KWARATA 87

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* ????
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ ????????
*ASMA’U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI’ATU AMINU MAMMAN DEE*
???? —— 85
Da sauri nabi bayanshi har an buɗe mishi mota ya shiga , yana shiga nima na shiga kafin a rufe , kallona yayi baiyi magana ba sai tsoki tare da matsawa daga kusa dani yana hararata , murmushi nayi kamar sakarai ina yaƙe haƙora , yadda nayi abun na bashi dariya yace hmmm Yarinya , tafiya aka farayi da motar ni kuma na miƙa mishi wayoyinshi yace in riƙe mishi zasu ajiyeni gida shi Kano zaije , cikin rashin jin daɗi nace haba Dikko Kano kuma yanzu na ƙarasa maganar kamar zanyi kuka , yi haƙuri An mata zan dawo ai ba kwana zanyi ba yayi maganar yana jawoni jikinshi , kwace jikina nayi ina cewa ai saika kaje kayi ta tafiya , yi haƙuri , ban sake magana ba har muka iso gida ,
Anayin parking na fita cikin ɓacin rai , kirana yayi nai banza dashi kamar banji ba , cikin fushi yace kije kiyi ta zuciyar ƙaramar yarinya dake , ban juyo ba na shige ciki da gudu ina kuka nidai bana so ya tafi da daren nan shine zai tafi ya barni , har sun fita daga gidan Dikko yaji kamar babu daɗi suka dawo , palo ya sameni kwance saman kujera ina kuka , cikin rarrashi yace An mata zo nan , dan bai shigo ba daga bakin ƙofa ya tsaya , ina tashi nayi bedroom , da sauri ya biyoni na kusa shiga ya riƙeni cikin disashshiyar murya yace haba An matana meye na fushi tou ? Yi haƙuri bazan daɗe ba maganina zan anso kinsan banajin daɗin tafiya da rana kafin ma kiyi bacci zan dawo insha Allah kinji An matan DK ya ƙarasa maganar yana rungumeni , banyi magana ba , ina shashshekar kuka , kinyi haƙuri ko ?
Ey , hannunshi yasa a aljihunshi ya ciro cingom saida ya saka a bakinshi yace kallar ni , tashi nayi daga jikinshi ina kallonshi , murmushi yayi da kallo mai kwantar da hankali tauna cingom in yayi sannan yace idan miji zaiyi tafiya ba’a mishi haka kinji ko ? Tom , ba’a yin abinda zaisa ya tafi da fushi kinji ? Tom , idan miji zaiyi tafiya addu’a ake mishi sai a rabu cikin soyayya da nuna kowa zai shiga taitaiyin shi idan abokin rayuwarshi baya kusa ki nunamin girman yadda zakiyi maraicina idan bama tare , zan tafi da soyayyarki kuma zanyi kewayarki zan dawo gareki ina mai farin ciki darajar waccan kulawar , kinga na baki wayoyina nace kije Ashiru ya maidake gida ni zanje na dawo ko ba daɗi sai kimin fatan alkairi ,
Kalli idona ki gani , kallonshi nayi cikin yanayin jin kunya , da nace zanje in dawo sai ki kalleni da irin wannan kallon ya nunamin cikin wata irin murya da shagwaɓa ina zakaje haka ne ? Kin gane ? Zanji wani iri a zuciyata kinyi min magana da salon da dole saina kalla , sai ya saki muryarshi yadda yake magana yace sai ince hajiya kano zanje , sake shagwaɓewa yayi ya nuna yadda zanyi idan zan bashi ansa , amma sai kiyi ta abu da Allah na yarinta ba lallashi komai maganarki a tsaye baki lanƙwasamin harshe nace miki bana san yadda kikemin magana saiki tayi min kallon da bana so , daga nace zan tafi kano ba addu’a ba komai fuuuuu ke ƙaramar Yarinya , kinsan Allah idan kikayi wasa saina ƙara aure ,
Tou kaje ka ƙara mana na hanaka ? Kinji yarintar ko ? Ji abinda kikeyi kina magana da miji kina ɗaga mishi murya , ba abinda kika iya sai kwanciya jikina shine kaɗai aikinki saina raba wurin kwanciya dake tunda ke Yarinya ce , kaje ka raba , murmushi yayi yace nasan ciwonki , yadda nayi maganar ya nuna dole zakace naje na kwanta tunda kaje ka kasa ka tsare kai tattabara sarkin aure , murmushi yayi tare dayin wasa da idonshi yana ci gaba cewa yes haka kishi ne , kishi kuma so ne , da hannunshi ya rungume kanshi yace wayyo An mata na kishi na ci gaba sabo ,
Da wata irin tafiya mai taɓa zuciya ya fita yana cewa ko bakimin addu’a a gabana ba nasan zakiyi a zuciyarki kuma saina yo miki tsaraba tunda kikaji kishina a zuciyarki saina sa kinyi farin ciki mage zan samo miki , ya fice , murmushi nayi da farin ciki na shige ɗaki da gudu na hau gado ina tsalle Allah ya tsare hanya mutumina.
