NOVELSUncategorized

NAJEEB 20

Bayan fitan Aisha, “Hauwa ta kalli Zarah tace miss danna waya, ya kamata kizo muje club wata rana wallahi 

Zarah dariya kawai tayi, Amma cikin ranta tace Allah ya kyauta, ya kuma shirya,”ita Zarah mamaki suke bata, yanda basa boye ma kowa su y’an bariki ne,
iyayensu sun turosu karatu amma bashi suke ba, kwata kwata yau sati biyu data sansu amma ta gane irin halinsu.


KANO NIGERIA 

washe gari da safe, tunda ibtisam ta tashi tayi sallah asuba, ta kasa komawa bacci, domin d’aukin zata skul yau, “Tana zaune sai k’ara gyara kayanta take 

Granny dake kwance taja tsaki tare da fad’in “ni Dallah kashe min wuta in samu In kwanta 

Ibtisam tace “da kwanciyan kike da wuya? Kunji min mata, ita da bata kwanciya saida wuta, sai anyi dakyar take kwana ba wuta shine take wani fad’in in kashe wuta 

Granny tace kyaji dashi, nidai kashe min wuta in kwanta 

Ibtisam tace oho dai, yanzu dai Gari zai Waye, haske zai fito, sai muga ta tsiya ai 

Granny tace aikin banza, ni zanyi Wlh wannan bokon da zaki baso nake ba, ko kad’an wlh, gaba d’aya kinbi kin fitsare ai Indai kika tafi wannan bokon Nasan nan gaba fito na fito zaki da mutane 

Ibtisam tace Sosai kuwa, kaman kin San abunda ke raina kenan “inna kammala karatu zan kaiki a rufeki a wani waje yanda bazaki dinga ganin kowa ba, ko fita bazakiyi ba, “hatta wannan goran da kike ci cikin dare ki dameni shima zaki daina ci 

Granny ta tsuke baki tare da fad’in aikin banza aikin hofi, “Dan uban mutum basai ya kasheni ba, karshen boko 

Ibtisam dariya ta saki sannan tace”in lokaci yayi ai zaki mutu,”saurin Mai kikeyi 

Tsaki Granny taja tare da k’ara janyo blanket ta rufe jikinta 

Bayan gari Ya gama wayewa wajan karfe 10 saiga Dad yazo gidansu ibtisam

Sanda ibtisam taji sallaman Abba, ba k’aramin dad’i taji ba Sosai. 

Da yake Dad zaizo sai yasa Abba bai fita kasuwa ba, ya tsaya jiran Dan uwan nasa, “gaisawa sukayi da Dad da Abba, “Abba yace ai yanzu nake tunanin in kiraka 

Dad yace bacci ne ya mamaye ni, naso in wuce tun 8, gashi yanzu 11 ya kusa, “Ina mama? 

Kafin Abba ya bashi amsa, “saiga Granny ta fito tana fad’in gani ai yanzu na jiyo muryanka, har kazo? 

Yace eh mama ina kwana? An tashi lafiya? 

Granny ta amsa da lafiya kalau, tare da fad’in “ga abinci can an ajiye maka, tun d’azu 

Yace Aikam yunwa ma nakeji babu abunda naci.

Ummi ce ta fito tana fad’in wai ai abincin ma yayi sanyi, ina shirin d’aura na rana 

Dariya dad yayi tare da fad’in haka zanci mu kama hanya, “Wai ina ibtisam dinne ma? 

Ummi tace tana ciki 

Granny tace ja’ira gaba d’aya ta hanani bacci jiya, sai shirya kaya take cikin dare kaman wata aljana 

Dariya Dad yayi ya fara cin abinci 

Granny d’aki ta koma inda taga ibtisam tana k’okarin saka hijab, “granny ta tabe baki tare da fad’in ai saiki fito 

Ibtisam tace ko baki ceba dama zan fito 

Granny tace ke yanzu har wani murna kike zaki jami’a koh?

Ibtisam tace Sosai kuwa 

Uhm Granny tace, tare da fad’in yanzu saiki tafi ki barni ni d’aya? 

Ibtisam tace Sosai kuwa”keda kike son inyi aure miye Abun damuwa a ciki dan Naje skul, tunda bakya son ganina a gidan? 

