai mahaifinka abokin Abbana ne”.
Murmushi Anwar yayi yace.
“Nima nasan da hakan !, na d’auka ke baki san hakan bane?”.
“Na sani ! “.
Ta bashi amsa a tak’ai ce, shiru ne ya biyo baya kafin ya katse shirun da fad’in.
“Saima a gaskiya bazan b’oye miki, gaskiya tun sanda na ganki a wajen birthday d’in Yarima kika kwantamin arai, sai dai naso dannewa sabida tsoron irin tarbar da zan samu daga gareki, amma zuciyata ta gaza samun nutsuwa da hak’urin da nake bata ako da yaushe”.
Sosai k’irjin Saima ya buga jin ya ambaci sunan Yarima, sai dai tayi k’ok’arin danne zuciyarta, tare da k’ak’alo murmushin dole, ya cigaba da fad’in.
“Ina fatan zaki karb’i k’ok’on bara na Saima?”.
“Kar ka damu zanyi shawara akan hakan”.
“Ok sai dai ina neman wata alfarma?”.
“Alfarmar me kuma?, fad’i ina jinka”.
“Kimin alk’awarin zaki dinga d’aukan kirana dan Allah”.
Saima tayi shiru na d’an wani lokaci kafin ta ce .
“To babu damuwa Allah ya bani ikon cikawa !”.
“Amin”.
“Ni zan koma, sai yaushe zan dawo kenan?”.
Sosai Saima ta farajin hiran na gundurarta cikin sauri ta bashi amsa.
“Ko yaushe ma”.
“Nagode sosai, sai kinjini a waya”.
“To”.
Ta juya kawai tabar wajen, ba tare datayi tunanin komai ba, domin ta kasa daurewa zuciyarta da tsayuwar da takeyi da shi.
Anwar yabi bayanta da kallo yana dariya cikin ransa.
***
Ta sowarsu kenan daga islamiyya suna tafe suna hira jefi-jefi Zainab ce ma ginshik’in hiran, can tayi shiru ta dubi Aynu da fad’in.
“Kamar fa kina cikin damuwa Aynu?”.
Aynu tayi yak’e tare da duban Zainab tace.
“Wallahi abubuwa ne sunk’ullemin kai sosai, kinsan Yarima Fudhal yana sona to gefe guda kuma Yarima Jalil shima yace yana sona har yana fad’in inrabu da Yarima Fudhal indawo wajensa, ta d’aya gefan kuma Ya sayyaadi Umar”.
“Dama na sani ai !, inkaga kare na shin-shinar takalmi to d’auka zaiyi, nidai kinsan daman na gaya miki na fisonn ki da Yarima Fudhal wallahi Aynu?”.
“Ni kuma kinga Ya sayyadi yafi kwantamin arai domin shine dai-dai ni, shi yafi dacewa dani da rayuwata”.
Zainab taja dogon tsaki.
“Ke kam bakya fahimta wallahi !, yauwa ni kuwa mai ya had’aku da Yarima Fudhal ne?”.
“Mai kika gani?”.
“Babu komai, naga dai kamar bakwa shiri kamar da”.
“Ehh to gaskiyar daya b’oyemin akansa ne ta fito fili”.
“Kamar ta me fa?”.
Nan Aynu ta kwashe dukkan abin da yafaru tsakaninta da Yarima Jalil ta sanarwa Zainab.
“Ni na yanke shawaran barin Yarima Fudhal kawai?”.
Cike da fushi Zainab ta hau fad’in.
“Zancen banza !, wai ke haryanzu baki san waye Yarima Jalil ba ko?, lallai da sauran ki Aynu to Jalil ya wuce dukkan tunaninki da har zaki d’auki maganarsa gaskiya wallahi zai kai ki yabaroki ne kawai”.
“Nifa gani nayi gaskiya ya fa’amin ai”.
“Gaskiyarsa d’in banza !, baki d’auki shawaran da nabaki ba ko?, shikenan kinga tafiyata ni”.
Zainab ta wuce tabar Aynu nan tsaye tana ta kwala mata kira amma tayi banza da ita.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARYA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdauceey Jibour.
19
Yarima Fudhal na shirin fitowa faga falonsa shima Yarima Jalil na fitowa tare da wata ‘yar aikin gidan, yarinyar ta rissina ta gaishe da Yarima Fudhal tabar wajen da sauri, wani mugun kallo Yarima Fudhal ya watsawa Jalil yana fad’in.
“Wai kai yaushe ne zaka san abin da yake maka ciwo ne?, idan aure kake so ka sanar ayi maka mana da wannan muguwar rayuwar da kake?”.
Yarima Jalil ya sosa k’eyar kansa yana fad’in.
“Broda bafa laifina bane ‘yan matan ke bibiyata fa !”.
“Ehh naga alama !, kenan Aynu ma bibiyarka takeyi ko?”.