Bayan na kwanta na ɗauki wayata na kira Amisty , babu wani daɗewa ta ɗauka bayan gaisuwa nace Amisty don Allah rubuto min An mata ki turomin , kamar ya ? An mata haka zaki rubuto min , tou ta faɗa tare da ajiye waya , burum ta rubuto ta turomin , gyara kwanciya nayi na rubuta An mata , wayar Dikko ta buɗe , Allah sarki Dikko ashe da gaske yake da sunan da yake kirana ya kulle wayarshi , ba wani ruwana da saƙonni wayarshi dan bana ganewa , ma’adanar hotuna na shiga ina kallon Dikko da “yan uwanshi , haka dai nayi ta zaliƙe² a wayarshi har na shiga inda nakejin maganata da tashi duk wayar da nakeyi dashi yana record kenan , Allah sarki Dikko , saida nayi filla² da duk inda nake iya shiga a wayar amma banga hotuna na ba , tou ina suke ai yacemin wayarshi bata san kowa ba daga An mata sai Doki , tou naga dukuna babu iyaka a wayar amma ina An mata tou…….. ?
Tashi nayi zaune na ciji ɗan tsayana cikin yanayin mamaki to dama masu gemu sunayin ƙarya ? Tsoki nayi tare da ajiye wayar , ina ajiyewa kira ya shigo , kamar ansa ni na ɗauka tare da cewa waye ? Caca , Oh Jiddah ce kenan ko ? Zuciyata ta fara turani inyi abinda zan ɓata mata rai amma sai wani sashi na zuciyata yace bari suja miki sharri Dikko ya sakeki , da sauri na kama kaina nace yana wanka , uban waye yasa kika ɗaukar mishi waya tou ? Ina da ansar bata amma nidai bana so naje nayi abinda zai jawomin tashin hankali har Dikko yayi fushi dani , tsinke kiran nayi , haka kiran yaita shigowa amma ban ɗauka ba , tunda kiran Jiddah ya shigo kira yaci gaba da shigowa , ita kuma ɗayar wayar naga hoton jirgi daga sama ita kira baya shigowa kenan ?
Da naji kiran yayi yawa zasu hanani bacci kawai na kashe wayar , nayi kwanciyata naci gaba da bacci abuna….
Yau kwanan Al ‘ Ameen 22 babu wanda yasan inda yake , duk wanda yasan yana da haɗin guiwa da Al ‘ Ameen akan “yan tsirkulle² hankalinshi a tashe yake danjin Dikko ya tafi dashi tun daga ranar da Dikko ya tafi dashi har zuwa yau basu da nutsuwa , su basu san ba’a kan matsalarsu Dikko ya riƙe Al ‘ Ameen ba shi Dikkon ya ɗauki Al ‘ Ameen dan yasan abinda ke tsakaninshi da Jiddah ne , wanda har ba’a magana sai tsakar dare , shi bai wani san akwai wani abu tsakaninshi da matar Dady ba…..