Granny tace haba takwarata ai aure daban, nasan in aurene zanyi kewarki Sosai, kuma zansa MA raina aure kikayi, “amma in karatu ne Kinga shida banbanci ai “kuma karki manta aure dai shine mutuncin y’a mace 

Ibtisam tace toh yanzu Mai kike nufi? 

Granny tace babu komai, nidai Wlh bason wannan karatun nake ba kum….

Ibtisam tace ya isa haka, yanzu naji zance Wlh Granny ki daina min irin haka, bafa naso, kowa na karatu duk cikin jikokin ki amma nice kad’ai kika sama ido.

Granny tace Suwa suke karatun? 

Ibtisam taja tsaki tare da fad’in Zarah bata karatu? Koshi NAJEEB baiyi karatu ba, ko Ahmad baya makaranta? 

Granny tace kinma uwarki tsaki bani ba, shi miskili aiya gama tun tuni, baki ga illar da karatun Yaja mishi ba? Sai rashin Kunya babu abunda ya iya, sai raina mutane. 

Sannan ita Zarah AI kin girmeta, yanzu AI abun kunya ne, mu Hausa Fulani ace kanwa ta Fara aure yaya batayi ba, ai sai Ayi dakai. 

Sannan Ahamd Dan k’aramin yaron ne za’a mishi aure? Tunda a garin mahaukata muke ba. 

Ibtisam tace oho dai, kwata kwata shekara d’aya naba Zarah, “sannan ni Wlh ba Abun kunya bane dan wacce na girma ta rigani aure ba, tab lallai ma Granny, Toh kunyar Mai zanji, Bayan nasan aure lokaci ne? 

Granny ta cabe da fad’in ina ko zakiji tunda baki Santa ba, ni Wlh kina bani tsoro.

Ibtisam tace ke kika ga wannan, shifa aure lokaci ne, “amma ku Hausa Fulani saiku dinga ganin kaman mutum ne baya son yi, Yooo koda ina son inyi auren ai ban isa inyi ba sai lokaci yayi, “amma duk kubi ku damu mutum ya’ki aure ya’ki kaza “wlh ku cire al’ada ku Kama addini. 

Granny tace uwarki muka Kama Inba addini ba? 

Ibtisam tace al’ada mana, wacce kuka maidashi kaman addini 

Granny tsaki taja tare da fad’in na fiki sanin aure lokaci ne, “amma da niya ba, tunda in baka da niyan aure taya lokacin zai zo? 

Ibtisam tace nifa Kinga Granny ban son surutu, kawai ki tafi ki barni.

Granny tace oho dai, aure dai nan da wata biyar, zamu Kai mutum Dan ubansa ko baya so, dole ya zauna, “sai muga boko ai 

Tsaki ibtisam taja tare da fita ta nufi falo tabar Granny a nan, tana fad’in “Aiko mutuwa za kiyi sai anyi wannan bikin yarinya kaman Mai iska 

Koda ibtisam ta fito falo gaida Dad tayi cikin girmamawa.

Dad amsawa yayi tare da fad’in ina fatan kin shirya mu kama hanya koh? 

Tace eh na shirya 

Yace toh d’auko kayanki kikai Mota driver yasa miki a booth muzo mu wuce 

Tashi tayi ta koma d’aki inda ta iske Granny itama na k’okarin fitowa sukaci karo 

Granny tace au fadar dani zakiyi?

Ibtisam tace sorry ban ganki bane 

Granny tace miye soro? 

Ibtisam tace kiyi hakuri nake nufi 

Granny tace yau naga tsiya, kefa tunda zaki tafi wannan makarantar kike nuna mana isa isa, kike ganin kin isa damu, wuyanki yayi kauri 

Ibtisam ta Lura da Granny fushi takeyi dan zata skul ta barta, dan haka dariya kawai tayi ta wuce, ciki 

Granny tayi gaba tana mita 

Ibtisam d’auko kayanta tayi ta fita dashi taba driver yasa mata a booth 

Granny na zaune a falo tana ta galla mata harara,”ibtisam kam dariya takeyi k’asa k’asa. 

Abba ya kira sunanta da mamana 

Tace na’am Abba 

Yace toh Ina son ki sani, kin San yanzu dake da matar aure banbanci kad’an ne? “kin San mai yasa nace haka? 

