Uncategorized

TAKUN SAKA 49

 *_Typing????_________________qq

*_MATAYEN ƘWARAI SARAKAN ADO DA ƘAWATA JIKI DA KWALLIYA KUNA INA NE?._*

_Maza ku garzayo da gudunku ga mutunuyar taku maida tsohuwa yarinya ta sake dawo muku da sabon salo, sabon sunfarin kayan gyaran jiki na mayika da sabulai ƴan gaske????????._

*Kayan kwalliya na mg’s skin care zasu maidaki shalele ƴar ƙwalisa tamkar wata ɗan daren sha biyar koda kina da kishiya ƴar Morocco bata girgizaki ba, balle saurayi ɗan son ƙyale-ƙyale da ƙawa ga burwallensa????????????*.

_Kayan mg’s skin care nada matuƙar sirrika da inganci irin wanda sai an gwada akansan na ƙwarai. 

*MUNADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA*????????

Hajiyata shin menene matsalanki, pimples ne?

Spot? sunburn,acne, stretch marks, knuckle, wrinkles, Black head,ko kinshafa Maine yabatamiki jiki

Inamai shaidamiki cewa ynx ne lokacin dayakamata kiyake dukkan wadannan kema kidinga fita sakayau abunki baruwanki da kunshe fuska ko kice sekinyi makeup hjy fita zar abunki kinuna ainihin natural beauty dinki????domin kayanmu gbdynsu organic ne babuna bleaching zssu sa ki haskaka fatarki tayi ta kyalli kamar madubi ze fiddomiki d ainihin natural beauty dinki ne????kunaji barin fadamuku wani Abu billah wannan prdcts damuke dashi ynx Koda kudinki seda rabanki domin duk sunzarce nabaya ankaramasu abubuwa dayawa masu matukar anfani agyaran fata????Ina Wanda basasan shafa Mai koda sabulun kawai kike anfani dashi inamai tabbatar Miki zkg ynd jikinki zekoma luwai luwai????

Soap:3k

Beauty kit:12k

Chat:08062991549

07066210195

Call :07046881166

08064532391

Instagram:glow_with_mgs

Facebook:mg’s skincare

 amare inakara shaidamuku duk wacce tayi anfani d kayanmu Bata bukatar gyaranjiki sedai ra’ayi????

Masoya kunanan kauna yanda nakwashe aljihu domin nafarantamuku kuyi achieving goal dinku pls Nima kunanan kauna kufarantamin????????aljihuna yafarfado hilis karnakoma kauyenmu???? 

Yar shawarmannan duk nasaba???? hilis kugarzayo arabani da kaya????

Nd guest what????

Duk Wanda yy siya 10k zuwa sama zesamu Karin gift????

Pamper your skin????‍♀️

Shine like a bride????????

Glow????????‍♀️

______________________

*_Chapter Forty Nine_*

………..Kamar almara Hibbah ta koma normal, dan cikin ikon ALLAH ma yau da ta kasance ana gobe tarewar tata idan ka ganta bazaka taɓa ɗaukar ta jigata jiya ba. Baƙi sun fara isowa daga ɓangaren dangin Hajiya mama da mai jiyyarta ta sanar dasu ta waya bisa Umarnin hajiya maman ba tare da sanin Ummi ba. Sai abokan arziƙin Ummin na nan cikin gari dake zuwa dan shirin abincin gobe idan ALLAH ya kaimu ɗin, tunda tace biki zatai sosai akan tarewar autar ta. Sannan kuma itace uwar ango ma ta wani fanin dan Isma’il ya cancanci hallaci daga garesu bayan na bashi Hibbah kuma.

_______________

       Su Habib ma da suka dage da shiri daga can ɓangarensu sun ƙagara gobe idan ALLAH ya kaimu tayi Aunty Queen ɗinsu ta dawo gatesu, dan sunyi matuƙar kewarta duk da suna gaisawa da ita su ta wayar Ammar da Master ya basu number. Sun ma zo sun ganta sau biyu bada sanin Master ɗin ba duk da dai Ammar ya gumtsa masa batun zuwan nasu. Dan lokacin shi bayanan ma saboda ƴan tafiye-tafiye da yayi a ɗan tsakanin nan akan wasu ayyukan dayake son kalmashe bakinsu dan hutu yake son ɗauka dogo dazai raɓashe ya ƙwalle da amaryarsa. 