Zaune take ta wani kame abunta a saman kujera ta ɗauke kanta gefe gudu ba kajin wani lafiyayyen motsi sai ƙarar cingom in ita ƙasa×⁴ , kallonta Dady yayi yace wai meke damunki ne ? Duk kinbi kin tashin hankalinki akan wani dalili naki na daban , akan me fushin wani ni zai shafe ni ne ? Saida ta ƙara ƙaras² sannan tace haba mai girma gwamna ya za’ayi ace duk inda Dikko yake ajiye mutane ace an kasa samo Al ‘ Ameen ? Kafa san halin Dikko kila ma yaje ya kasheshi ya jefar dashi ruwa , tou ni gaskiya bazan daina fushi da tashin hankali ba sai an samomin Al ‘ Ameen a daren nan…..
Dady bai sake magana ba ya fara kiran wayar Dikko , gaba ɗaya wayoyin a kashe suke , Ashiru ya kira kuma ba tare dashi Dikko ya tafi ba saboda shine yace ya maida Sultana Goruba shi zaije ya dawo sai bata bi Ashiru ba tabi Dikko , cike da girmamawa Ashiru ya ɗauki wayar Dady ya gaishe shi , bayan gaisuwa Dady yace ina Babana ya kai Al ‘ Ameen ? Har ga Allah Ashiru bai tunanin komai ba yace yana Goruba road , Dady yace ka kawoshi yanzu² , Ashiru yace insha Allah suka ajiye waya ,
Bayan Dady ya gama waya da Ashiru ya kalli Bilki yace tou kinma ji yana Goruba Ashiru zaizo dashi yanzu , murmushin jin daɗi tayi ba tare data kalli Dady ba tayi godiya kusa da ita ya zauna…………….. !!! | cikin “yan mintuna da basu wuce 15 ba Ashiru yakai Al ‘ Ameen , kuma lafiyarshi garas dan Dikko bai dakeshi ba tunda ya buga mishi kai a bango ya suma bai sakeyi mishi wani abu yana mishi tambayoyi ne kafin ya gama yaci mutuncin shi ,
Momy kuwa tana can sake da baki tana bacci bata san wainar da ake toyawa ba , dan ita ba ma’abociya sa ido bace da sanin halin da wani yake ciki ba , barta dai da zafin kishi taƙalo fitinar da bata garai bata da dalili dan mafaɗaciya ce ta farkon shafi kuma bata san zaman lafiya ko kaɗan , ko shiru taji gidan kwana 2 ba’ayi faɗa ba haka nan zatace ta fita ana mata kallon hadarin kaji haka zata saka Dikko gaba tace anyi mata an matsa mata ita zata kashe auren nan tayi tafiyarta bata zama hawan jini ya kamata idan kuka bari na mutu kun shiga3 kaza² duk dan dai ayi hayaniya , haka zata haukatoshi ya fito yaita cancara ruwan rashin mutunci dan duk yafi kaf “yan uwanshi fitina bai gajiya da faɗa kuma baida haƙuri kamar amai idan ya fara babu kyau , tou bata tsayar da kanta wuri ɗaya ba bare ta gane inda duniya ta dosa…..