Yarima Jalil ya d’an fiddo ido waje alamun tsoro k’arara bisa fuskarsa kafin ya wayence ya nemowa fuskarsa murmushin dole tare da fad’in.
“Haba dai..!, kawai mutuncin Yarinyar nake gani amma…?”.
“Daga yau ina so ka daina ganin mutuncin nata !, bana shiga harkar rayuwarka kasani ko?, kasan nafi kowa sanin waye kai Jalil?, kayi tunani idan na sanarwa duniya ko kai waye mai zai faru?, to inaso ka fita cikin tawa rayuwar kafin zuwan lokacin da zaka fara fuskantar fushi na !, fatan ka fahimce ni ?”.
Yayi kwafa tare da barin wajen yabar Yarima Jalil tsaye yana binsa da kallo har sai da yaga ya b’acewa ganinsa sannan yayi dariya yana fad’in.
“Ina….bazai yiyu inzuba ido a cikin gidan nan ana neman mai damu bayi ba !, mumafa ‘yayane da har zai kasance komai sai kai !, yanda aka raba ni da Gimbiya Safiyya to kaima dole ka hak’ura da Aynu..!”.
Ya juya ya koma cikin falonsa cike da dariya ciki-ciki.
Aynu da ke shara falon Yarima Fudhal duk tanajin abin da ya faru, babu abin da yafi d’aure mata kai sai maganar Yarima Jalil ta k’arshe har sake mai-maita maganar tayi cikin ranta.
“Yanda aka rabani da Gimbiya Safiyya to kaima dole ka hak’ura da Aynu….”.
“Ke nan Yarima Jalil yayi hakane domin yarabamu?, kenan son da yake fad’a yanaimin duk k’aryace?, ashe gaskiya Zainab take gayamin na kasa fahimta?”.
Aynu ta zauna d’abas ak’asan carpet tana tunani kala-kala, tsoro ya kamata sosai har dai da ta tuna irin wulak’ancin da tayiwa Yarima Fudhal, take ta yanke aranta zata bashi hak’ura.
“Zai hak’ura kuwa?”.
Wani b’angare na zuciyarta ya jefa mata tambayar, tayi ajiyar zuciya tare da addu’ar Allah yasa ya hak’ura, domin itama cikin kwanakin nan Allah kad’ai yasan halin da tashiga sabida k’auracewa Yarima Fudhal da tayi sauk’in tama tana ganinsa kullum duk da cewa bata kulashi hakan na d’an rage mata damuwar dake k’unshe k’asan zuciyarta.
Yarima Fudhal kuwa yana barin wajen neman Zainab yaje yi, a can b’angaren mahaifiyarsa suka keb’e waje guda babu wanda yake iya jin dukkan abin da suke tattaunawa akai, amma da ka kalli fuskar Yarima Fudhal zaka san ransa a b’ace yake sosai.
Sun shafe tsayin lokaci kafin yabar wajen ya koma b’angarensa, zaune ya tadda ita tayi zurfi cikin tunani bai kulata ba illa neman guri da yayi ya zauna yana fuskantarta ya k’ura mata ido na wani lokaci kafin yayi gyaran murya mai k’arfi daya sanyata d’ago kai da sauri tana kallonsa.
Aynu ta sauke kanta da sauri ba tare da tace komai ba.
“Tunanin me kike?”.
Ya jefa mata tambaya shiru tayi na d’an lokaci tana wasa da yatsun hannunta tana son yin magana amma kuma ta kasa, shima bai kuma cewa da ita komai ba illa kafeta da idanuwa da yayi shi komai Aynu takeyi ba k’aramin burgeshi take ba, da k’yar dai ta iya furta.
“Kayi hak’ura abisa abin da nayi maka !”.
Ta fad’a ba tare da tayi tunanin bashi amsar tambayarsa ba.
“Babu komai, amma kinsan wani abu kuwa?”.
Kai ta girgiza alamun a’a, ya cigaba da fad’in.
“Mai yasa kika k’i sanarmin dukkan abin da ya faru tsakaninki da Jalil?, ke nan har yanzu baki rabu da shi ba?”.
“A’a, babu yanda zanyi ne akan had’uwata da shi”.
“Ok..amma mai yada kika d’au maganarsa serious ba tare da bincike ba?”.
“Kawai na kasa tausar zuciyata ne”.
“Aynu !, har yanzu baki yarda da son da nake maki bane?, ko nine baki yarda dani ba?”.
“A’a na yarda mana”.
Ajiyar zuciya Yarima Fudhal yayi yana mai cigaba da kallonta tare da nazarin yanayinta, kafin yace.
“Kada ki yaudari zuciyarki kamar akwai abin da kike kokwanto a kaina haryanzu, zanyi k’ok’arin kau da kokwantanki nan da lokaci k’ank’ani zaki fahimci waye ni Fudhal?”.
