Labaran Kannywood

Bayan Shekaru 3 tana Wahalar Son ta Hadu da Adam Zango, a Karshe Ya Kirata a waya da Kanshi, Farin ciki Kamar Zai Kasheta

A Karshe dai burin Giwarmata Ya Cika bayan Shekaru 3 tana Wahalar Son ta Hadu da Adam Zango, Ya Kirata da Kanshi, Farin ciki Kamar Zai Kasheta.

Jarumi Adam Zango Ya Kira wata Babbar Masoyiyar shi a waya da kanshi bayan ganin yadda take matukar Kaunar sa da kuma Yabo a gareshi.

Ganin yadda take Matukar kaunarsa yasa aka nemo mashi numbarta ya kuma kirata da kanshi, Matar wacce akafi sani da Giwarmata tayi fice ne a kafar sadarwa na Tiktok inda ta bayyana cewa Tayi Kimanin Shekaru uku ta neman haduwa da gwanin  nata watau jarumi Adam Zango amma hakan bata samu ba.

Sai gashi a karshe bayan da a kullum take wallafa bidiyoyin jarumin na yabo da jinjina a Shafin ta na Tiktok, wanda harma rigima take tare mashi daga mahassadan shi.  Hakan yasa mabiyan ta a shafinta na Tiktok suka bayyana cewa so take kawai jarumin ya aureta domin sonda take mashi ya wuce misali.

Sai dai kuma ta fito ta karyata hakan inda take cewa ita bada aure take sonshi ba amma kuma idan har shida kanshi yace zai aureta to tabbas fa babu abinda zai hanata amincewa.

Gadai bidiyon wayar da sukayi dashi nan kamar haka.

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button