Da inda ya ajiye Al ‘ Ameen ya fara bayan ya dawo daga kano babu shi babu dalilinshi , agogon hannunshi ya kalla 2:15am jinjina kai yayi ya nufi ciki , wayoyinshi ya ɗauka duk ya fitar dasu a jirgi , kai tsaye Umar ya fara kira , cikin yanayin bacci ya ɗauka , bayan ya ɗauka Dikko yace ina Al ‘ Ameen ? Kallon Al ‘ Ameen dake kwance kusa dashi yana bacci yayi sannan yace har kin farka kenan ? Dikko yace kai nine ta farka gidan su wa ? Ai na gane ki ranki ya daɗe Baki daɗe da kwanciya ba a kusa dani kikayi mafarki ? Shiru Dikko yayi yana sauraren Umar daya maidashi mace , Umar kuma yaci gaba da cewa ……. A ina kika ga ɗakin ne ? ……. Tou Allah ya ƙarawa mai girma gwamna lafiya da nisan kwana muyi ta zarce muci gaba da zama a gidan gwamnati kuma kema zan kawoki har sai kin kwana kamar yadda nake kwance dani da mai gidana Al ‘ Ameen a ɗaki ɗaya yana bacci , kashe waya Dikko yayi tou waye ya tafi da Al ‘ Ameen wato yana can ma yana bacci yasan zan nemeshi shi yasa bai tafi G R A ba ya tafi wurin Umar , tashin Sultana ya farayi , da sauri na buɗe idona a firgice dan mafarki nakeyi da mutumin nan , An mata tashi na dawo lafiya kuma na samo miki magen kamoni yayi yana sauko dani yake cewa muje ki anso fita zanyi , banyi magana ba kafin in saka takalmina har ya fita daga ɗakin ina fitowa harya fice daga palon da sauri , kafin na gangare daga sama har ya sauka , cikin mota na sameshi kwalin da magen take ciki ya miƙomin tare da cewa jeki saina dawo , ajiye kwalin nayi ƙasa zan riƙeshi a kasalance yace yi haƙuri An mata idan kika taɓani yanzu zaki jawo rigima , nidai dan Allah , tou taho ya faɗa yana kamo hannuna ɗan jirgewa nayi na zauna a jikinshi na kwantar da kaina a ƙirjinshi baimin magana kuma bai taɓani ba shi kaɗai yasan ɓacin raan da yakeji a zuciyarshi saida na gaji na tashi da kaina ya ɗauki kwalin ya miƙamin na wuce ciki shi kuma ya fita……
Yau yazo da wani irin ɓacin ran da babu wanda ya taɓa ganinshi a yanayin , yayi ihu yayi hauka yace ana shiga mishi haƙƙi ya daki kanshi da saitin zuciyrashi yace shi ba mahaukaci bane ba , shi Dikko yasan abinda yakeyi ya rantse da girman Allah a tsautsayi wani ya kuskura yazo kusa dashi saiya kashe shi da gaske yake kisa zaiyi zai kashe ko waye ya kuskura yazo inda yake idan kuma mutum ya taɓashi to tabbas ko gawarshi bazatayi kyan gani ba saidai shima ya mutu ya yadda da wannan , idan da wanda ya gaji da rayuwar duniya yazo yau shine zai kashe ko waye idan baiyi kisa yau a gidan nan ba tou wallahi ya yadda shi ba ɗan Babanshi bane ba ina Al ‘ Ameen ina wanda yaje ya taho dashi waye yasa aka fito dashi ne………… Ya ƙarasa maganar yana buga kafarshi ƙasa da ƙarfi tare dayin wani irin ihu mai tada hankali da gigita , dake dare ne ihun Dikko da hayaniyarshi ya karaɗe kaf ilahirin girman gidan gwamnati ihunshi na yau yafi na kullum tashin hankali dasa ɗimuwa , duk mai imani saida ya tausaya ma Dikko kuma kowa yasan wannan abu badai mutum ba , kowa yayo waje inda yake tsaye yana hayaniya sun zagayeshi amma an rasa waye zai shiga wurinshi , sunan Al ‘ Ameen ya kira da wata irin murya yace ba duka ba zagi ba harara bare magana mara daɗi ka fito da kafafuwan ka kazo ka shiga mota kafin in irga 10 idan kuma ka bari na fito dakai da kaina saidai uwarka ta sake haifo wani ba kai ba dan zaka shiga 3n ka kuma zaka bani ka lalace , rufe idanuwa yayi cikin rashin mutunci ya fara kiran numbobi One , Two , Three , Four , Five , Six , Ser….. Da gudu Al ‘ Ameen yazo gabanshi , Momy tace me yayi maka ? Babu ruwanki kuma nayi rantsuwa duk wanda yazo kusa dani saina kashe shi…………..
Waye yaje ya ɗauko ka ne ? Ashiru ne Al ‘ Ameen ya bashi ansa , bai sake magana ba yayi gaba Al ‘ Ameen yabi bayanshi wurin yayi tsit kamar babu kowa yana fara tafiya suka riƙa darewa suna buɗe hanya har ya wuce , saida Dikko ya fita da Al ‘ Ameen hayaniya taci gaba tashi kowa yana tausayin rayuwar da ta samu Dikko gashi mahaifiyarshi bata da ragowa bare a fahimtar da ita yadda lalurar ɗanta take bata ajiye komai ba sai girman kai wulaƙanci rashin mutunci da masifa dama marar mutunci haka ake masa ana ganin kuskure babu mai gyara masa saidai a barshi yaje can yaji da halinshi…..
