BidiyoLabaraiObasanjo

Bidiyon Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo Yana Kwasar Zazzafar Rawa A Bainar Jama a

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana a matsayin wanda ya lashe gasar rawa tsakaninsa da jarumar Nollywood Adedoyin Kukoyi.

A wani bidiyo mai nishadantarwa da bada dariya da ke ta yawo a kafar sada zumunta, an ga Obasanjo ya na juyi wurin rawa wanda ya sanya jama’a ihu.

Amma ana dab da gangar za ta tsaya da kida a shagalin bikin, Obasanjo ya tsinkayi wurin rawan da irin salonsa mai bada mamaki.

Hausa Legit ta ruwaito Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya mai shekaru tamanin da hudu ya bayyana salonsa da irin karfi da jikinsa ke da shi tamkar matashi a wurin rawa da jaruma Adedoyin Kukoyi.

Bidiyon mai nishadantarwa da bada dariya ya nuna tsohon shugaban kasar da jarumar inda suke girgijewa.

Sun yi rawa ne ga wani kidan Yarabawa inda ganguna masu yawa da zaki ke buga musu sauti.

A yayin rawar da ta birge masu kallo kuma ta saka suka dinga ihu da tafi ga tsohon shugaban kasan, an ga Obasanjo ya yi juyin masa a filin rawar.

Obasanjo ya bayyana a filin rawan Amma a yayin da kidan ya shige shi aka yi kuma wata irin kida, tsohon shugaban kasan ya tsaya sannan ya cigaba da girgijewa.

A yayin wallafa bidiyon, Adedoyin Kukoyi ta rubuta:

“Ni da kaina na bukaci mu yi rawa kuma babu wasa ya amsa kirana. Masu kallo, ga rawa na da tsohon shugaban kasar Najeriya, Chief Olusegun Okikiola Aremu Obasanjo.”

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button