AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 33-34

??33 and 34??

Via Okai tsaye garden ya wuce cike dajin haushin Amal, wayarshi ya fiddo yana addu’ar Allah yasa Ameelah na online ko fira suyi ya samu natsuwar zuciyarshi,

Cikin rashin sa’a kuwah bata online tsaji yaja, ya tura wayar cikin aljihu sannan ya lumshe ido, kamannun ameelah yafara bayyanowa a cikin zuciyar yana murmushi, tunanin ameelah kadai ya isa yasaka shi farin ciki,
*** ***
Sai bayan la’asar lis sannan hilal yafita, bayan duk mai wakana ta auko tsakaninsa da matarsa ameelah, sabon wanka yasake tare sukayi wanka shida ameelah, yaudaikam yasamu farin ciki sosai a gurin ameelah, basu fito daga bandakinba saida sukayi alwala, suna fitowa hilal yajasu sallah, bayan sungama yafita…

Ameelah tafita tarakashi har waje, sannan tadawo cikin Falo yanayin Falon ta kalla yadda yayi kaca kaca, tayi ajiyar zuciyah, sannan tashiga gyara, komai batayi acikin gyaranba taji wayarta tayi karar shigowar text, da sauri ta ajiye aiki tanufi wuri wayar,

Sakon afham tagani, magiya yake mata akan dan Allah ta hau online, yayi miss dinta,

Murmushi kawai ameelah tayi, ta janyo data ta bude tana jiran shigowar massages,
*** ***

Afham yana zaune yaganta online wani dadi ya kama zuciyarshi don yanason chart da Ameelah, nan take ya manta da bacin ranshi cikin nishadi yake mata typng..

Afham “Ina fatan kyakkyawar mace ma mallakiyar zuciyatah tana cikin qoshin lpy.

Murmushi Ameelah tayi cike dajindadi

Ameelah “lpylau kaipa?

Afham ” ina cikin Annashuwa dajin dadi, Ameelanah yau babu wanda ya kaini farin ciki, gsky nazo duniya cikin sa’a dana hadu dake??

Ameelah ” ‘nima nayi sa’a kuma ina cikin farin ciki”

Afham “kinsan me? Inanan zaune nake a garden ganyayyakin itatuwa sai kadawa suke ga daddadan iska mai dadin shaka, ji nake dama muna tare! Don Allah Ameelah yaushe zamuyi aure??

Ameelah tazare ido, kafin tayi ajiyar zuciya

Ameelah “da wuri haka? Duka yaushe na sanka? ko soyayya bmu fara bapa”

Afham yayi murmushi, yana kallon text din ameelah azuci yake fadan, da ameelah tasan yadda yadamu dasuyi aure da wuri dabata fadi hakanba, kodan yabakan tawa amal zai nemi auren ameelah da wuri, bayan yadawo duniyar tunanin daya shiga yafara typng…

Afham “miye a cikin soyayyah Ameelah? Zamu dinga chart ne ko waya, kullum tambyr bazata wuce ya kke? Kinyi mafarkina? Gsky hotannan kinyi kyau sosae! Hmm wannan bashine soyayyaba, ni Kullum burina in kasance tare dake, amma sai dai ayita musayar kalamai ana bayyana shauqi, mezai hana muyi aurenmu kawai?

Gaban Ameelah ya fadi, lallai Akwai rigima, tana cikin tunanin text dn Afham ya kara shigowa
Yace “son gaskiya nake miki Ameelah sona aure, idan kina ganin biki sanni ba ko banyi miki ba zan miki bayanin komi a kaina ga hotunanah nan, don Allah Ameelah ki zamo tawah karki gujemin!

Ajiyar zuciah tayi bayan ta gama karantawa duk ta hada zufa, hotunanshi ne take kallo ta jinjina kai a fili tace gaskia Afham kyakkyawan gaskene!

Yayi matuqar burgeta, nan tafara saqe saqe a zuci, ji take daman Afham ta fara haduwa dashi kafin ta auri hilal,

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button