“Amma kafin nan kisani ina k’aunarki sosai wallahi Aynu sai dai bazan iya tsayawa inyi miki bayanin son da nake miki ba amma zaki iya karantar hakan a cikin idona, sannan ni aganina tsayawa infad’awa mace irin son da nake mata k’auyanci ne kiyi hak’uri dani Aynu a duk yanda kika ganni, kiyi hak’uri da halayyata”.
Murmushin jindad’i Aynu tayi domin sosai takejin dad’in kalamansa a cikin zuciyarta, ta fahimci Yarima Fudhal sosai yana sonta sai dai girman kai da izzar mulki bazai bashi damar nuna mata ba, duk da wani lokacin tasan zuciyarsa na rinjaye akan girman kansa indai akanta ne.
“Ba kice komai ba sai murmushi da kike?”.
Aynu ta sanya tafukan hannunta ta rufe fuskarta wai ita a dole kunyarsa takeji, murmushi yayi mai sauti yace.
“Kunyarki na burgeni Aynu, ina son mace mai alkunya sosai”.
Ita dai Aynu ta gaza cewa komai, ya cigaba da fad’in.
“Wannan malamin naku naga kaman yana neman wuce gona da iri fa !, domin Zee ta fad’amin cewa shima sonki yake?”.
Ya k’arashe maganar tare da guntun tsaki, Aynu ta d’anyi murmushi kawai.
“Ina magana kinyi shiru?”.
“Ni mai zance to”.
“Komai ma kice, ina buk’atar jin muryar taki”.
“Kinsan wani abu ?”.
“Bari inje fada yanzu, anjima kad’an zan dawo ka da kitafi gida ki jira ni “.
Ya k’arashe maganar yana mik’ewa tsaye tare da sakarwa Aynu wani tsadaddan murmushi da bata tab’a ganinsa saman fuskar Yarima Fudhal ba sai yau, Aynu ta mayar masa da martanin murmushinsa tana fad’in.
“Angama Ranka ya dad’e !”.
Yasa yatsan hannunsa d’aya ya lakuci karan hancinta yace.
“Kema ranki ya dad’e Gimbiya”.
Ya fice yabarta zaune falon, yana fita tamik’e ta k’arashe sharar falon zuciyarta fari k’al, har wani sanyin dad’i takeji yana ratsa dukkan wasu k’ofofin gashin dake jikinta.
A gag-gauce ta kammala ta fice zuwa wajen Zainab domin taji dalilin da yasa ta sanarwa Yarima Fudhal komai.
Zainab tace “aini fushi nake da ke Aynu tunda har zaki yarda da maganar Yarima Jalil”.
“To ya kikeso nayi ne Zainab kishi ne duk yajamin hakan”
Dariya suka d’anyi kad’an Zainab na fad’in.
“Kaga masoya !, Aynu ta Yarima Fudhal d’inmu”.
“Ke banson iskanci fa !, me yasa kika sanar mishi abin da na fad’amiki?”.
“Me zai hana bazan sanar masaba d’an bawan Allah na neman zaucewa akanki, wallahi Aynu Yarima Fudhal yana sonki sosai bazan daina fad’amiki ba”.
“Nima na sani Zainab, to amma ai naga mata biyu zai aurafa, kenan ni zai aura ta uku kome?, ko kuwa matsayim k’warkwara zai aure ni?”.
“Wannan ne bansani ba gaskiya”.
Aynu tayi ajiyar zuciya tana fad’in
“Nasan inason Yarima Fudhal nima, amma bazan iya kishi da Gimbiya Safiiya ba”.
“Nima inna tuna haka abin nad’an tsorata ni, kawai dai muyita addu’a shima abin da ya gayamin kenan”.
” Yauwa wai kuwa kinsan abin da naji Yarima Jalil na fad’a d’azu?”.
“Sai kin fad’a ina jinki bani labari”.
“Na fasa fad’a domin nasan sai kin gayawa Yarima Fudhal, in kina son ji sai kinyi alk’awarin bazaki fad’a masa ba”.
Zainab tayi shiru tana duban Aynu taga tabbas da gaske take hakan yasa tace.
“To na amince fad’amin”.
Aynu ta kwashe komai ta fad’awa Zainab, Zainab zaro ido waje tayi tana fad’in.
“Kin ji ko?, ai nagaya miki dama kiyi hankali da Yarima Jalil ya wuce dukkan tunaninki wallahi”.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdaucee Jeebour.
20
(Kuyi hkr dani abisa rashin jina da kukayi kwana biyu, amma yanzu komai nml insha Allah zaku dunga jina kullum, ngd sosai sosai masoyana da masu call zuwa message).
“Ya bawa da kyakykywar halaiyarka tasa na aminta da kai !, na baka dama ka cigaba da zuwa wajen Aynu, kafin zuwan lokacin da zamu san abinyi, duk da cewa sai kayi hak’uri da ita sosai domin Aynu yarinyace haryanzu batasan me rayuwa take ciki ba…”.
