NOVELSUncategorized

HUSNA KO HUZNA 4

????️ 4

             A garin kano

Malam Abubakar Wanda akafi Sani da malam Garba , haifaffen garin kano ne a cikin k’aramar hukumar Dala, a wata unguwar da ake cewa rijiya biyu, Malam Garba malamine Wanda yake da tarin ilimin islma  sosai ,yana koyar da yara ‘yan makaranta har ma da manya Wanda suke karatu bayan sallar asuba , mutum ne shi mai hakurin gaske tareda aiki da ilimin da yake dashi , haka kuma yana taimaka ma masu matsala aljanu , kuma ana da cewa sosai da izinin Allah , Malam Garba yayi suna Sosai a cikin garin na Dala harma da cikin gari sosai mutane ke zuwa Neman magani a wajan shi , 

Matar shi d’aya Hajaru wadda yaran unguwar ke kira da Inna , Inna itama macece mai ilimin addini kuma Sosai take taimaka ma mijinta akan karatun yaran kasancewar abubuwan sun mashi yawa , tun da sukayi aure Allah bai basu haihuwa ba har suka shafe shekara goma , sannan Allah yabawa Inna Hajaru ciki , sunyi murna sosai tareda godiyar Allah bayan wata Tara ta haihu inda aka samu ‘ya mace sunyi murna matuka inada aka sanyasa yarinya suna Zainab suna ce mata Abu , Abu Nada shekara d’aya a duniya tayi ciyon Kyanda inda alla ya sanya da ajali tace ga garinku nan , sunyi bakinciki rashin yarsu sosai amma da yake mutane ne masu tawakkali sai suka hakura suka rungumi kaddara Abu kamar wasa hakance tarinka faruwa dasu Bayan rasuwar Abu sau hudu Inna Hajaru tana haihuwa amma yaran da sunfara tasawa suke rasuwa , daga baya ma sai bata sake samun cikin ba ,har sun hak’ura sun zubama sarautar Allah ido sai bayan shekara biyar sannan Allah yakoma bawa Inna ciki wannan karon ma basuyi wani dokin cikin ba suna ganin kila shima kamar sauran ne ,

Bayan wata Tara inna ta haifo ‘yan biyunta duk maza masu matukar kama da juna , farare Tass dasu ga kyau kamar ka sacesu ka gudu Gaba d’aya mahaifiyarsu suka biyo da yake inna bafulatanar Adamawa ceTunda aka haifi yaran suka dauki soyayyar duniya suka dorama yaran kullum cikin addu’a suke akan Allah ya raya masu yaransu , inda Hassan da Hussain suka taso cikin so da kaunar junansu gasu da farinjinin mutane kowa so yake ya daukesu a haka har shekaru sukaja yaran suka fara girma,

BAYAN SHEKARA BAKWAI

Yara ne yan shekara bakwai masu matukar kama da juna amma kuma hali ya bambanta ,Hassan yanada hakuri sosai saidai akwai kulafuci ko wane lokaci yana tare da iyayenshi sam shi ko a cikin unguwar bayason fita kullum yana zaure tareda Babanshi ko cikin gida yana taya Inna aiki 


Hussain kuwa shegen zuciya ne da shi da fadan tsiya hade da tsokana ga shegen yawon tsiya da shige-shige sannan Allah ya sanya mashi son karatun boko kamar mi ,amma Malam Garba yayi tsayin daka yace bazai sanyasu a boko ba , Hassan bai damu ba amma Hussain ya damu wannan yana yake tserewa yaje har can cikin makaratar bokon garin yana labewa ta window yana sauraren karatun da ake koya masu , kuma abun mamaki sosai yake fahimtar karatun Wanda har yafi wasu dake ajin ma,

Malam yayi dukanshi har ya gaji amma yaki daina zuwa , 
Ana haka malam yayi wani bak’o alhajin birni Wanda kana ganinshi kasan naira ta zauna mashi,  ya dawo ‘yarshi yar shekara d’aya da take fama da matsalar aljanu , yarinyar kullum a tauye take an rike mata kafafu an shanye hannu d’aya baki na dalalar da yawu abun gwanin tausayi ,yayi yawo da ita kasashe daban-daban amma basu dace ba , yana matukar son ‘yar tashi kasancewar Yakima bai samu haihuwa ba kuma ita kadai ya mallaka a halin yanzu shiyasa bayajin ciyon kashe ko nawa ne wajan nema mata lafiya, Alhaji Mansur Naira kenan Wanda yake zaune a cikin garin na kano a unguwar GRA Matar shi d’aya Hajiya Halima wadda tare sukazo wajan mallam ,

Wanda suma sun samu labarinshi ne sukace bari suzo su jaraba sa’arsu 

Malam Garba ya tausaya masu sosai inda ya shaidar masu cewa tabbas iskane kuma bak’ak’en aljanu ne a jikin  yarinyar kuma zai taimaka insha Allah zata samu lafiya. 