Ita matar aure an d’aura aure mutane sun shaida, dama shi aure shaidu yake bukata 

Idan aka bada sadaki, sai shaidu kuma 

Toh ke mun amsa sadakin ki, saura shaidu kawai su shaida, ina son ki sani mun amsa kud’in sadakin ki domin munba Kabir ke, kuma munyi bincike dan gidan mutunci ne, ina son kiji tsoran Allah koda Kinje makaranta karki kula kowa, sannan ki kame kanki, karki manta inmu bama ganinki Allah yana kallonki shida ya halicceki , “sannan ba tsoranmu muke so kiji ba, face kiji tsoran Allah daya halicceki 

Sannan shi mutunci madara ne, idan kika kama kanki babu wani mutumin banza dazai zo miki, amma idan kika banzatar da kanki toh ko wani irin mutum zaizo gareki, “sai kiji ana fad’in tana da farin jini wanda ba haka Abun yake ba, yawan samari ga d’iya mace ba alkairi bane “bazan tsaya miki dogon magana ba koh bayani ba, Nasan kina da ilimin addini, abunda zan fad’a miki a matsayina na mahaifinki shine kiji tsoran Allah a duk inda kike, Allah yayi miki albarka 

Ibtisam wani irin hawaye ne ya zubo mata, tare da amsawa da Ameen 

Ummi tace toh Allah ya taimaka abbanki ya Gama cewa komai, sai dai in k’ara da komai kike bukata, bamu ce ki tambayi kowa ba, ki kiramu zamu baki, koda kuwa wanda zaki aura karki tambaye shi, domin har yanzu nauyinki na kanku, tunda kina gabanmu, “Allah ya bada Sa’a, yayi miki albarka 

Ibtisam ta amsa da Ameen 

Dad yace Toh Bari mu kama hanya,tare da tashi 

Abba kudi yaba ibtisam dubu ishirin tare da fad’in gashi ki ri’ke wannan, ya kamata ki bud’e account 

Tace Nagode Abba, tare da fad’in zan bud’e insha Allah “Zarah Nada account in za’a min sa’ko sai inyi amfani da nata

Abba yace hakam yayi 

Granny tace Allah ya kiyaye hanya, Tana fad’in haka tayi ciki Tana y’ar share kwalla”yau ibtisam zata karatu ta barta ita d’aya bata da abokiyar hira, ” Granny kaf jikokinta babu wanda take so kaman ibtisam sai kuma miskili duk tafi son su.

Su Abba da ummi har waje suka rasa Dad, inda Abba yake fad’in wannan makarantar dai mama bata sonshi 

Dariya Dad yayi yace kasan ita mama bazata gane muhimmancin ilimi ba, gani take duk Wanda yayi ko zaije Tana mishi kallon d’an iska, kuma ba haka Abun yake ba, duk da akwai Mara sa ji, Aiba duka aka taru aka zama d’aya ba 

Abba yace hakane, Amma yaran dai sai a hankali, kasan muke kasuwa, muna ganin yara y’an makaranta Wanda suke zuwa siyan kaya, in kaji irin firansu babu kamun kai, kai Abun dai sai Addu’a, Allah dai ya shirya mana zuri’a 

Dad ya amsa da Ameen 

Ibtisam da dad suka shiga mota, ibtisam ita da Dad duka baya suka zauna “Da gaba zata shiga Dad yace ta dawo inda yake, dole ta koma ta zauna dashi a baya, suka Kama hanyar zaria 




ABU ZARIA

Bayan sun isa cikin makarantar, Dad kiran Zarah yayi a waya tare da fad’a mata ta fito waje yana kusa da hostel d’insu .

Tace OK Dad amma baka fad’a min zaka zoba? Gani nan zuwa. My Dad kayi min surprise visit, Tana fad’in haka ta kashe wayan 

Dad bayan ta kashe wayan kallon ibtisam yayi tare da fad’in dama bata san zaki zoba yau? 

Tace eh bamuyi waya ba 

Dad yace sai yasa take mamakin zuwa na 

Zarah ce ta fito, cikin jallabiya tare da yafa gyalen jallabiyan akanta, bud’e kofar motar yayi ganin ibtisam yasa ta saki ihu tare da janyota ta fito daka motar “rungumeta tayi tana fad’in wayyo yau ina cikin farin ciki. 

Dad shima fitowa yayi, yana fad’in shine tun Farko baki fad’amin an hanata zuwa skul ba? 