Aynu da keshirin shiga gida taji Babanta yana yiwa Ya sayyadi Umar maganar, sosai k’irjinta ya buga har sai da tad’an dafe wajen da hannunta.
“Gata nan ma ta dawo ai”.
Babanta ya fad’a fuskarsa cike da fara’a, Aynu ta durk’usa ta gaisheshi ya amsa yana mai cigaba da fad’in.
“Ga Malaminku nan, anan na sameshi yana zaman jiranki, ni bari ink’arasa bakin kasuwa “.
“To Baba Allah kiyaye !”.
Sukayi maganar kusan atare, Aynu ta mik’e tsaye tana mai duban fuskar Ya sayyadi, sai dai yau d’aya sai taji bata son ganin fuskar tasa ma, d’auke kai tayi gefe tare da fad’in.
“Ina yini?”.
“Lafiya k’alau Aynu, kwana biyu kinjini shiru ko?”.
“Ehh”.
Ya Sayyadi yayi d’an guntun murmushi.
“Zuwa nayi har gida inji amsa ta”.
“Amsar mefa?”.
“Ohh kina nufin kin manta Aynu?”.
Aynu tayi k’ok’arin nemo murmushi saman fuskarta.
“Wannan mai sauk’ine tunda gashi har Baba ya amince da kai”.
“Kina nufin kema kin amince kenan?”.
Murmushi tayi tare da gyad’a kai, alamun ehh.
“Alhamdulillahi…Aynu nagode sosai Allah ya tabbatarmin da mafarkina akan ki”.
Mai-makon ta amsa da amin sai cewa tayi.
“Zan shiga gida sai zuwa anjima nagaji wallahi”.
“Babu komai Aynu kina buk’atar hutu dama, a gaishemin da Umma”.
“Za taji”.
Ta fad’a tana mai shigewa cikin gida ta barshi nan tsaye.
Kafin shima ya kama hanya yabar wajen.
***
” Ya kamata indai da gaske kana sona Iyayena su sanka ko?”.
“Kamarya kenan !, wani abu ya faru ne?”.
“Ehh jiya naji Babana yana bawa Ya Sayyadinmu umarnin ya cigaba da zuwa wajena, kuma baki d’aya su Umma shi suka sani basu sanka ba”.
Ajiyar zuciya Yarima ya d’anyi, yana mai duban fuskar Aynu dake k’asa sosai yake nazarinta kafin ya bud’e baki ya fara magana.
“Ke yarinyace Aynu !, nasan cewa ina sonki sosai Aynu amma kamata yanda nake d’innan har saina k’ask’antar da kai zan samu abu?”.
“Ban gane ba?”.
Aynu tayi tambayar tana mai duban fuskarsa.
Dafa kafad’arta yayi da hannunsa guda d’aya, d’ayan hannun kuma cofin juice ne yana sha.
“Nifa d’an Sarki ne !, muna da kud’i da mulki aganinki ko da mahaifinki ya bayar dake idan naje zai hanani auren ki?, idan ma zai hana ai ga kud’i !”.
Aynu tabishi da kallo kawai tana nazarin maganarsa amma ta kasa fahimtar abin da yake nufi, shima kuma dama bawai buk’atar fahimtarta yake ba.
” Karki damu Yarima naki ne har abada !, Mubar wannan maganar kinji ?”.
Yayi maganar yana mai zama a gabanta suna fuskantar juna, aransa yasan gaskiya ta fad’a amma girman kai da Izzar mulki bazasu bari yakai kansa gaban iyayen taba domin shi akomai nasa yanayin ammafani da mulki da kud’i ne, yasan kuma indai akwai kud’i tamkar ya samu Aynu ne, domin yasan iyayenta gajiyayyu ne ba tunyanzuba sabida bai je k’ofar gidansu ba sai da ya fara sanin wacece Aynu?.
Murmushi Aynu kawai tayi tare da dubansa duk da cewar zuciyarta bata aminta da zancen da yayi ba, shima kuma ya karanci hakan, amma yasan duk iya tunaninta bazai tab’a kawo kan abin da yake nufi ba.
Gimbiya Safiyya ce ta shigo fuskarta cike da murmushi, amma yanayin data gansu ya sanya fuskarta canjawa daga murmushi zuwa b’acin rai, Aynu tayi k’ok’arin mik’ewa da sauri ta tsaya, shi kuwa gogan ko a jikinsa wai antsikari kakkausa, saima cigaba da shan juice d’insa da yayi bai ko kalli inda take ba bare ya nuna mata cewa yasan ta shigo.
Sosai Safiyya taso danne zuciyarta sai dai shaid’an yaci galaba akanta ta hanyar hura wutar kishi sosai a cikin ranta.