Uwar Jiddah kuwa data biyo Momy cewa tayi Maryam ashe ɗanki mahaukaci ne shi yasa kika maƙale saiya auri Hauwa’u ? { Jiddah } da yanzu tana can ƙasar waje tana aure yanzu haka ma takarar gwamna zai tsaya Dikkon ma har nawa yake ? Aure babu wani ci gaba ita ba ciki ba sai haƙuri irin wannan haukan yayi ya riƙemin ɗiya yaita bugu ita ba ƙato ba ? Kai ׳ gaskiya abun baiyi tsari ba kila ma bugun da yayi mata ne yasa take rashin lafiya gaskiya an shiga haƙƙina kinci amanata wallahi saida Hauwa’u tacemin bata zama kwanaki daya bigeta tace saiya saketa kika shiga kika fita ta haƙura ta zauna ashe zalinta ake ci , Momy tace aini ban iya neman asiri ba ita tayi ma kanta karatun ta natsu ta koma nidai shawara na bata kuma ta ɗauka , Maman Jiddah tace tou wallahi bana lamunta ni ban yadda da auren bugu ba waye ma Dikkon ? Waye shi…….. ? Murmushi Momy tayi mai ciwo a zuciyarta tace Dikko kuwa kowa ne dan ba sakarai bane ba yasan damarshi , bata sake magana ba ta kwanta , Maman Jiddah kuma wayarta ta ɗauka ta fara kiran Jiddah tana ci gaba da cewa aure babu wani ci gaba har yanzu ko ciki babu ina ma amfanin rayuwar Dikko ɗan iska kawai daya raina mutane.
Bayan Jiddah ta ɗauka tace Hauwa’u ashe Dikko hauka yake mara ɗaura zani ? Magana Jiddah tayi , mahaifiyarta taci gaba da cewa wallahi nasan ba komai bane sai hassadar ganin zaki ci gaba shi yasa Maryam tasa kika auri Dikko da yanzu kina can ƙasar waje kina huta ………. Eh da kema zaki zama matar gwamna …….. Wallahi hassada ce kawai tunda taga ita “ya “yanta basu auri gwamnoni ba shi yasa tayi zalinci ta haɗa aurenki da mahaukacin ɗanta , haka dai taita maganganu Momy kuma bata ce ummm ummmm ba……
Inda yakai Suwaiba yaje yakai Al ‘ Ameen , kuma wuri ɗaya ya haɗasu babu abinda ya dameshi Suwaiba kuwa sai bacci takeyi kamar jakar data kwana tana wahala , saida Dikko yayi ma Al ‘ Ameen lullusar fitar hayyaci ya ɗora da cewa idan wani ya sake zuwa ya bishi yaga yadda zaibi ta kanshi da mota kuma ya kashe banza , a wahalce Al ‘ Ameen yace nasan idan ka kashe ni ko bayan bana raye zaka tuno da maganganu na….