Nan ya janyo ruwan zam-zam yayi mata tofi ya karbeta ya bata tareda shafa mata ajiki yanayi yana tofa mata wasu addu’o’i bayan ya gama ne ya shafamata wani ganyen magani, 
Aikuwa sai ji sukayi yarinyar ta fashe da kuka iya karfinta , Wanda hakan yasa iyayen nata suka zaro ido waje cike da tsananin mamaki da al’ajabi don tunda aka haifeta sau d’aya kawai tayi kuka , sam bata kuka  duk yunwar da zataji bazatayi kuka ba sai dai ita uwar tata ta rinka kintatar lokaci tabata nono ko ruwa a haka suke rayuwa har wannan lokacin amma abun mamaki yau yau itace takeyin kuka ,

Hajiya Halima har kukan fariciki tayi gdy sosai sukama Malam Garba inda Alhaji Mansur yayi mashi alheri sosai amma sai Malam yaki karba ,sunyi-sunyi ya karba amma yaki haka suka tafi suna mashi godiya.bayan yabasu wasu magunguna tare da shaida masu lokacin da zasu dawo,


Wasa-wasa jikin wannan yarinyar mai suna Lauratu yafara sauki , cikin wata d’aya sai gashi  an saki hannunta da kafafunta har tana rarrafenta a ko ina , duk sati suke zuwa wajan mallam Garba yana mata addu’a ,

Fad’ar farincikin wadan nan bayin Allah bata baki ne ,wannan yasa suka dauki malam Garba tamkar d’an uwansu , sun mashi alheri sosai har Makka Alhaji Mansur ya biya mashi , 

Wannan zuwan da sukeyi ne yasa sukayi sabo sosai da ‘yan biyu , sosai Alhaji Mansur yake son su tare da  kashe masu kudi ,
Sun dauki akalla shekara d’aya tare sunzama kamar yan uwa wannan yasa Alhaji Mansur tuntubar Malam Garba akan yanaso ya Bashi rik’on ‘yan biyu yanason zai sasu a makaranta , Malam Garba baiso ba amma saboda kunyar Alhajin ya yarda ,lokacin da yaran sukaji ba karamun murna Hussain yayi ba amma mirsisi Hassan ya nuna bazashi ba , babu yadda Alhaji Mansur baiyi ba amma fir yaki ganin haka malam ya yanke kawai su tafi da Hussain su bar mashi Hassan koba komai bazaiso yayi nesa dasu gaba d’aya ba, haka suka tattara Hussain suka taxi badon sun so ba don yanajin takaicin da Hassan zaiyi rayuwa babu ilimin zamani ,


Bayan shekara 22 a lokacin ‘yan biyu sun zama samari Wanda har yanzu kamarsu na nan saidai babbancin yanayi  don Hussain yazama Dan birni sosai sannan ya gogu da ilimin zamani  Wanda a halin yanzu ya hada degree dinshi akan Business 

Lauratu ma anzama budurwa sosai itama ta gama secondary school tun shekarar da ta wuce Wanda Alhaji mansur ya yanke shawarar aurawa Hussain Lauratu ,akayi dace suma suna son junansu , wannan Abu yayiwa iyayen dadi sosai inda aka Sanya biki nan da waya daya ,

Hassan kuwa kana ganinshi kaga Dan kauye sai dai akwai tsafta sosai kuma alhamdulillah Hussain yana kulawa da shi sosai tareda yimashi dunkuna akai-akai don ba karamun haushi yakeji ba idan yaga yadda dan’uwan nashi ke rayuwa a karkara, daga gona sai gona sai kuma karantar da yara don ilimin addini kam akwaishi alhamdulillah 

a wannan lokacin itama Inna tana rikon yar kanwarta da ta rasu mai suna Hafsatu sunace mata Hafsee, yarinya ce mai tsananin kyau da alkunya kasancewar ta cikakkiyar bafulatana , tana da shekara 19 a yanzu inda itama suke soyayya sosai tsakaninta da Yayanta Hassan ,Wanda har magana take gaban manya inda aka yanke cewa za’a hada dana d’an uwanshi Hussain ayi gaba d’aya,


Agurguje pls????????????