A hankali ta taka zuwa inda Aynu take sai jin sautin k’arar mari kawai Yarima yayi akunnenta ya d’ago da sauri dan ganin wa aka mara ?, ganin Aynu yayi rik’e da kunci tana bin Safiyya da kallo, Safiyya ta watsa mata wani mugun kallo tare da fad’in.
“Banza kawai KARUWAR CIKIN GIDA….!”.
Kafin ta kai ga rufe bakinta Yarima Fudhal shima yad’auke ta da wani gigitaccen mari, ba Gimbiya Safiyya ba hatta Aynu ta girgiza da marin da Yarima ya yiwa Safiyya, cike da b’acin rai yake fad’in.
“Zaki iya sanya hannu ki mare ni in kyaleki, amma tunaninki zaki mari Aynu natsaya ina kallonki ne!, idan kin kirata da karuwar cikin gida ke kuma a kira ki da me?, akwaima mace mara aji da rashin kamun kai data wuce matar da zata biyo saurayinta har cikin gidansu ta zauna kuma kullum k’afarta na hanyar d’akinsa wai da sunan soyayya?”.
Shiru ya gauraye d’akin sai aikin kallon-kallo da sukeyiwa junansu, Yarima Fudhal ya katse shirun da fad’in.
“Akwai banbanci mai yawa tsakanin Mace me kyau Mara aji da mummuna mai aji !, da yawan ‘yan mata kuna daukar aji da ake fada abun wasa ne toh aji Yana nufin wadda take tamkar MAR’ATUSSALIHA irin macen da akai kwatan ce da ita a ilmance wallahi dana auri mai kyau ballagaza mara kamun Kai kwara mummuna mai aji da sanin hak’k’ina !, har yanzu bangama aminta da tarbiyarki ba, taya zan auri macen da tarbiyarta bata wadace taba bare ta baiwa ‘ya’yan da zata haifa zuwa gaba ?, kiyi tunani da kyau sosai Safiyya ni Yarima Fudhal ko kusa ban dace da ke ba sabida ni ba ajin ballagazar mace bane !”.
“Sannan ina mai baki kyakykyawan albishir ki gayawa kowa AYNUL-HAYAT nakeso wato ‘yar aikina kuma Baiwata !, ko da kinmatsa na aure ki to kisani babu d’igon sonki a cikin raina !, domin nasan ke baki da aikin da yawuce kai k’arata to bismillah…!”.
Ita dai Aynu tana gefe tana aikin zubar hawaye k’asan zuciyarta kuwa Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un kawai take ambato domin tasan Allah kad’ai yasan yau iya yawan ruwan da Yarima yab’allo mata.
Shi kuwa a ganinsa hakan da yayi ne dai-dai domin shi bayason takura a cikin rayuwarsa, yayi hakan ne domin ya share tunaninta naganin cewa yana sonta kawai sharewa yake, a gefe guda kuma hakan yake ganin mafita wajen warwarewar alak’ar aurensu da akeson k’ullawa.
Zuwa yayi gaban Aynu ya kama hannunta ya jata zuwa cikin bedroom d’insa ya bar Gimbiya Safiyya nan tsaye kamar anjona mata lantarki, tayi mutuwar tsaye hawayan dake zuba kan fuskarta ne kawai zai iya tabbatar maka kasan cewa da ranta ba mutuwa tayi ba tsabar kad’uwa da tayi da maganganun Yarima Fudhal.
Toilet ya kai Aynu tare da fad’in.
“Wanke fuskarki, kada ki fita da hawaye”.
Shi kuma ya dawo cikin d’akin gefan katifarsa ya zauna tare da dafe kansa yana tariyo abubuwan da suka faru.
“Mai Martaba…!”.
Ya furta hakan afili yana mai d’ago kansa da sauri cike da kad’uwa hankalinsa ya tashi sosai.
Ko meye dalilin hakan ?, Oho.
Gimbiya Safiyya kuwa da k’yar ta iya d’aga k’afafuwanta tabar cikin falon ta koma b’angaren Fulani Sokoto tana tafe tamkar zata fad’i, duk inda tawuce sai anbita da kallo tare da tambayarta lafiya?, amma bata iya furta komai sai hawayen takaici dake bin fuskarta.
Tana shiga falon Fulani ta zube k’asa tare da fad’in.
“Wayyo Allah Momy ki taimake ni wai baya sona!”.
Fulani Sokoto da Jalila sukayi ca akanta kowa na tambayarta.
“Lafiya !, mai ya faru ?”.
Safiyya ta fad’a kan cinyar Fulani ta kifa kanta, tana mai cigaba da rera kukanta, d’ago da kanta Fulani tayi tare da fad’in.
“Kalle ni Safiyya share hawayenki ki bani bayanin abin da yafaru, domin insan abinyi insan irin lallashin da ya kamata inyi miki, amma kinzo kin sani gaba kina kuka ban san me ya faru ba taya zan lallashe ki?”.