*_RANA BATA ƘARYA……_*

       Tabbas rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya. Dan kuwa a yau aka tashi da gagarumin bikin ƙarin girma daga headquarter na ƴan sanda bisa ƙoƙarin mai gayya mai aiki I.G da wasu manya-manya da suka bada gagaurumar gudunmawa domin girmamawa ƙoƙarin su Master ɗin akan zaƙulo su Dr Sufi dake gidan yari sunacin azabar rayuwa data cututtukan da suka taso musu bisa ƙazantar homo da suka aikata. Dan takai ko a cikin prison ɗin yanzu ba’ako buƙatar son zama kusa dasu saboda shegen warin da sukeyi. master kam shi ba’a ma batunsa. Dan wani irin ƙuraje ke fito masa a jiki na allurar poison ɗin da Master yay masa. Hakama Abba Halilu yana nan yanacin azabar ƙafa da alamun ruɓewarta duk ya bayyana gareshi.

        Wani irin gyara da ado na musamman akaima harabar headquarter ɗin tun a yammacin jiya. Zuwa yau kuwa aka ƙarasa ƙawata ko ina har an fara tarbar manyan baƙi tun kusan ƙarfe bakwai na safe. 

         Dan ta ko’ina duk wani mai ruwa da tsaki akan wannan taro yana can yana ƙoƙarin shiryawane domin isowa akan lokaci. Musamman ma amarya mai tariya biyu Hajiya mandiya Muhhibat Aliyu Hamza Gwarzo mai zamani????????. Dan wata irin tsadddiyar riga mai azabar ƙyau kalar sararin samaniya su Habib suka aika mata da ita tare da duk wani abinda zai cika adon nata da ƙawatashi. Sai kayan kuma da zatai amfani dasu a wajen ƙwarya-ƙwaryan walimar da suka shirya nacin abinci daga bakwai na dare zuwa goma. Da farko Master da suka sanar masa ya tirje sai da Abdull yasa baki da ƙyar ya taushesa ya amince. Dan koba komai yana son ganin farin cikin ƴan kannen nasa kuma ta wani fanin. Itama mai gayya mai aikin yasan zataso hakan kodan ya goge laifinsa na nanata zancen satota da bata gajiya dayi idan tsiwar ta tashi, tare da ɓoyema ganinta da yayi tamkar almara.

         Cikin ƙanƙanin lokaci mai kwalliya ta tsantsarama Hibbah da zuciyarta ke cike da ɗoki da kewar son ganin mijinta. Sai dai tanata ƙoƙarin dannewa a zahiri. Ana gab da kammalawa Ammar ya shigo yake sanar musu suyi sauri harsu Master sun iso za’a wuce. Babu ɓata lokaci mai kwalliyar ta kammala mata komai ta fito tsaf tamkar wata ƴar daren sha biyar. Ga ƙibar da tayi ta ƙara ƙawata tsarin shigar tata masha ALLAH.

      Ummi kanta da su Zahidah kasa haƙuri sukayi sai da suka tanka wannan ƙyawu da Hibbah tai. Su Yaya Muhammad dake jin wani ɗunbin farin ciki suka zagayeta suna zuba mata ruwan hotuna. 

        A haka suka fito da Hibbah harabar gidan inda su Master ya ke tsumayen fitowar ta su. Akan su Habib da ke zagaye da shi cikin shiga iri ɗaya tamkar wasu bodyguard ta fara sauke ido. Taja gajeren numfashi da satar kallon mai gayya mai aiki dake sanye cikin wasu Haɗaɗɗun suit sky blue kalar kayan jikinta. Shi kansa tun fitowar tasu yay mutuwar tsaye yana jan wani hargitsatstsen numfashi da ajiyar zuciya har su Habib na iya jinsa.

     Kunyar Ummi data Yaya Muhammad ta hanashi xuwa ya tareta ya rungume ko zaiji nutsuwar abinda yakeji na ratsa ɓargonsa zuwa cikin jini. Maimakon ya nufi Hibbah sai ya matso kusa da Ummi cikin girmamawa ya gaisheta. Ummi ta amsa cike da fara’a tana sanya masa albarka shi da su Habib da suka ƙaraso suma suna gaida Ummin.

         Ya gaisa dasu Yaya Muhammad ma sama-sama kowa ya shiga mota dan jiransu akeyi. Duk da tsokanar da su Habib kema Hibbah bata iya cewa komai ba dan gaba ɗaya idanun Master sun hanata sukuni. Duk yanda yaso daurewa ya kasa. Suna shiga motar da Habib ya kawosa a ciki ya jawota jikinsa ya rungume. A tare suka saki ajiyar zuciya suna sake ƙanƙame juna har yana mamakinta. Habib dai yi yai tamkar bai gansuba yaja motar suka fice a jere da sauran nasu Yaya Muhammad.

        A cikin kunnenta ya raɗa mata “I miss you so much Baby luv”.

        Hibbah da ɗunbin kewarsa da kunya ke zagaye da ita ta sake cusa kanta jikinsa tana mai shaƙar ƙamshin turarensa da yay mata matuƙar daɗi. Itama a hankali tace, “Ni dai bana kewarka”.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button