3 ta wuce ya koma gida kuma bai sake tashin Sultana ba haka kuma baiyi bacci ba yana zaune a gefen gadon yana nazarin wasu maganganun da sukayi da Al ‘ Ameen ,
Al ‘ Ameen miya haɗaka da Jiddah ne ? Wallahi mai gida ba abinda ya haɗani da ita kawai dai tana aike na ne na samo mata asiri tana san ganin bayanka , kamar ya zata ga bayana ? Saboda makirci da sharri irin nashi saiya kawo mishi zanje can baya wanda shi Dikko daga shi sai Allah sai Jiddah suka san wannan sirri na zance sperm , ya akayi maganar yaje wajen Al ‘ Ameen da wasu zantuka na rayuwar shi da ita a fanni auratayya ? Me yasa Jiddah ta tona mishi asiri ? Me yasa ta faɗeshi a yanayin da duk duniya ko iyayenshi baya fatar su san yana shiga irin wannan yanayin me yasa ׳…………… Kai wannan wace irin mace ce ……….. ? Hayaniyar shi ta farkar dani daga bacci , takalmin ƙafarshi ya fara cirewa ranshi a matuƙar ɓace kanshi yaji ya yamutsa daya tuno har kwanciyar da yayi a jikin Jiddah da bai sauka ba sai bayan mintuna 20 duk hadashi ta faɗawa Al ‘ Ameen wani irin ihu Dikko yayi mai tada hankali , da gudu na sauka daga saman gado jikina yana kyarma dan na firgita kuma ban taɓajin irin ihun ba , fashewa nayi da kuka , ke zo ki kwanta mana , maganar shi ta ƙara gigitani dan haka da gudu na fita daga ɗakin ya biyoni yana cewa karki hau bene An mata ki rufamin asiri , tsayawa nayi nace tou me nayi maka ? Da hannunshi biyu yake nunawa na yanayin lallashi bake bace ba yi haƙuri taho ,
A tsoroce naje wurinshi na riƙe hannunshi ina kallon idonshi , murmushin ƙarfin hali yayi tare da cewa wuce muje ciki idan ina ihu ki daina fita da gudu kinji ? Ni bana san ihun tsoro nakeji , kiyi haƙuri na bari bazan ƙara ba An mata , tou ina kakai m card in nan ?
Cikin murya mai kwantar da hankali yace me zakiyi dashi ne ? Wata ɗauka da nayi zan goge , dalili ? Nidai ka bani , ni wallahi bansan inda na ajiyeshi ba , wani abu ya faru ne ? Ey , tou meye ne ? Muje ɗaki , hannu na yaja muka koma ciki gaba ɗayanmu toilet muka shiga ni na wanke fuskata da bakina na fito , duk daren nan saida Dikko yayi wanka shi bansan abinda yasa ya mada rayuwarshi ta dare ba yanayin abu da dare kamar rana , bayan ya fito ya saka kayan jersey ya ɗauki wayarshi ya shiga duniya yace ina saurarenki…..
Gefen gado na zauna shi kuma yana zaune gefen madubi , da farko dai ina baka haƙuri akan maganar da zanyi , baimin magana ba hankalinshi yana kan wayarshi , naci gaba da cewa can² baya na haɗu da wani mutumi muka shiga har ƙallar rayuwa dashi amma babu wani abu daya shiga tsakani , yadda abun ya faru na faɗa masa kaf da zancen maganar recording da nayi masamasa ,
Ranar dana fara ganinshi a bacci da zancen ƙwaƙwale ido da yakeyi kuma yake faɗamin kuma ya zama gaske , ganin Al ‘ Ameen a baccina ranar dana ga Dikko ya rabu biyu daren ɗaurin aurenmu kenan , yace shine ya turomin tsafinsu a auna nauhin idona saboda naci kuɗin su ban biya da idanuwa na ba za’a ɗauramin aure gobe sai su cire idona , a tsarin tsafinsu basa cin idon wacce babu igiyar aure akanta zanyi aure sai aka zo dubani , shine nayi kuka kake tambayata abinda ya faru , ranar da aka kawoni gidanka a ranar nayi mafarki dashi yacemin ya cire ido saura nawa tunda nayi aure….
Abinda yasa har yanzu basu cire idona ba saboda wannan record in da nayi mashi yana so ya tabbatar babu wata sauran hujja a wurina suna so na basu su goge shi , shin idan na goge ko sun goge zasu fita harkata ko kuwa zasu kaini nima kamar yadda suka kai sauran matar aure ne ? Tsoki Dikko yayi ba tare da kalleni ba ya gyara zaman shi yana cewa ƙarya ne , wannan labari tatsuniya ne , a , a Dikko da gaske ne wallahi , An mata banda ƙaryar bacci to me ya kawo Al ‘ Ameen a mafarkinki ?