Gimbiya Safiyya ta share hawayenta ta fara bawa Fulani labarin dukkan abin da ya faru bata rage ko d’aya ba illa k’arin masu sugar da tayi cikin bayanin nata domin Fulani Sokoto ta zuciya sosai.
Ai kuwa idan ran Fulani ya kai duba ayau yab’aci, amma da yake mata ce irin ‘yan duniya da suka goge a iya bariki murmushi tayi tana fad’in.
“Wannan ne zai tada hankalinki?, har kizo kina ihu akan wani banzan kwaro Fudhal !, kwantar da hankali ai anzo inda nake so azo WACECE AYNUL-HAYAT kuma ?, hmmmm karki damu yanzu za’a fara wasan indai ni naci sunan nawa da ake kirana dashi Fulani Sokoto zanga tayanda za’ayi Fudhal ya samu dukkan cikar burinsa a duniya !, bare kuma har ya auri wacce yake ikirarin ita yake so !, kuma ko yak’i ko yaso sai kin aure shi indai ina raye…. !”.
Jalila dake zaune gefe tana jin batun da mahaifiyar tasu takeyi tayi wani guntun murmushi tace.
“Ai dama Momy ke kika k’yale komai haka sakaka wallahi, ya kamata ki tashi tsaye tun da wuri!”.
***
Zainab ce zaune falonsu tasa kwanun abinci a gaba tana ci gefe guda kuma Maman tace zaune tana yankan farce, Zainab ta d’an dubi Mamanta tace.
“Wai kuwa Mama idan saurayi yace bazai zo gidanku yaga iyayenki ba susan juna, kawai dai yasan ko bayan anba dake zai zo da kud’ine yasan kuma dole a bashi ke me hakan ke nufi?”.
Baba Ta Sallah tabar yankan farcen tana duban Zainab tare da tambayar .
“Waye wannan shi kuwa?”.
“Wani ne ya gayawa Aynu wallahi”.
Baba Ta Sallah tayi ajiyar zuciya kafin tace.
“A iya sanina da tunanina da kuma duk wanda yaji wannan zancen, abin da zai d’auka koma ince yanda gaskiyar al’amarin yake, shi wannan saurayin kwata-kwata baisan muhimmanci iyayenta ba, asalima ko da auren akai taya zai daraja iyayenta domin a ganinsa iyayen banza ne sun bada ‘yarsu shi kuma yazo ya nuna kud’i anbashi ita !, wannan mutumin baya daga cikin irin mazajen da ya kamata mace ta aura”.
Zainab tayi shiru tan duban Baba Tasallah kafin tace.
“Mama Yarima Fudhal shiya fad’awa Aynu haka, ni abin ya bani mamaki fa, yanzu ace duk irin son da yake nunawa da fad’a yanayi mata kenan ya tashi abanza tunda bai d’auki iyayenta bakin komai ba?”.
“Sosai ma kuwa ni dama tunda kika bani labarin yana son Aynu nasan za’ayi haka, ku a tunaninku gidan Sarkin nan da danginsu baki d’aya sund’auki talakan mutum a bakin komai ne?”.
“Ban gane ba Mama?”.
“Ku yara ne yanzu kukazo duniya, amma abin da baki sani ba shine Sarki Ubaiyd bai d’auki talaka abakin komai ba illa ya zama bawansa, kuma a hakan ya tarbiyartar da iyalinsa”.
“Amma kunsan hakan kuka bari muke aiki a gidan?”.
“Dole ce ta sanyamu Zainab da muna da yanda zamuyi da ko k’ofar gidan ba zamu je ba”.
Zainab shiru tayi tana duban Mamanta cike da tambayoyi kala-kala amma ayanda ta karanci yanayin Maman bazata iya sanar da ita komai ba.
KO MEYE DALILI?.
Nima kaina ina buk’atar sanin wannan amsar, amma nasan koma mene akwai wani boyayyan al’amari.
*YARIMA FUDHAL*
Na
FIRDAUSI S.A(QURRATUL-AYN).
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®
SADAUKARWA:-Namesy Phirdaucee Jeebour.
21
DARE
9:00PM
Falon Mai Martaba cike yake da mutanan gidan sabida meeting d’in gaggawa da Mai Martaba ya shirya a daran nan.
Gefe guda Mai martaba Sarki Ubaiyd ne kishingid’e bisa kusun, daga wajen kansa Fulani Bingel ce tare da ‘ya’yanta Aunty Sadiya da Aunty Sa’ida mazajensu suka kawosu, sai Yarima Fudhal daga wajen k’afarsa kuma Fulani Sokoto ce tare da ‘ya’yanta ita ma a kusa da ita, Yarima Jaleel da Jalila sai Gimbiya Safiyya .