Zarah tace Dad wlh kwata kwata na manta, kuma nasan inda na fad’a maka daka sa Abba ya barta,”and abunda yasa ma ban damu in fad’a maka ba, ta fad’amin yanda sukayi da kabir sai yasa. 

Dad yace Toh shikenan, gata na Kawo ta, sai a d’age da karatu banda wasa, musamman ke ibtisam da aka wuceki wajan sati biyu da wani abu yanzu, saiki dage da karatu Sosai 

Ibtisam tace insha Allah zan dage sosai

Dad yace Toh Allah yayi muku albarka 

Su duka suka amsa da Ameen 

Dad ya kalli Zarah yace Mai kike bukata Zanzo in wuce, 


Tace Dad inada kayan abinci,kasan da yawa na siya mana, tunda mu biyu ne, sai kuma Abba ya hana ibtisam zuwa, so yanzu tunda ya yarda wlh nafi kowa murna “ni yanzu Dad kud’i kawai zaka bamu 

Dad yayi murmushi tare da bud’e Mota ya bud’e wani k’aramin akwati ya d’auko kud’i ya mi’ka ma zarah da ibtisam yace ko wacce ga 100k sai ku dage da karatu banda wasa, sannan banda bin kawayen banza 

Ibtisam tace mun gode

Zarah tace insha Allah Dad zamu dage

Yace toh Bari mu kama hanya 

Driver ya ciro ma ibtisam kayanta daka cikin akwati, “Zarah ta tayata d’auka sukai cikin d’akinsu inda hauwa ke kwance ke bacci 

Ibtisam kallon d’akin tayi gado ne guda hud’u, sama da k’asa, d’akin ba wani girma gareshi ba, sai kayan sawansu dake akwati, dana abincinsu sai su gas Mai had’e da cylinder. 

Gadon ibtisam dana Zarah sama da k’asa, ibtisam tace ita saman take so, tare da fad’in kar indau k’asa Zarah ki fadomin akai 

Zarah ta kwashe da dariya tare da fad’in sai kace wata giwa 

Dariyan Zarah ne ya tashi hauwa dake faman baccin gajiya

Hauwa tace Zarah kinyi Bakuwa ne? 

Zarah tace itace cousin d’ina da nake fad’a muku, gashi yau tazo skul 

Hauwa tace eyya sannu da zuwa, ibtisam koh? 

Ibtisam tace eh haka Sunan yake 

Hauwa tayi dariya tare da kallon ibtisam sama da k’asa, lallai wannan Tana dakyau zatai kasuwa, but sai dai na ganta da hijab, Allah yasa dai ba y’ar saka hijab bace

Ibtisam cire hijab d’inta tayi tana fad’in Wlh na gaji Sosai 

Idon hauwa na kanta, ba komai take tunani ba, sai inta had’a ibtisam dana miji zata samu kud’i 

Hauwa tayi caraf tace ai Wlh ana zafi ma, gwara ki cire kisha iska ga gajiya duka 
.ibtisam tayi murmushi tare da fad’in Wlh kuwa yau naga garin kaman za’ayi rana, “koda yake naga is lyk kaman ke baki fita ba, tunda naga yanzu kika tashi daka bacci. 

Hauwa tace Aifa kam, yanzu na farka 

Bud’e kofar akayi aka shigo dan basu rufe ba. 

Aisha ce ta shigo hannunta ri’ke da y’ar jakarta, fad’awa tayi kusa da hauwa tana fad’in Washhhhh Na gaji Wlh “tare da kallon hauwa tace ke kin had’ani da jarabban mutumi gashi ya daure min hannu da kaca, babu daman in tureshi, gashi shegen hariji, Kinga irin cin da yayi min kuwa? “amma wlh ke y’ar iska ce hauwa da baki fad’amin ba, cikin dare yayi wajan sau hud’u ko biyar zance ma? ni nama manta wlh saboda tsabaragen Wahala, gashi cin hauka yake ma mutum yana wani buga maka banana cikin hq kaman ana buga guduma akan k’arfe 

Hauwa dariya ta saki tare da fad’in sai yasa naki zuwa ai,.