Yacemin Al ‘ Ameen ya munafurce shi kuma wallahi zai tona masa asiri Al ‘ Ameen shine jagorar matsalar rayuwarka , duk haukan da kakeyi shine , ni banasan wannan maganar karki sakemin irinta , Dikko wallahi har inda aka binne asirin ya nunamin , cikin hayaniya yace da Allah bana san iskanci in banda iskanci ya za’ayi Al ‘ Ameen ni yayi min wani abu ? Zan sake magana ya dakamin tsawa yana cewa kwanta kiyi bacci idan na sake jin surutunki saina zaneki , Dik….. Ki rufemin baki karki ɓatamin rai a daren nan…………. Ya ƙarasa yana rufe idanuwanshi.
A hankali na koma na kwanta tare da fashewa da kuka nace na rantse da Allah da gaske ne , kuma a ido biyu zan iya gane wurin , ka tsaya na faɗa maka abinda yace Al ‘ Ameen ɗin yayi masa mana , ke……………… Ki rufemin baki……. Idan kika sake magana saina kashe ki……
Shiru nayi ban sake ko tari ba nabi shi da kallo , dakamin tsawa yayi cewa daina kallona ki juya can ki kalli bango , banyi magana ba na juya naci gaba kallon bango kamar yadda yace , har aka kira sallah asuba ban sake magana ba kuma ban koma bacci ba saishi dake ta ansa kiran waya , ana kiran sallah asuba kuma ya maida wayar jirgi ya sauya kayan jikinshi zuwa jallabiya ya fita masallaci.
Abinda ya faru a baccina kamar yadda na saba mafarki dashi lokaci bayan lokaci , ina ganinsa a wasu kwanaki na baccina wanda bana iya ganewa ko tuna lokacin da yake zuwa a baccin saboda ba kullum yake zuwa ba kuma ranakun zuwan nashi daban ne ,
Ranar da naga sunayin kokowa da Al ‘ Ameen , wata ranar kuma da yazo a baccina kamar yadda ya saba yace mi yasa ban goge ba ? Nace masa Dikko bai bani ba , shine yacemin inyi alƙawari na samo mishi record Al ‘ Ameen yaci amanarshi ya yadda dashi amma ya zalinci rayuwarshi , ga yadda ya faɗamin dai , kuma yace abinda yasa zai tonawa Al ‘ Ameen asiri yana so Dikko ya ƙoreshi daga ƙasanshi shima saiya tagayyara kamar yadda shi mai ƙwaƙwale idon ya tagayyara…….
Dani da Al ‘ Ameen dukanmu iyayenmu ne sukayi aiki a gidansu Dikko , mahaifinshi Dikko mutumin kirki ne mutum mai mutunci da mutunta kowa kuma yana da alkairi da san kyautatawa wanda bashi da hali haka kuma bashi da ƙyanƙyamin talakawa , lokacin da iyayenmu suke aiki a gidansu shi mahaifin Dikko lokacin yana da mata 4 cas mahaifiyar Dikko itace babba amma yayi aure² dan samun ɗa namiji ,
Dan ya tashi hankalin rashin samun namiji tun kafin haihuwa tayi nisa , haihuwar Maryam 3 a wancan lokacin kullum mata take haihuwa dan haka kawai Dady yaci gaba da aure saida ya tara huɗu gaba ɗaya , ganin haka yasa ita kuma ta dakata da haihuwa kwata² saboda baƙin ciki da kishi , ta tashi hankalin miji ta hanashi zaman lafiya da kwanciyar hankali dan duk yadda zan kwatanta fitinarta ta zarce wurin , ga rashin san zaman lafiya ga wulaƙanci idan ta fara fitina babu wanda ya iya yasa tayi shiru , dan haka itace ta ɓata kaf gidan ya haukace aka shiga sahun kishi da jefe²n juna , a lokacin da take ita ɗaya bata san “yan uwan Dady dan ita Allah yayi mata tsantsani da ƙyanƙyami idan dai ku masu kuɗi ne ko “yan gayu tou kune abokan tafiyarta dan ita “yar gayu ce ajin farko da ƙarshe bata tarayya da mutumin data fi wayewa cewa takeyi zai kidahumar da ita , tasan hannunta kuma tasan abinda take dan duk matan da Dady ya auro babu kamar ta , ga kyau ga gayu ga aji idan ta raina ka ko ƙofar ɗakinta baka taka mata bata da mutunci yadda baki tunani , idan tana sanka kawai tana sanka idan bata sanka bata sanka……..