Mai Martaba ya shafe tsayin lokaci yana bin iyalinnasa da kallo, kafin yayi gyaran murya tare da jero addu’o’i sannan yayi sallama suka amsa ya fara fad’in.
“Ba komai ne yasa ni shirya wannan taron na gaggawa ba sai dalilin faruwar bijirowar wata b’araka daga cikin danginmu, da kuma shirya rushewar martabar danginmu da mutuncin sarautarmu!”.
“Fudhal…!”.
Mai martaba ya kira sunan da kakkausar murya.
Kowa sai da ya dubi Mai Martaba domin yau karo na farko da sukaji ya kira Yarima Fudhal da sunansa sab’anin Magaji da akafi ji yana kiransa da shi tsayin shekaru.
Mai martaba ya cigaba da maganarsa.
“Fudhal kai ne ke shirin ruguza mana komai !, mene haka ka ke shirin aikatawa ?, k’asar wajen da na kai ka tsayin shekaru kayi karatu abin da suka koya maka kenan soyayya da Baiwarka?”.
Yarima Fudhal yayi shiru kansa a k’asa ya kasa iya d’aga kansa bare har ya iya bada amsar tambayar da ake yi masa, mai martaba ya cigaba da fad’in.
“Karka manta kaifa magaji ne a bayana, shin kanason bijirewa umarni nane kome?, ko kuwa ban isa da kai bane?, kar kamance ni Ubaiyd bana magana biyu auren ka da Safiyya tamkar anyi angama ne !”.
Sai lokacin Yarima Fudhal ya d’ago kai ya kalli Mai Martaba kafin ya sake yin k’asa da kansa ya fara magana.
“Bazan gajiya wajen neman afuwarka ba, sai dai ina rok’o agareka Abba ka taimaka kabani zab’in raina nasan hakan tamkar tozarcin Family namu ne amma babu yanda na iya ne tabbas inason Aynu amma da ace ina da damar da zan iya cire soyayyar da na cire ta domin samun yardarku da cika umarninku…!”.
Yayi shiru nad’an wani lokaci yana jira yaji ko Mai martaba zai ce wani abu jin da yayi bai ce komai ba yasa yacigaba da magana.
“Kayi hak’uri Abba !, ni banyi haka domin na bak’anta ranku ba burina kullum bai wuce ganin farin cikin iyayena ba ko da zan rasa raina !, amma Abba ina son yarinyar ne badan komai ba sai domin ta can-canci a so ta, sabida tarbiyarta da kamalarta….sannan!”.
“Kaga ya isa Magaji !, ban kira ka dan intambayeka can-cantar taba ko tarbiyarta na kira ka ne domin in tabbatar maka kome za kayi aure kai da Safiyya da Saima babu fashi sai dai idan sune sukace basa so !, kuma babu kai babu auren wannan Baiwar KO BAYAN RAINA !”.
Yarima Fudhal ya rintse ido sabida yanda yaji zuciyarsa na zafi sosai, har jiyake kamar ransa zai iya barin gan-gan jikinsa a lokacin.
Fulani Bingel ta dubi d’an nata tare da duban Mai Martaba, ta so yin magana amma tasan bazai saurareta ba, tana tausayawa Yarima Fudhal domin tasan halinsa ko kad’an bai iya sanyawa ransa damuwa ba.
Mai Martaba ya sake duban kowa kafin yace.
“Sannan ita kuma yarinyar daga yau tabar aiki a gidan nan, kowa ya tashi ya tafi “.
Wannan hukuncin bak’aramin dad’i yayiwa Fulani Sokoto da Yarima Jaleel ba, musamman uwar gayyar Gimbiya Safiyya gefe guda kuma ga Aunty Sa’ida domin itama tak’i jinin ace Yarima Fudhal yarasa wadda zai lak’ewa sai Baiwarsa tir da wannan al’amarin.
Kowa ya mik’e ya fice ban da Fulani Bingel da Yarima Fudhal ya ya kasa mik’ewa, domin yasan indai yamik’e a wannan lokacin to tabbas sai dai su d’au keshi hakan yasa yayi zamansa yana karanto addu’o’i cikin ransa, Mai Martaba ya dube shi duba na musamman yana fad’in.
“Ka kwantar da hankalinka Magaji kai fa magajina ne, akan wane dalilin zaka bari ka lalata rayuwarka a banza?, ina so ka cire duk wata damuwa dake cikin ranka kayi ayyukan dake gabanka, an kammala ginin Asibitin dana shirya gina maka, na gayyato gwararrun likitocin da zasuyi aiki a cikinsa tare da kai, zuwa nan da sati guda sai ayi bikin bud’eshi ko?”.
“Ehh duk yanda kace Abba, Allah yasaka da alkhairi ya k’ara girma da arzik’i “.
“Amin”.
Fulani Bingel ta amsa tare da cigaba da fad’in .
“Ka k’ara hak’uri kaji ?, komai mai wucewa ne a rayuwa !”.