Aisha tace Aida kin fad’amin irin cin da yake ma mace Aida banje ba wlh, duk da ina neman kud’i gashi wai shegen dubu hamsin Yaban duk wannan cin da yayi min 

Hauwa tace toh Ina laifi kin samu 50k Kinga saiki saka ruwan dumi ki gasa wajan 

Dariya Aisha tayi tace uhm ai naga rayuwa wlh, na ciyu iya ciyuwa wlh, Amma yanzu tunda na samu kud’in babu laifi Kinga anjima in Naje club na samu na drinks 

Dariya suka saki, hauwa tace nima kya siya min, “yauwa Ina kaso na? Dubu ishirin din? 

Tsaki Aisha taja tare da fad’in kin manta duba d’ari ne, “bude jakarta tayi ta kirgo dubu biyu ta mi’ka ma hauwa tana fad’in gashi 

Hauwa ta amsa Tana fad’in raba mugu da makami ibada ne 

Aisha tace au nice muguwar? 

Hauwa tace a’ah Indo 

Aisha kallon ibtisam take da take ta faman kallonsu tana mamaki, tace wannan black beauty dinfa? 

Hauwa tace itace cousin din Zarah yau tazo.. 

Aisha tace eyya ibtisam koh? 

Hauwa tace eh ita 

Aisha ta kalli ibtisam tace sannu ibtisam kice yau kika shigo skul din? 

Ibtisam tace yauwa, “eh wlh yau na shigo 

Aisha tace naji ai course d’aya muke karanta, medicine department dinmu d’aya, karfe 4 muna da lecture saiki shirya, domin shegen lecturer dinnan baya wasa, inya rigaki shiga kin bani, domin wlh ko zaki mutu baki shiga, gashi shegen shi babu ruwanshi da mata, balle mukai kanmu ko nono ya taba. 

Hauwa dariya tayi tace Tab, sai yasa naga bakya wasa da course d’inshi, duk inda kika je indai zai shigo sai inga kin dawo.. 

Aisha tace ba dole ba, in dawo ba, “nifa duk iskanci na, ina son in fita da First Class,in ban samu ba sai ince second class. 

Ibtisam da Zarah kam jinsu suke, ita Zarah firan nasu baya bata mamaki danta saba, jin Wanda yafi wannan ma

Ita kam ibtisam mamaki take, yanda suke ta sakan zanje, lallai dole maza suce macen da take jami’a idonta ya bud’e, Allah dai ya kyauta, danna wayarta tayi karama taga 3:30 tashi tayi ta d’auko akwatinta ta bud’e ta d’auko wata jallabiya milk colour, da gyalenshi domin ta shirya dan tana fashin sallah

Zarah tace Mai zaki ci? 

Ibtisam tace na koshi saida muka biya muka ci abinci Kafin muka karaso 

Zarah tace au na manta Ashe da Dad kika zo, nake wani tambayar Mai zaki ci, dama Nasan Dad dole ya siya muku abinci 

Hauwa tace OH dama Dad d’inki ya Kawo ta? Shine baki kirani IN gaidashi ba? 

Zarah tace naga kina bacci ai shi yasa 

Karfe hudu saura Aisha da ibtisam suka nufi lecture inda suka tarar lecturer din bai shigo ba, hakan yasa ibtisam sauke ajiyan zuciya,. 

Karfe hudu dai dai sai gashi ya shigo din, saurayi nema, ba wani babba ba, ita ibtisam tasha ko zata ga babban mutun irin wanda ya manyanta sai taga matashi, wanda bai wuce sa’an Kabir d’inta ba

Lecture ya farayi musu, ibtisam gaba d’aya hankalinta nakan abunda yake musu, wannan ne shigarta na farko class, gashi kuma an wuceta, shi yasa gaba d’aya ta maida hankalinta wajan Dr jibril, domin sauraran abunda yake musu 

Lokaci d’aya yace zai basu text yanzu kuma 20mrk 

Ibtisam ido ta zaro tare da furta na shiga uku cikin ranta, yanzu mai Zan rubuta? 


(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());



Idonshi ya sauka a kanta kaman zaiyi magana kuma saiya basar 

Ibtisam kam gaba d’aya tsoro ya hanata komai, gashi ance baya wasa, dan haka kawai ta tashi ta fita tabar class din domin tasan kota zauna ta rubuta babu abunda zata ci, toh maima zata rubuta ita da yau ta Fara attending lecture 

Ido Dr jibril ya bita dashi……… 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button