Itace babba kuma itace ta ɓata gidan , ita bata iya neman asiri ba amma tasan logo da kissa na duƙunƙune kan namiji shi yasa Dady ya fifita ta akan kowa sai suke ganin kamar asiri take masa dan haka suka tisota gaba jifa , nan fa gasar haihu ya tashi dan haka akaci gaba da watso ma Dady “ya “ya mata , ganin buƙatarshi bata biya ba ya fara tarawa da ebewa , amma ita Maryam duk rashin kunyarta ba’a taɓa jaraba mata bulalar saki ba.
Ganin ana haihuwa yasa itama taci gaba da haihuwa , tana komawa haihuwa Allah ya bata Dikko , tunda ta haifi Dikko su kuma suka tasashi gaba yadda basu haifa ba babu wacce ta isa itama tayi namiji sun yadda su kashe shi a tashi a tutar babu…
A kanshi aka samu namiji kuma har yau ba’a sake samu ba , bayan Dikko ya girma kuma aka riƙa harin rayuwarshi a waje idan ya fita shine dalilin da yasa aka haɗashi dasu Ashiru , shi kuma Al ‘ Ameen da ƙarfin bala’e ya shiga ya fita yake tuƙa Dikko kuma bansan abinda ya rabasu ba a halin yanzu amma dai nasan basu tare ya koma tafiya da zugar yaranshi.
Abinda yayi min shine , dani dashi gaba ɗayanmu munyi aure wurin zama da duk hidimar da kika sani anayi a aure Dikko ne yayi mana gaba ɗayanmu , tunda nayi aure na fita daga ƙarƙashin shi domin a lokacin Al ‘ Ameen ya zuƙeni daga jikin mai gida , amma duk da haka na yadda da Al ‘ Ameen sosai ganin iyayena da nashi sun tashi wurin aiki ɗaya kuma gaba ɗayanmu a gidan muke zaune , na yadda da Al ‘ Ameen jinsa nake kamar a ciki ɗaya muka fita , ashe ni mugunta ta yakeyi mugune azzalimi ne ya yaudareni anan inda nake tsaye a nan aka binne sihirin da akayi ma mai gida , abinda yayi min shine zaici gaba da faɗamin ne Dikko ya tasheni yacemin wai in tashi ya dawo , tabbas zan gane wurin amma ta ina zanbi inje wurin ? Ina Dikko ya ajiye m card in nan wai ? Har ya dawo daga masallaci ban tashi ba a yadda ya barni ba , kuma banyi sallah ba , cire jallabiyar shi yayi ya maida kayan daya cire ya kwanta.
Shin wai wannan mafarkin da gaske ne ko kuwa tatsuniya ne kamar yadda Dikko yace , tashi nayi naje nayi alwallah nazo na kabbara sallah , shi kuma Dikko bayan ya kwanta yana tunanin maganar Sultana da zancen Sadiyya sai kuma maganar Suwaiba da tace masa ya tattaro kaf yaranshi duk wanda yasan ya taɓa zama a ƙasanshi ko basa tare yazo dashi , ita kuma Sadiyya tace masa a cikin yaranshi wanda ya kasheta yake , An mata kuma tace masa Al ‘ Ameen , shin wai me ye gaskiyar lamarin nan ,
Gaishe shi nayi bayan na gama sallah , bai ansa gaisuwar ba kuma bai kalleni ba , nima ban sake gaishe shi ba nayi kwanciyata a wurin , bayan wani lokaci yayi tsoki tare da saukowa daga saman gadon , canja kaya yayi ya ɗauki makulin mota ya fita , tashi nayi na koma saman gadon ina cewa aikin banza adashen tusa…..
Kai tsaye wurin da ya ajiye Suwaiba da Al ‘ Ameen ya nufa………
04/12/2019 ????????
*JAMILA MUSA…* ????????