“Insha Allah”.
Yarima Fudhal ya mik’e yana mai jan k’afafuwansa da sukai masa nauyi tare da bin bango yabar d’akin kai tsaye d’akinsa ya nufa ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwan shower mai sanyi domin wai yaji sanyi cikin ransa.
Fulani Bingel ta dubi Mai Martaba bayan fitar Yarima Fudhal tace.
“Da anbi komai a sannu Mai Martaba !, wannan hukuncin kamar yayi tsauri domin ban da Allah babu wanda yasan matar mutum, domin shi al’amarin aure sai anbi a sannu…!”.
“Ki na so ki goyi bayan d’anki ne?”.
“A’a ko kusa kaima ai d’an kane”.
“To bana buk’atar jin wani k’orafi cikin maganar da nayi !”.
“Allah ya huci zuciyarka !”.
***
Ko da Aynu ta koma gida wunin ranar tayi shine sukuku, har zuwa sanda ta dawo daga Islamiyya ta zauna gaban Ummanta tare da d’aukan littafin Hisnul-muslum tana dubawa, Umman ta d’an kalli gefen da Aynu take zaune tace.
“Meye alak’arki da Yarima Fudhal kuma?”.
Aynu ta d’ago da sauri fuskarta cike da murmushin jindad’i domin ansosa mata inda yake mata k’yaik’ayi.
“Umma ba wani abu bane bafa, kawai dai cewa dai yayi wai yana….!”.
Sai kuma tayi shiru domin jin nauyin mahaifiyarta akan maganar da zata fad’a mata.
Umma tayi ‘yar dariya tare da k’arasa mata maganar da take son yi.
“Yana sonki ko?”.
“Ehh”.
“Aynu kenan…!, amma kinsan abin da zan fad’a miki kuwa?”.
“A’a umma”.
“Duk da cewa ba ganinki nake da ido ba, amma ina kallonki ta zuciyata, nasan kina son Yarima Fudhal amma kada ki bari soyayyarsa tayi tasiri aranki da yawa domin mudai iyayanki zab’inmu shine Ya Sayyadi Umar, duk da ba musan yanda Allah zaiyi nasa hukuncin bisa wannan al’amari ba, amma inaso kiyi tunani Yarima yafi k’arfinmu mu iyayenki bare ke Aynu ki tsaya a matsayinki kada ki kai kanki inda Allah bai kai kiba kinji ko?”.
“Ehh Umma insha Allah zan kiyaye !”.
Aynu takai maganar tana mai goge hawayen da ke bin kan fuskarta, tasan tana son Yarima Fudhal amma kuma bazata iya jayayya da umarnin mahaifiyarta ba.
***
Misalin 6:25 na yamma.
Aynu ta dubi Ummanta tana fad’in.
“Umma bari inje wajen Zainab yau duk bamu had’uba sabida banje aiki ba, kuma ina son karb’o wani littafi ne”.
“To amma kinga yamma tayi ankusa sallar maghriba ki dawo da wuri kada Babanki yazo ya tarar bakya nan”.
“To Umma dama ba jinawa zanyi ba, ina karb’owa zan tawo”.
Ta kai maganar tana mai ficewa, ko da ta isa gidansu Zainab Mamanta bata nan sai Zainab d’in zaune tana yankan farce, Aynu tayi sallama ta shiga ta nemi guri kusa da Zainab d’in ta zauna suka fara hira.
“Kinsan kuwa amsar da Mama ta bani dana tambayeta akan maganar nan?”.
Cewar Zainab kenan tana mai duban Aynu, Aynu tace.
“A’a sai kin fad’a”.
Nan Zainab ta kwashe duk yanda sumai ta sanar mata, sosai kayan cikin Aynu suka juya har sai da ta nufi toilet ta fito ta nemi guri ta zauna tayi ta gumi tana fad’in.
“Ko kinsan d’azun nan Umma kemin maganar wai inyi baya-baya da Yarima su zab’insu Yasayyadi Unar ne?”.
Zainab taja ajiyar zuciya tana fad’in.
“Karki damu Aynu muyita addu’a dai koma waye mijinki Allah ne masani kuma shine zai zab’a miki mijin da ya dace da ke, sannan akwai wata magana ma da zan fad’a miki”.
“Ina jinki”.
Aynu ta fad’a ba tare data dubi Zainab ba.
“D’azu Jakadiyya tazo tace a fad’a miki kinbar zuwa aiki sabida Mai Martaba ya bada umarnin kada ki sake zuwa !”.
A firgice Aynu ta d’ago kai ta dubi Zainab.
“Me kika ce?, to mai nayi masa ?”.
“Baki masa komai ba, akan d’ansa Yarima Fudhal yace kibar aiki gidan sabida ya raba ku”.
Aynu tayi ajiyar zuciya tana fad’in.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un !, shikenan ta faru ta k’are”.