NOVELSUncategorized
BARIKI NA FITO (BOOK 2) 15

BOOK 2
PAGE 15
Bariki direct u/kanawa ta koma, har takai gida Yarima bai zoba, dan haka taita zaman jiranshi, tayi wajan 30mnt din sai gashi ya kirata akan ta fito yana kofar gida…..
Tashi tayi ta fita inda ta sameshi cikin mota….
Gaidashi tayi cikin kulawa tare da fad’in ya aiki??
Mai yakon ya bata amsa saiya kafeta da ido, ba komai yake tunawa ba sai kalaman mahaifin nashi, inda yace karya K’ara mishi maganan auran da yake son k’arawa ….. Ido ya lumshe yana tunanin abubuwa da dama, ya tabbata bazai iya juran rashin Zainab ba, amma ya, ya iya tunda mahaifin nashi haka ya bashi umarni…. Tunda yake abbanshi bai taba cewa Kar yayi abu ba ya ketare, yana ji a jikinshi bazai iya juran a hanashi auran Zainab ba……
Jin yayi banza da ita yasa ta d’ago taga ita yake kallo da sauri tayi k’asa dakai tare da fad’in Yarima lafiya kuwa??
Murmushi yayi tare da fad’in lafiya, kawai I miss you ne…
Murmushi tayi tace kullum fa saika ganni jiya ne kawai baka ganni ba….
Yace hakane, jiyan kawai da ban ganki ba, yasa naji kaman Nayi shekara ban ganki ba
Dariya tayi mara sauti domin taji dad’in maganan da yayi…….
Sun d’an taba fira, sannan ya mata sallama ya wuce…..
Bayan Yarima ya koma Gida direct wajan mum dinshi ya nufa, bayan ya gaidata ya zauna kusa da ita tare da fad’in mum plz ina son magana dake which maganan ya shafi rayuwana…..
Gaba d’aya hankalin mum din yayi kan Yarima wanda magananshi ya bata tsoro, musamman daya ce maganan dazai Mata ya shafi rayuwanshi….. Tace Yarima Mai ya faru?? Maiya sameka? Wani abu ne?
Yace mum akan maganan k’arin auren da nake son yine. Plz mum Ina son yarinyar Sosai, mum Bari kiji tun a mafarki na Fara ganinta……..
Mum tace mafarki??
Yace eh, tare da bata labarin abunda yake faruwa… Ya d’aura da fad’in mum had’uwa na da yarinyar had’in Allah ne, ina matukar sonta, mum Idan aka hanani auranta ban iya j……
Da sauri mum tace ya isa haka, jikinta a sanyaye tace Yarima zanyi magana damai martaba, Kaje ka huta dan naga alaman kaman yanzu ka dawo…..
Yace eh mum, tare da tashi ya fita…..
Mum shuru tayi tana nazari, lallai ya kamata abar Yarima yayi wannan auran, tunda har Ya iya cire kunya ya Mata bayani irin haka….. Tashi tayi ta nufi gefen mijin nata , toko ci Sa’a shi d’aya ne, zama tayi tare da fad’in Barka da yamma.
Mai martaba Ya amsa da yauwa, yana ga kaman kina cikin damuwa? Domin Fuskanki ya nuna hakan.
Tace inada magana ne akan Yarima.
Da sauri mai martaba yace maiya sami Yarima din??
Tace babu komai magana ne akan auranshi da yake son karawa….
