Comment on TAME GARI Page 51 to 60 (The end) by Unknown

****************
“Wai me kake Fadi ne Habee?”
“har yanzu nakasa fahimtar inda zancenka ya dosa”.Kana nufin kicemun ni ke dauke da ciki! Cikin ma Kuma na haihuwa to ta Yaya hakan zata kasance?
Kowa a gurin shuru yayi Yana sauraren maganarta,Wanda Habeeb yaso yin shuru ne Dan kada suji komai,Amma ganin tana neman Raina Masa hankali yasa shi fadin,
“Kada ki daukeni marar hankali Mana” ni Zaki kalla ki dinga tambayar wai kinada ciki ko bakida shi! Bayan kin fi kowa sanin ta’asar da Kika aikatamin,to wallahi ki sani bakiyi a banza ba duk irin son da nake yiwa mace,in har ta Nuna Bata son hada jini dani to babu abinda zai hanani tsanarta Nima sann……
Daddy ne ya dakatar dashi ta hanyar fadin,
Wai me ke faruwa ne,kun tsaya kunata wasu maganganu marasa tushe,ku sanar damu meke faruwa?
Ga mamakin su gani sukayi Habeeb ya fashe da kuka tare da fadin,
“Daddy, sajida ta cuceni,cikina ta zubar!
Innalillahi wa’innailahir raji’un!
Kowa ya shiga Fadi a dakin,inda hakan yayi dai dai da sallamar su Naseer shida Zainab.
Runtse ido Sajida tayi tana me tunanin ta yadda hakan ya faru.
*MAFARIN LAMARIN*
Tun lokacin da suka yanke wannan shawarar ita da laila,sannan da dataje gida ta fada wa mamanta Nan suka yanke shawarar abinda suke ganin zai fisshe su family doctor dinsu suka Kira suka yiwa bayanin komai,batare da Bata lokaci ba ya sanar dasu hanyoyin da zasu bi.
Magunguna ya bawa Sajida yace matukar tana shansu zasu canza ta,sannan zasu sata kiba Susa tayi fresh,inda har kowa zaiyi tunanin tanada ciki sannan idan mijin yace zaiyi Mata scanning kada ta yarsa,ta taho asibitin su zai San yanda zaiyi mata,haka dai yayita Basu shawarwarin da zasu bi.
To bayan sun dawo ne Kuma maman tace ta tafi gida kafin ta yanke abinda zai biyo baya.
Kasancewar cikin magungunan da doctor ya Bata harda na daukewar al’ada hakan yasa tsarinta ya tafi yadda take so.
*Allahu akhbar*! Allah Mai yadda yaso da al’amarin bawansa,cikin wannan yanayin Allah yayi ikonsa sajida tasami ciki batare da saninta ba,Wanda kowa ya fidda Mata Rai da samun haihuwa,sai dai ba’a cire Rai da rahmar Allah.
Duk yadda suka so tsarin yabi baiyi aiki ba,hakan yasa Sajida sauya salon kishinta akan Dije,in Habeeb na Nan faram-faram,in kuwa ya fita sai ta hau zagin Dije,Wai duk Dan ta tamka mata,saita kamata ta buga inyaso ita Kuma ta kwanata laga-laga tace Dije ta gayyato aljanunta sun ta naushin cikinta har cikin ya zube,sai ta Kira mamanta a kaita asibitin su inda family doctor dinsu ke aiki,to ganin Dije taki kulata yasa ta sanar da Mamanta,shine ta Bata maganai tace duk ranar girkin Dije ta zuba a cikin lemon da zata Sha,inya so in sun zo cin abinci saita Sha da zarar Tasha din kada ta Nuna komai saita dawo bangarenta saita Kira wayar maman inyaso saita zo su kaita asibitin su,daga baya su Kira Habeeb suce cikin dare abin ya faru,Kuma an tabbatar abincin dataci na karshe a shi aka sa Mata maganin zubar da ciki, daga Nan za’a zargi Dije sai yayi waje road da ita.
Shiyasa ranar da Dije tayi girkin ta shiga wanka tazo ta saka kwayar cikin karamin cup,tadan sakada ta yadda baza’a ganta ba,to bayan sun zauna cin abin cin ta jawo kofin ta zuba,inda a tunaninta ko ta Sha tunda batada komai ba abinda zai faru da ita
Wannan shine Mafarin lamarin.
Pls ba nida charji ne
*Alkalamin khady* ✍
[7/8, 9:11 AM] El~hajj: ????????????????????????????????
*AWESOME WRITER’S ASS..* ????
(Palace of excitation n’d pleasant writer’s)
*TAME GARI*
NA
khadeeja Usman
5⃣5⃣
Cike da tashin hankali Dije ta fito daga dakin,kacibis sukayi da Naseer Wanda yaga lokacin da suka fito daga gida,ya lura kamar ba lafiya ba,hakan yasa ya biyo sahun su,cikin rudewa Dije ta shiga fadin,
” Pls Yaya Naseer ka taimaki Anty sajida, ban San meya sameta ba,Amma tana bukatar taimako”
Bai wani tsaya tambayarta Ina Habeeb ba ya nufi dakin dayaga ta fito,itama binsa tayi da gaggawa.
Koda ya shiga ya isketa cikin wannan yanayin tabbas ya razana shima,Dan haka wayarsa ya daga ya Kira doctor yusuf yasanar dashi abinda ke faruwa.