Bayan wata d’aya akayi auren su inda Hussain yakeda gida a cikin garin kano kerarren gidane mai kyau sosai Alhaji Mansur ya guna ma shi , a wannan lokacin ma yaso kwarai Hassan ya yarda ya Gina masu gida a tare amma nan ma fir yaki a cewarshi bazai iya rayuwa ba tareda iyayenshi ba kuma kiba haka ba shi sam bazai iya rayuwar birni ba tunda bai saba da can din ba,
Wani babban fili MALAM Garba ya bashi anan cikin garin na Dala akayi mashi gini dai-dai da zamani nan suka tare da Amaryarshi ,

Shekara d’aya da auren su Lauratu ta haifi danta namiji ranar suna yaro yaci suna Ibarhim suna ce mashi ( mu’azzam) mu’azzam Nada shekara ukku ta sake haihuwar Fatima daga nan haihuwar ta tsaya mata Wanda har wannan lokacin ko batan wata Hafse batayi ba , saidai basu damu ba don kusan  duk sati ana kawo masu mu’azzam ya kwanan masu biyu suna matukar son yaron kamar su suka haifeshi, 

Fatima Nada shekara Hudu Allah yayiwa malam Garba rasuwa ,mutuwar ta girgizasu sosai saidai ba yadda suka iya doli haka suka hakura , 

Shekara d’aya da rasuwar shi Hussain ya had’u da Hajiyar Ni’ima , a bikin wata k’awarta Wanda shi kuma angon ne abokinshi , tunda ta kyalla ido ta ganshi taji duniya ba Wanda take so sai shi ,tun daga lokacin tafara bibiyar rayuwarshi kasancewarta mace yar duniya saidai duk abunda takeyi abanza don baimasan tana yi ba , ganin haka yasa ta fara shiga bokaye dayake dama can halinta ne bata wani sha wahala ba ta shawon kanshi suka fara soyayya , 

Lokaci daya ya juyawa Lauratu baya , baya ganin kowa da gashi sai Na’ima da danginta hidima sosai yake masu ,hankalin lauratu ya tashi sosai ganin yadda ya juya mata baya ga kuma labarin soyayyar shi da Ni’ima da taji  , 

Kullum abun nashi said gaba yake wannan yasa ta yanke shawarar sanarma da inna ,
      Lokacin da Inna taji wannan maganar itama ta shiga damuwa sosai haka ta kirashi ta mashi magana amma a banza don ji yake in bai auri Ni’ima ba zai iya mutuwa haka yashiga Neman aurenta  gadan-gadan inda Takai har yayi Hayar wasu mutane sukaje ma shi Neman aurenta , ganin haka yasa kowa ya zuba ma shi ido suka fara tayashi da addu’a 

Alhaji mansur kuwa lallashin Lauratu yayi sosai akan ta bi mijinta ta ma shi addu’a dok duk Wanda yaga abunda yake yasan ba’a hayyacinshi yake ba haka ta hakura doli ta rungume kaddara ,

A cikin sati biyu akayi auren Hussain da Ni’ima  Wanda a lokacin takara damkeshi kam a hannunta sai abunda tace ‘ya’yanshi ma bai damu dasu ba bare Mamansu haka sukaci gaba da wannan zaman Yayinda lauratu take cikin kuncin rayuwa ,shekara d’aya da aure ta haifi ‘yarta ta farko Harira ,duk da Ba haka taso ba taso ta haifi namiji sosai wannan yasa tun Harira Nada shekara d’aya ta yayeta don ta matsu ta sake samun ciki ta haifi namiji   cikin ikon Allah kuwa tasamu ciki bayan wata Tara ta sake haihuwar ‘Ya mace inda aka sanyawa yarinya suna Saudat, tayi bakinciki sosai don har kuka tayi akan rashin haihuwar namiji wannan karon ma haka tayi saurin yaye Saudat don tasamu ciki saidai shiru ba wani bayani har tsawon shekara ukku………….naso kwarai nagama da tarihin nan a wannan page din amma abun bai samu ba nagaji wlh mutara a goben karku kosa yau bakuji labarin ‘yan biyun Ku ba

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button