GOJE

GOJE 31 and 32

Ad

_____

31&32
Jiki a mace! ta nemi kujera ta zauna tana laluben number k’aninta wanda suka shirya ‘kula k’ulalliyar dashi. Yana d’aga wayar tayi kasa da muryata da fadin.” Sadiq na san dai yanzu ka samu labarin abinda ke faruwa yarinyar nan fa ta bayyana ina tsoron kada asirinmu ya tonu.”

Yace.”Aunty Maijidda kada ki damu babu yanda za’ayi asirinmu ya tonu tunda yarinyar ba zata iya sheda fuskokinmu ba, don haka ki saki jikinki kiyi mu’amula da kowa lafiya kada kiyi abinda zai sanya a gane cewa muna da hannu acikin al’amari!

Ajiyar zuciya ta sauke mai zafi! kafin tace.”Sadiq wallahi har yanzu na kasa samun nutsuwa gabadaya hankalina a tashe yake shiyasa na kasa zama a cikin jama’a na dawo gurina.” Yace.” hakan kuma da ki kayi shine zai janyo cewa a gane muna da hannu a cikin al’amarin ki saki jikinki kada ki kuskura ki tona masa asiri.”

Ta sassauta murya da fadin.” Insha Allah zanyi kokarin ganin na boye fargabata.” Yace.”Yawwa hakan shine abinda ya dace dake. amma har yanzu akwai kurah fa.”!

Tace.”Menene kuma.”? ‘Yar dariya yayi da fadin.” Kudin da ki ka bayar domin gudanar da aikin nayi wata bukata dasu, yanzu zaki bada wasu a biya masu hakki.”

Tace.”Yanzu Sadiq ina ka kai miliyan daya da rabi? cikin kwanaki bakwai kacal! fisabilillahi ba’a samu biyan bukata ba kuma sai ace sai na bada wasu kudin.”

Ya ‘bata da rai da fadin.” Kinga Aunty Maijidda duk wannan tambayoyin basu cancanta ba domin wannan aikin yafi karfin miliyan biyar amma don kin bada miliyan daya da rabi kike surutu haba kada ki bani kunya mana kawai ni ki tura min kudin ko kuma anjima kadan nayi miki dirar mikiya.”

Da sauri tace.” Aa ba sai kazo ba bari zuwa anjima ko gobe da safe zan tura mak…..Katseta yayi da fadin.” No! ni ban zarda a wayi gari ba, a yanzu mutanan suke bukatar kudinsu idan kuma kinfi so asiri ya tonu to.”

Da sauri ta girgiza kai da fadin.” Aah! bana bukatar hakan ka saurari alert yanzu.” Cike da farin ciki ya kashe wayar yana tsallan murna ya fad’i saman katifarsa yana kyalkyala dariyar biyan bukata, tunda ya fuskanci ta tsorata da al’amarin, cikin sauki ya samu hanyar samun kudi da ita.


Jaridar Leader shirp ce a hannunsa yana dubawa, hausawa sukace labarin zuciya a tambayi fuska, annuri ne kadai yake fita a kyakykywar fuskarsa, hakan kuma shi yake nuna tsantsar farin cikin dake cikin zuciyarsa…….Shigowarta gurin yasa ya d’aga kansa yana kallonta bai janye ba har sai da ta isa inda yake zaune, ta zauna kusa dashi itama tata fuskar a sake, take gaisheshi, amsawa yayi tare da tsareta da wani irin kallo wanda ke nuna mata zahirin so da tsantsar kauna.

Ad

‘Yar dariya tayi tare da lumshe ido, personality ta kirashi da suna na mussaman wanda take kiransa dashi tunfil-azal.

Da murmushi a fuskarsa yace.” Aysha Kinga Yaron da zaki kira da JARUMI! NAN.” ya fad’a yana nuna mata hotonsa dake jikin jaridar.

Ta tsirawa hoton ido tana girgiza kanta, ingarman namiji maji k’arfi kyakykwa tamkar SADAUKINTA murmushi tayi Ta kalleshi da fadin.” Lallai ni Ayshatu na sheda cewa babu RAGO! ga duk wanda ya amsa wannan sunan, ha’kika wannan yaron ya cancanta ayi masa komai saboda jarumtarsa! da kuma sadaukarwarsa.”

Kansa ya girgiza da fadin.” Sosai kuwa Aysha na jima ina nazari da tunanin irin alkairin da zanyi wa yaron, Munyi waya da Asp Musa Baharu mun tattauna muhimman maganganu dashi na fahimta, ya kuma bani tabbas a kansa cewa ZINATU ta samu dukkanin kulawar da ta dace a gurinsa, ya tabbatar min da cewa yarinyar tana cikin koshin lafiya babu wani mugun rauni! a jikinta bayan wanda ta samu kafin zuwan shi wannan yaron da ya taimaka mata, sannan bayan haka kuma ya sheda min cewa daga zarar sun gama gudanar da binkicen daya dace to dashi kansa da yaron zasu kawo min ZINATU har gida, sosai yaron ya taka muhimmiyar rawa akanta babban abinda yafi burge ni dashi yanda yayi namijin kokarin ganin ya karya alkadarin takadirin d’an ta’addan nan! da ya addabi! ‘kasa da al’ummar dake cikinta, Aysha wannan yaron jarumtarsa! har ta zarce tawa.”

Murmushi tayi idonta cikin nashi tace.”Ina shakku! akan maganarka ranka ya dade, domin kuwa ban yarda cewa akwai wanda yafi mijina jarumta ba, har yanzu kana nan yanda kake Jarumi! a gida kuma jajurtacce a waje.”!

Hannuwanta ya rike yana jifanta da wani irin kallo………Har yanzu Tana nan mak’ale a zuciyarsa, sam bata tsufa a idonsa, duk kwanan duniya sonta nunkuwa yake a zuciyarsa, Aysha ta zame masa jinin jiki………. Ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta fahimci abinda yake da akwai, murmushi kawai tayi, tana mamakinsa, baya tsufa da soyayya, kullum da irin kalar soyayyar da yake nuna mata idan suka kad’aice, babu wani abu da ya samu tangard’a a zamantakewar auransu.

kusan a tare suka mike tsaye, ‘kugunta ya ratsa da hannunshi, ya riketa sosai a jikinsa, kai tsaye bedroom suka nufa domin mutunta junansu.


To Ranar da zasu cigaba da gudanar da binkice a sansanin UBAN DABA! Asp ya bada umarnin kwance masa sasarin! dake daure da k’afafunsa! ‘yan jarida mane ma labarai suka cika harabar gurin, koda ganin fitowarsu sai sukayi caaa! a kansu sunayi musu tambayoyi.

Ad

_____

1 2 3Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button