Bayan zuwan doctor yusuf din,
Fita Dije tayi ta jingina da kofar tare da kuka,tana tunanin to meya Sami Sajida haka?
Kusan mintuna talatin suka dauka kafin suka samu jinin ya tsaya,kowannensu cike da mamakin abinda suka gani,sai dai shi Naseer ya tahallaka faruwar hakan ga Dan uwansa,Dan yasanshi Sarai tun farko yace shi a ra’ayinshi bayason matarshi ta haihu da wuri,to Amma ai ya sanar dashi kwanaki cewa Sajida nada ciki,Kuma ga dukkan alama yayi matukar farin ciki da faruwar hakan Wanda a lokacin shi kanshi Naseer din har Saida yayi mamaki,aikuwa ya Zama dole yaje yaji dalilin faruwar lamarin dandai a yadda gwajinsu ya Nuna musu Sajida maganin zubar da ciki tasha.
******
Ba Wanda Habeeb ya sanarwa Sajida na asibiti daga Iyayenta har nashi,Wanda su Naseer sun dauka ya fada shiyasa Basu wani damu ba ganin wai ba Wanda yazo tunda dare ne,shi Naseer gida ya wuce ya bar su a asibitin Dan yaso magana da Habeeb Amma yanayin Daya ganshi shiya tabbatar mishi akwai damuwa,shiyasa ya kyaleshi.
Shima Habeeb din hakan take a gurinshi,inda yaja hannun Dije wadda keta rokonshi akan yabarta ta kwana a asibitin Amma ko kulata beyi ba,ya sata mota suka tafi gida.
*****
Tun asuba Dije data tashi Bata koma bacci ba ta tsaya ta gyara ko’ina tare da yin abincin da zasu asibiti dashi,Sam takasa gane matsalar dake faruwa, domin tana ganin jiya Habeeb kwana yayi beyi bacci ba, duk juyin datayi saita ganshi tsaye ko zaune Yana safa da marwa har aka Kira sallar asuba yayi alwala ya fita masallaci,acan Suka hadu gaba dayansu har Daddy Nan Daddy yaji Naseer na tambayar Habeeb ya jikin sajida.
Amsa masa yayi da cewar,
” da sauki”
“Assha” cewar daddy!
“Meya sameta?”
“Dan zazzabi ne Daddy Amma taji sauki”
“To Allah ya bata lafiya”
“Ameen!
Direct asibitin ya wuce Dan so yakeyi yaji ta Yaya hakan ta faru,sai dai Koda ya Isa ya tarar an Kuma Mata allurar bacci,wadda sai Nan da kusan awa Daya zata saketa,kujera yaja ya zauna ya zuba Mata ido Yana Mata kallon tuhuma.
Itako Dije Jin shuru Bai dawo ba yasa ta tabbatar da ya tafi asibitin,Dan haka ta shirya itama ta dauki abincin da zata Kai a basket ta shiga part din mama mariya ta sanar Mata, kasancewar Daddy na part din mamy ne,yasa mama mariya ta kirashi a waya ta sanar dashi,yayi mamaki kwarai da Jin Wai asibiti Sajida ta kwana Amma Habeeb Bai fada Masa ba dazu a masallaci,nan yace to suyi gaba ita da Dijen shima gasu nan zuwa.
Hakan ko akayi habu driver suka sa ya kaisu.
Suna Isa direct dakin suka nufa.
Yana Nan zaune yaga ta Fara motsawa alamun zata farka,sannu a hankali yaga ta bude idanunta fes,sannan ta fara kalle-kalle,har idonta ya sauka akansa,so takeyi ta tashi Amma sai taji jikinta yayi Mata wani iri,ba kwari.
A hankali yayo tattaki ya iso bakin gadon a tunanin ta taimaka mata zaiyi ta tashi sai Jin maganar sa tayi Yana fadin,
“Dama Sajida Ashe bakya Sona?”
“Ashe duk cewar da kikeyi kinfi kowa kaunata,da son ganina cikin farin ciki Ashe karya kike yi?”
“Laifin me na aikata Miki da kika zabi salwantar da gudan jini na,farin cikina a yanzu Wanda na tahallaka dukkan burikana akansa!”
“Meya hadaki da maganin zubar da ciki? In bakya son haihuwar ai saiki sanar Dani,ni Kuma zan durkusa na rokeki ki fadi ko nawa zan biyaki harki haifamin shi,Amma sai da Kika bari nasawa raina nima na kusa Zama uba sannan Kika Sha abinda yayi sanadiyar zubewar cikina, wallahi kin cuceni bazan ta……”
Sallamar su Daddy da su mama mariya da sun Dan jima da yawa amma dayake Daddy ya kirata yace suma suna hanya shine suka tsaya jiransu Dan su shiga tare….
*Toh fa! Ana wata ga wata,ku biyoni Dan Jin ta Yaya kaddara ta sauya lamarin Sajida har reshe ya juye da mujiya*
*Alkalamin khady* ✍
????????????????????????????????
*AWESOME WRITER’S ASS..*
(Palace of excitation n’d pleasant writer’s)
*TAME GARI*
NA
khadeeja Usman
5⃣6⃣
*Kuyi hakuri na rashin jina da bakuyi ba jiya,mun Sami matsalar wuta ne,Kuma ko yauma charji na kadan ne zanyi muku abinda ya samu*
****************
“Wai me kake Fadi ne Habee?”