Mai martaba yace ba jiya nace abar wannan maganan ba, sai nan gaba
Tace hakane, amma ina son fad’a maka Yarima yanzu yabar wajena, akan maganan auran nashi, labarin yanda sukai da Yarima ta fad’a mishi harda mafarkin da Yarima yakeyi, sannan tace ina son in baka shawara ,tunda muke da Yarima bamu taba cewa yabar Abu ba, sannan daka baya ya dawo da maganan……
Mai martaba ya dakatar da ita da fad’in, lallai wannan babban magana ne, Yarima yana mana biyayya a matsayin mu na iyaye….. Tunda har na hanashi maganan ya kara taso da ita bai kamata in hanashi ba, domin hanashi zai iya sawa ya bijire mana, domin shi SO daban yake, sannan muma ya kamata mu masa adalci mu amince da duk wata bukatarshi Indai bai sabama Shari’a ba….. Yau na fahimta abunda ya dad’e yana damuwa, lallai iyaye k’alu bale garemu Idan d’anka ko y’arka suna maka biyayya tare dajin duk wata magana taku, Indai yaron ya Kawo muku abu kuka nuna bakwa so, Indai ya dage Toh ku tayashi son Abun tare da mishi fatan alkhairi….. Sau da yawa wasu iyayen suke saka yaransu suke bijire musu Bayan yaran suke da gskya amma iyayen Suki yarda da kudiran yaran, in ba’a sami Mai hakuri ba saiya bijire musu, yaka mata iyaye su dinga Lura da miye yaransu suke so tare da abunda suke bukata…. Kar matsayinku na iyaye yasa ku manta hakkin yaranku akanku…… Haka zalika Kuma yaran Kar soyayya yasa ku bijire ma iyayenku ,domin Kaf duniya babu mai muku son gskya kaman iyayenku……. Akwai wani labari da naji na wani yaro da yake son auran wata yarinya……. Yarinyar kowa yasan bata ji, Ma’ana dai y’ar iska ce yarinyar, lokacin da yaron Ya fad’ama ma iyayenshi sai suka k’i yarda suka ce ya nemi wata, shiko yaron yace Wlh ita yake so, aka buga aka raya, Baban yaron yace sam bai yarda Yaronshi ya auro yarinyar ba domin y’ar iska ce……. Ganin yanda babanshi ya dage, sai yaron Ya daina musu komai dama iyayen ba masu karfi bane, yaron ke musu komai tunda yana aiki,…… Toh Kunga irin matsalolin dake faruwa, a sanda naji wannan labarin Nayi takaici Sosai, ai iyaye iyaye ne, yaka mata mu dinga hakuri dasu, mu muna ganin mune akan dai dai, haka suma suke gani sune akan dai dai, in kayi hakuri kabi umarnin su, kasan kwana nawa za suyi a duniyar?? Koko saika rasa su zaka Fara kuka dayin dana sani?? Wlh baka taba sanin muhimmancin iyaye sai basa raye, sai munyi hakuri da iyayenmu sau da yawa kana ganin abunda yake dai dai kuma kowa yasan dai dai ne amma su sai suce sam, in mutum ya duba Aida basa haka, yanzu harda girma daya kamasu sai yasa suke irin haka, Idan mutum yana girma tunaninshi yana kara canzawa…… Idan har yaro yana tuna haka ya kamata ya dinga hakuri da iyayenshi, sannan abunda kama iyayenka kaima haka naka za suyi maka shairi ko khairan, sannan Indai kai burinka kuntata ma iyaye bazaka taba ganin haske ba a rayuwa..
Mum tace hakane, Allah yasa mu dace
Mai martaba ya amsa da Ameen, tare da fad’in zan tura aje a nema masa auran yarinyar cikin satin nan insha Allah, saiku Fara shiri
Mum tayi y’ar murmushi tare da fad’in Allah ya bada Sa’a zamma Yarima albishir
Dariya Mai martaba yayi tare da fad’in dan nema ba, Ashe tun a mafarki yake ganin yarinyar ikon Allah.
Mum tace Wlh nima nayi mamaki, Allah dai yasa abokiyar zama ce.
Mai martaba yace lallai soyayyarsu had’in Allah ne, duk Wanda yace zai shiga tsakani akwai matsala
Mum tace hakane, tayu rabo ne na kusa tsakani sai yasa ya kasa hakuri, kuma rabo na kisa
Mai martaba yace hakane, Allah ya shige mana gaba…..
Mai martaba yasa an tura gidansu bariki, inda su waziri suka je, kuma babu laifi su waziri Sun yaba da irin gidan tarbiyan da bariki ta fito, domin tunda Yarima ya fad’a mata ranan da za suzo bariki ta hayo wasu mutum biyu Sunan sune y’an uwan mahaifinta, sannan duk ta tsara musu yanda za suyi.
Koda waziri yayi maganan sadaki akan nawa zasu yanke
D’aya daka cikin kawun Bariki na karya yace dubu hamsin ya isa, domin karancin sadaki shine albarkan aure,
Waziri yaji dad’i Sosai domin ya gano gidan mutunci Yarima yake neman aure sannan ba masu kwadayin abun duniya bane, duk da ya gansu talakawa kuma ko yanzu a sauron gidan suke zaune, Ma’ana a zaure.
Nan take Waliyan Yarima suka biya sadaki, dubu hamsin tare da K’ara million d’aya suka ce wannan kaman matsayin kyautatawa ne, tunda iya abunda suka yanke shine na sadakin,
Dakyar iyayen bariki suka amshi kud’in, domin cikin mutanan Yarima sunce gidan sarauta in sun bada Abu dole ake amsa, ba’a miyar musu. Sannan an tsaida rana nan da wata biyu
Nan dai akayi addu’a tare da tashi kowa Ya wuce…..
Cikin Wanda sukazo daka gefen Yarima harda Mai Anguwa, ma’ana sarkin u/kanawa, wanda Kafin su zo shine aka bama damar yin bincike akan gidansu yarinyar da irin tarbiyanta, kuma yace babu wani matsala gidan tarbiya yarinyar take Yadai yi magana Mai Kyau akan gidansu bariki ???? ko Mai yasa yayi haka?? Bayan yasan yanda sarauta take?? Sannan hausawa na cewa shidai ramin karya kurarre ne, koma dai miye dalili za muji zamu gani….
Koda su waziri suka koma, sunyi ma Mai martaba bayanin irin gidansu bariki, Sun fad’a mishi gidan mutunci Yarima yake neman aure, sannan suka kara da fad’amai sai dai talakawa ne Sosai ba masu karfi bane, domin yana yin gidansu ya nuna hakan, kuma kaman gidan Haya suke, waziri ya kara da fad’in sai dai abunda ya kara burgeni duk da irin talaucin su , suna da wadatar zuci, basu da kwadayin abun duniya
Mai martaba yaji dad’i Sosai, tare da fad’in ina son Kafin Ayi bikin a nema musu Gida su koma, wannan kyauta ce daka gareni
Waziri yace an gama godiya suke .
Bariki bayan magabatan Yarima sun tafi, ta fito ta sami babanta na Bariki da sauran mutanan, nan suka bata kud’in, sannan ta sallami mutum biyu din akan saita kara nemansu. Tafiya sukayi suna godiya.
Kallon abbanta na Bariki tayi tace gskya aiki yayi kyau
Yace Sosai kuwa, sai naji dama auran nan da iyayenki na gskya kika had’asu, ina tsoran ranan da asiri zai tonu
Bariki tace karka damu, komai a tsari nake tafiyar dashi.
Yace dakyau tare da fad’in ni kam inda mmnki zata yarda Aida munyi aure
Bariki tace dagaske kakeyi?
Yace dagaske nake Wlh
Bariki tace Aikam zan mata magana sannan ni zan biya sadaki, da kayan lefe akwati guda biyu ai zan had’a maka Indai dagaske ne wlh, nima na samu lada
Yace ina godiya Kinga gwara Ayi auran, tunda nida ita Kar tasan Kar ne
Dariya bariki tayi tare da fad’in wannan haka yake.
Yarima Aliyu yana barin asibiti ,direct wajan bariki ya nufa, inda bata ma San da zuwanshi ba, saida ya kirata yace ta fito yana waje, Dan haka ta tashi ta fita ta sameshi a mota
Yarima kallonta yayi cikin jin dad’i tare da fad’in amaryata
Murmushi tayi cikin jin kunya tare da gaidashi
Amsawa yayi tare daja mata hanci, yace am so happy today
Kallonshi tayi tare da fad’in happy for wht?
Yace soon zaki zama tawa ….. Oh na manta kin ma riga kin zama, Ashe an bani ke har an biya sadaki…
Murmushi kawai tayi
Yarima yace yaushe za muje kiga gininki?
Tace a’a basai Naje ba,
Yace toh ni ina son kije ki gani , ya za’ayi kenan??
Tace zan tambayi Umma inta amince sai muje
Murmushi yayi kawai tare da kawar da maganan yace, Mai kike bukata Ayi da bikin mu??
Tace kaman me??
Yace event din da za’ayi
Shuru tayi tana nazari inta yarda Ayi event Kar a wajan event taga Wanda ta sani, Kar su fad’ama Yarima gskya Kafin ita ta fad’amai, kai gskya a’a.. Kallon Yarima tayi wanda shima ita yake kallo tace Yarima inaga Kar Ayi wani bidi’a…..
Kamo hannunta yayi tare da fad’in, a’a ya kamata muyi koda Abu d’aya ne, muyi dinner, inaga zaifi
Tace toh amma fah badan taso ba, ta dai amince ne dan Kar yaga kaman ta’ki yarda da maganansa…..
Kallonta yayi yace tunda an gama maganan event saura na akwati zan baki kud’i Kisai irin kayan da kike so, duk da za’a kawo miki daka gidanmu, wannan wanda zan baki akwai wanda nake bukata ki siya wanda only me zan dinga ganinki dashi, saiki K’ara da irin naki choice din .
Bariki ido ta rufe ciki jin kunyan maganan Yarima, ta rasa mai yasa Idan yayi mata wata maganan take jin kunya Bayan tasan ita bata jin kunyan magana gaban kowa, kodan Yarima badan iska bane sai yasa nake jin kunyan shi? Tabbas hakane domin duk Wanda kuka ga yana maganan banza gaban wani in kuka duba za kuga shiya bada dama Ayi mishi.
Sunyi fira akan in zai dawo zai Kawo Mata kud’i cash ta siya abunda take so sannan ya Mata sallama ya tafi ….. Toh andai ce duk abunda akace an yishi had’e da karya komai daren dad’ewa gskya zata bayyana, zamu gani asiri zai tonu Kafin biki ko sai Bayan biki muje zuwa……..
MARYAM OBAM